Nau'ukan cutar kansa biyar da suka fi addabar 'yan Najeriya

xxx

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Masana harkar lafiya sun yi ittifakin cewa kwayoyin halittun cutar kansa kan rarrabu, su girma su kuma yaɗu a sassan jiki, wanda muddin likitoci suka kasa gano hanyoyin da za su hana su yaduwa rai na shiga cikin hadari.

Akwai dalilai da dama da masana suka bayyana cewa suna haifar da cuttukan kansa daban-daban a sassan jikin dan'adam, sai dai har yanzu bincike na ci gaba a fadin duniya domin samun makamar yaki da cutar.

Wasu abubuwa da masana kan yi gargadin cewa suna kara hadarin kamuwa da cutar sun haɗa da shan taba sigari, cin abinci maras kyau, har ma da rashin motsa jiki.

Wannan ne ya sa cibiyar bincike kan cutar kansa da magungunanta a Najeriya (NICRAT) ta yi gargaɗi game da ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ƙasar.

Shugaban sashen kariya daga kamuwa da cutar a Najeriya, Dakta Usman Muhamed Waziri ya shaida wa BBC cewa cutar ta jima cikin mutane, sai dai yanzu ne aka fi samun iliminta.

"Tun a da can baya nau'ukan cutar kansa na nan amma yanzu ne aka fi gano su," in ji Dakta Usman.

Ya ƙara da cewa tsohon ciwo ne wanda iliminsa ke yawaita a yanzu.

"Kiyasi ya nuna cewa kusan mutum 128,000 suka kamu da sabuwar cutar kansa a Najeriya a shekara ta 2022.

Ya lissafa na'ukan cutar da suka fi addabar Najeriya kamar haka:

Kansar mama

Kansa

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Usman Muhamed ya ce ita wannan cuta ta kansar mama ta fi kama mata.

Kuma an fi samun ta galibi daga matan da shekarunsu suka yi nisa.

"Saboda yanayin halitta ya kasance kansar mama da ta bakin mahiafa su suka fi yawa a ƙasa," in ji shi.

Amma kuma akwai yiwuwar warkewa idan aka gano cutar da wuri, in ji kwararru.

Don haka yake da matukar muhimmaci mata su rika zuwa ganin likita akai-akai ana duba lafiyarsu don gano idan akwai wasu sauye-sauye a jikin maman nasu.

Sai dai likitan ya ce cutar na kama kowane irin jinsi.

Kansar bakin mahaifa

Kansar bakin mahaifa kan tsiro ne a bakin mahaifar mata. Kuma ta fi shafar matan da ke kan ganiyarsu, wato daga shekara 30 zuwa 45.

Dakta Usman ya ce ita wannan cuta mata ne kaɗai take kamawa.

Haka ma, masana sun ce yawancin matsalolin cutar kansar bakin mahaifa na faruwa ne sakamkon kamuwa da nau'in kwayar cutar da ake kira HPV, wadda galibi kan yadu ta hanyar ko wace irin mu'amalar jima'i tsakanin mace da namiji.

Amma kuma akwai irin nau'ukan wannan kwayar cuta ta HPV guda 100 da akasari ba su da haɗari. Sai dai wasu nau'ukan sukan haddasa wasu sauye-sauye a cikin kwayoyin halittar bakin mahaifar da ka iya haifar da cutar kansar.

Amma kuma waɗannan kwayoyin cuta ba sabbin abu ba ne, kana akasarin mata ba su cika kamuwa da kansar a dalilinsu ba.

Kansar mafitsara

Dakta Usman ya ce wannan na daga cikin na'ukan cutar kansa da suka fi addabar ƴan Najeriya.

Cutar kansa ce wadda ke addabar maza.

Akan kuma samu namiji ɗaya cikin tara da ke kamuwa da cutar, amma kuma mutum daya kadai cikin 39 kan mutu da cutar.

Kusan kashi 80 bisa dari na mazan da suka kai shekara 80 na da kwayoyin halittar kansar a mafitsararsu.

Bayan kasancewa maza, akwai wasu dalilai da kan haifar da cutar ta kansar mafitsara.

Akwai dalilai kamar na shekaru, da yanayin abinci, da kiba da tarihin cutar daga cikin dangi, da kuma yadda mutum yake tafiyar da rayuwarsa.

Kansar hanji

Wani bincike da masana suka gudanar ya nuna cewa akan samu babban tsaiko a tsakanin lokacin da mutane kan gano alamun cutar kansar hanji da kuma lokaci da aka ainihin gano cutar.

Wannan tsaiko da galibi yakan kai watanni biyar, da hakan kan haifar da bazuwar cutar ta yadda kan iya kawo cikas waje warkarwa.

Yayin da gaskiya ne akasari mutanen da suke da alamun cutar ta kansar hanji ba su ɗauke da ita, amma akwai hadari tattare da tunanin cewa ba itan ba ce.

Don haka yana da matukar muhimmanci a san cewa alamomin cutar kansar hanjin don saboda mutum ya san hanyoyin ɗaukar matakan gaggawa a daidai lokacin da za a iya warkarwa kafin ta bazu zuwa wasu sassan jiki.

Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da murɗawar ciki, yin bayan gida mai launin baki ko kuma ja, ko kuma sauyi a yanayin yadda mutum yake yin bayan gida, kamar yin gudawa ko kuma bayan gida akai akai.

Su waye cutar ta fi kamawa?

Dakta Usman Muhamed ya ce cutar ba ta bar kowane mutum ba.

Ya ce tana kama mazauna birni da kuma na ƙarƙara.

"Abin da ya sa ake ganin ta fi kama mazauna birni shi ne saboda suna zuwa yin gwaje-gwaje a asibiti don tabbatar ko suna ɗauke da ita," in ji shi.

Ya ce wasu mazauna ƙarƙara ba sa samun damar zuwa gwaji, inda har cutar ke yin tsanani ta kuma zama ajalinsu.

"Watakila saboda yanayin al'ada da sinadarai da ake alaƙantawa da cutar ta daji da ake ganin an fi samunsu a birni, shi ya sa mutane ke ganin ƴan birnin sun fi kamuwa," in ji shi.