Shin an raba gari ne tsakanin Fafaroma Leo da gwamnatin Amurka?

Pope Leo XIV leads Blessed Virgin Mary of Guadalupe Holy Mass at St. Peter's Basilica at the Vatican on December 12, 2025 in Vatican City, Vatican

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Leo ya soki shirin korar ƴan gudun hijira da gwamnatin Trump ke yi
    • Marubuci, Lebo Diseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

Jesse Romero, wani kirista ɗan ɗarikar katolika mai ra'ayin riƙau wanda ke shirye-shiye na podcast, ya yi wasu kalamai ga Fafaroma Leo na 14.

''Abin da ya kamata Fafaroma ya faɗa mana shi ne yadda za mu shiga Aljannah,'' In ji Romero. " Ba shi da wani iko kan gwamnati, ya tsaya a matsayinsa.''

A matsayinsa na mai goya wa Donald Trump baya, ya fusata game da sukar da Fararoma wanda aka haifa a Amurka, da wasu manyan malaman ɗarikar Katolika a Amurka suka yi kan shirinsa na kokar baƙi.

A ƙiyasi duk mutum ɗaya cikin mutum biyar a Amurka ɗan ɗarikar Katolika ne, don haka cocin na taka muhimmiyar rawa a rayuwar Amurkawa da kuma siyasar ƙasar.

Ƴan katolika kamar mataimakin shugaban ƙasa JD Vance, da sannanen mai fafutukar kwato yanci Leonard Leo, na daga cikin mutanen da suka bayar da gudunmawa sosai wajen samun nasarar Trump a zaɓe.

Hakazalika da dama daga cikinsu na riƙe da manyan muƙamai kamar sakataren harkokin waje Marco Rubio da sakatariyar ilimi Linda McMahon.

Sai dai batun kwararan baƙi zuwa Amurka na daga cikn abubuwan da ke kawo saɓani tsakanin shugabancin Cocin da gwamnati, da ma a tsakanin mabiya ɗarikar.

A lokacin da manyan malaman cocin suka haɗu lokacin zaɓen Fafaroma a watan Mayu, Romero ya yi fatan za a samu ''Fafaroma mai hali irin na Trump'', wanda mahangarsa ta zama irin ɗaya da ta shugaban ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Fafaroma Leo na 14 ya sha bayyana damuwarsa game da abubuwan da ake yi wa ƴan gudun hijira a Amurka, inda ya yi kiran a sake yin ''nazari mai zurfi'' kan hakan a watan Nuwamba.

Ya ɗabbaƙa aiki da sura ta Matthew, inda ya ce '' Yesu ya faɗa ƙarara cewa a ƙarshen duniya, za a tambaye mu ' Ta yaya muka tarbi baƙi?''

Mako guda bayan hakan, ƙungiyar manyan malaman ɗarikar Katolika a Amurka (USCCB), ta fitar da sanarwar mai muhimmanci da ba kasafai takan fitar ba, inda ta bayyana ''damuwarta kan abubuwan da ƴan gudun hijira ke fuskanta a Amurka.''

Malaman addinin sun ce sun 'damu' game da abin da suka kira ' yanayi na tsoro da fargaba.' Sun kuma ce ba sa 'goyon bayan korar ƴan gudun hijira da ba su ji, ba ba su gani ba'' kuma suka yi 'adduar kawo ƙarshen wulaƙanta bil'adama da cin zarafi.''

Wannan ne karon farko cikin gomman shekaru da ƙungiyar USCCB ta fitar da irin wannan sanarwa. Sanarwar ta kuma samu goyon bayan Fafaroma, wanda ya bayyana ta a matsayin 'mai matuƙar muhimmanci'' ya kuma buƙaci dukkanin ƴan ɗariƙar Katolika su mayar da hankali kanta.

Immigration and Customs Enforcement (ICE) agents conduct operations in the Little Village neighborhood, a predominantly Mexican American community in Chicago, United States on November 08, 2025.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jihar Chicago ce gwamnatin Amurka ta fi mayar da hankalinta kan wajen aiwatar da shirin korar baƙin haure.

Rikici da Fafaroma

''Ina ganin alaƙarsu ta yi matuƙar tsami'' in ji David Gibson, shugaban a cibiyar kula da addini da ala'ada ta jami'ar Fordham.

Masu ra'ayin riƙau sun yi fatan Fafaroma Leo zai kawo sauyi daga abin da wanda ya gabace shi Fafaroma Francis ya yi, na mayar da hankali kan kare ƴanci alumma da ƴan gudun hijira, a cewar Gibson.

"Da dama daga cikin na cikin fushi, suna so su gargaɗi cocin ta iya bakinta'', ta tsaya kan tattauna batun zubar da ciki, In ji Mista Gibson.

Mai kula da mayar da baƙin haure na fadar White House Tom Homan, wanda shi ma ɗan katolika ne, ya ce cocin ta yi ''kuskure'', kuma ya kamata shugabanninta su mayar da hankali wajen gyara cocin.

A watan Oktoba sakatariyar yaɗa labarai ta White House Karoline Leavitt ta yi watsi da shawarar da fafaroman ya bayar kan cewa yadda gwamnatin Amurka ke yi wa ƴan gudun hijira abu ne da ke take haƙƙin bil'adama.

Gibson na ganin cewa a hasashen gwamnati, "akwai isassun Amurkawa yan darikar katolika, musamman fararen fata da ke goyon bayan jam'iyyar Republican da kuma shugaba Trump, kuma a ƙarshe zai amfane shi a siyasance idan ya samu saɓani da Fafaroma.''

Kusan kashi 60 na fararen fata ƴan katolika sun amince da matakan da Trump ke ɗauka kan baƙin haure, a cewar wani sabon bincike da wata cibiyar bincike kan addini ta yi.

US Vice President JD Vance speaks during the National Catholic Prayer Breakfast at the Walter E. Washington Convention Center in Washington, DC, US, on Friday, Feb. 28, 2025.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya sha nanata yadda ɗarikarsa ta katolika ta yi tasiri kan siyasarsa

JD Vance ya kasance abin misali wajen ƙaruwar tasiri da ƙarfin da masu tsatsaurar ra'ayi ƴan Katolika ke samu a fannin siyasa, wanda ya ce addininsa ne ya saita siyasarsa.

Duk da dai ya bayyana cewa shirye-shiryen da suke yi bai saɓa wa koyarwar Cocin ba, ya kuma ce akwai buƙatar a riƙa tunawa da cewa mutanen da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba ma mutane ne.

Sai dai wasu ƴan Katolika na ganin cewa ba haka abin yake ba. Jeanne Rattenbury wata mabiya ɗarikar ce da ke cocin St Gertrude da ke birnin Chicago. Birnin ya kasance inda Gwamnatin Trump ta fi mayar da hankali wajen aiwatar da shirinta na korar baƙin haure.

A watan Nuwamba Miss Rattenbury ta shiga cikin wani taron addini na mutum dubu biyu da aka gudanar a harabar cibiyar da ake tsare ƴan gudun hijira da ke unguwar Broadview a Chicago.

''Ina alfahari da zama ƴan ɗariƙar katolika a yayinda cocinmu, daga kan Fafaroma da manyan malamanmu ke cewa ƴan gudun hijira na da ƴancin a mutunta su.'' In ji Ms Rattenbury.

Wata majami'a a kusa da Boston ta bayyana cewa Yesu ma ɗan gudun hijira ne, har suka sauya hoton Yesu da wani rubutu da ke cewa "Jam'ian da ke kula da shige da ficen baƙin haure sun zo nan''

Sai dai mutane da dama a garin sun yi ƙorafi, lamarin da ya sa shugaban katolika a Boston ya bayar da umurnin sauke rubutun, sai dai har zuwa yanzu ba a sauke ba.

A demonstrator holds up a sign saying "Jesus wouldn't do this" during a protest outside the US Immigration and Customs Enforcement detention center in Broadview, Illinois against the latest US immigration crackdown, on October 10, 2025

Asalin hoton, Getty Images

'Ya saɓa wa koyarwar addini'

Bishop Joseph Tyson na birnin Yakima da ke jihar Washington na daga cikin mutum 216 da suka goyi bayan saƙon ƙungiyar USCCB. Malaman cocin biyar ne kawai suka ƙi goyon baya, yayinda uku kuma suka ƙi bayyana ra'ayinsu.

''Akwai saɓani tsakanin yadda Cocin ke kallon batun ƴan gudun hijira daga yadda gwamnatin mai ci a yanzu ke kallon batun.

''Muna ganin abubuwan alheri a tattare da su.''

Ya ce ba wai yana goyon bayan a buɗe iyakoki ba ne, wani abu da shi ma Fafaroma ya bayyana, sai dai ba ya goyon bayan korar su, ba bisa ƙa'ida ba.''

''Korar mutanenmu da muke gani ana yi a Amurka, ba bisa ƙai'da ake yi ba ko kuma ana lalubo masu laifi bane a kore su, '' in ji shi.

Ya yi ƙiyasin cewa a cikin rabin iyalan da ke cikin cocinsa na da aƙalla mutum guda da ke fuskantar wata matsala game da matsayinsu a ƙasar. Ya ce wasu malaman cocin ma ƴan gudun hijira ne, wanda hakan ke sanya cocin a cikin wani mawuyacin hali.

''Za a iya janye wa mutum takardunsa a kowane lokaci, mutanenmu ko da yaushe suna yawo da takardunsu.''

Bishop Tyson na ganin wannan tsarin na Amurka ya saɓa wa koyarwar ɗariƙar Katolika.

Sai dai shi a nasa ɓangaren, Jesse Romero ya ce malaman katolika na Amurka da Fafaroma ne ke saɓa wa koyarwar ɗariƙar. Ya ce ɗariƙar Katolika ta bayyana cewa ya kamata ƴan gudun hijira ya kamata su riƙa bin doka, ciki har da ko ya kamata a ce sun shiga ƙasar sun zauna.

''Muna da malamai da yawa a cocin katolika na Amurka da ke mahanga ta zamani kan koyarwar addini.''

Romero ya ce duk da ya amince fafaroma da sauran malaman cocin shugabannin addinai ne, ''amma hakan ba ya nufin komai suka faɗa ɗaiɗai ne, su ma ƴan adam ne.''