Wane ne Jeffrey Epstein, mutumin da ya tafka badaƙalar da za ta shafi masu hannu da shuni?

Jeffrey Epstein

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 4

"Ni ba na zaluntar mutane da lalata, kawai 'mai laifi' ne,'" kamar yadda Jeffrey Epstein ya taɓa faɗa wa jaridar New York Post a 2011. Shi ne bambancin tsakanin mai aikata kisa da mutumin da ya saci burodi."

Epstein ya mutu a wani gidan yari na birnin New York ranar 10 ga watan Agustan 2019 yayin da yake jiran shari'a, ba tare da wani tsammanin beli ba, kan tuhumar safarar mutane domin aikata lalata.

Lamarin ya faru ne fiye da shekara 10 bayan kama shi da laifin neman yin lalata da ƙaramar yarinya, wanda ya sa aka ayyana shi a matsayin mai laifin lalata.

Daga baya kuma, ana zargin sa da gudanar da "babban gungu" na yara matan da shekarunsu ba su kai 18 domin aikata jima'i. Ya musanta laifukan da ake zargin sa da su.

Amma wane ne shi?

'Mutum na musamman'

Mutumin da aka haifa kuma ya tashi a New York, Epstein ya koyar da lissafi da kimiyyar physics a makarantar Dalton School a shekarun 1970. Ya karanci kimiyyar physics a jami'a amma bai kammala jami'ar ba.

Epstein ya burge ɗaya daga cikin iyayen ɗalibansa, abin da ya sa har ya haɗa shi da wani abokin aikinsa a bankin Bear Stearns.

Ya zama abokin hulɗar bankin cikin shekara huɗu. Ya zuwa 1982, ya kafa kamfaninsa mai suna J Epstein and Co.

Kamfanin na taimaka wa kwastomomi game da harkokin kuɗinsu wanda ya kai darajar dala biliyan ɗaya. Jim kaɗan bayan haka Epstein ya fara kashe arzikinsa - ciki har da gidan da ya saya a Florida, da gidan gona a New Mexcio, da kuma wani babban gida a New York.

Kazalika, lokacin ya fara hulɗa da shahararrun mutane, da mawaƙa, da 'yansiyasa.

"Na san Jeff tsawon shekara 15. Mutum na musamman," in ji shugaban Amurka na yanzu Donald Trump cikin wata hira da mujallar New York kan rayuwar Epstein a 2002.

"Yana da daɗin zama. An ce ma yana son mata masu kyawu kamar ni, kuma da yawansu matasa. Babu wata tantama Jeffrey ya ji daɗin rauwarsa."

Jeffrey Epstien

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeffrey Epstien (hagu) da Donald Trump a 1997

A 2002, Epstein ya ɗauki tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton da ɗan fim Kevin Spacey da Chris Tucker a jirginsa zuwa Afirka. Ya so ya sayi mujallar New York tare da tauraron fim Harvey Weinstein a 2003, shekarar d aya bai wa Jami'ar Harvard kyautar dala miliyan 30.

Ya yi soyayya da mata kamar sarauniyar kyau ta Sweden Eva Andersson Dubin, da Ghislaine Maxwell, 'yar marubuci Robert Maxwell, amma bai taɓa aure ba.

Rosa Monckton, tsohuwar shugabar kamfanin Tiffany & Co, ta faɗa wa mujallar Vanity Fair a 2003 cewa Epstein mutum ne "da ba za a iya siffantawa ba" kuma "mai matsayi".

"Kana tunanin ka san shi, sai kuma ka hango wani abu daban mai ƙayatarwa da ba ka sani ba," a cewarta. "Abin da kake gani ba shi za ka samu ba."

Laifi da ƙulla yarjejenya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A 2005, iyayen wata 'yar shekara 14 sun faɗa wa 'yansandan Florida cewa Epstein ya yi lalata da ita a gidansa da ke Palm Beach. Binicken da 'yansanda suka yi a gidansa sun gano hotunan yara mata da yawa.

Jaridar Miami Herald ta ruwaito cewa ya ɗauki tsawon lokaci yana lalata da yara mata.

"Bai taɓa ɓoye hulɗar da yake yi da ƙananan yara mata ba," kamar yadda marubuci Michael Wolf ya faɗa wa mujallar Nw York a 2007 bayan an kai Epstein kotu.

"Wani lokaci bayan an fara zargin sa, muna magana da shi sai ya ce min, 'Me zan ce, ina son yara mata.' Na ce masa, 'Ƙila ya kamata ka ce, 'Ina son matasan mata.'"

Amma masu gabatar da ƙara sun ƙulla yarjejeniya da shi a 2008.

Saboda haka gwamnatin tarayya ba ta tuhume shi ba - wanda ba don haka ba za a iya yanke masa ɗaurin rai-da-rai - amma sai aka yanke masa ɗurin wata 18 a gidan yarin kuma akan ƙyale shi ya je ofis tsawon awa 12 a rana sau shida a mako. Daga baya aka sake shi bayan wata 13 bisa dabi'ar da ya nuna.

Jaridar Miami Herald ta ce mai gabatar da ƙara na gwamnatin tarayya Alexander Acosta - wanda shi ne ministan ƙwadago na gwamnatin Trump - ya ƙulla yarjejeniya da shi domin ɓoye girman laifukan da ya aikata da kuma rufe binciken hukumar FBI kan ko akwai wasu mutanen da ya zalinta.

Mista Acosta ya ajiye aiknsa a watan Yulin 2019 kan badaƙalar, amma ya kare abin da ya aikata.

Tun daga 2008 aka saka Epstein cikin ragistar masu laifin lalata a matsayi na uku a New York. Ayyanawar ta tsawon rayuwarsa ce wadda ke nufin zai iya sake aikata laifin.

A 2010, tsohon yariman masarautar Birtaniya, Andrew wanda shi ne ɗan sarauniya na uku, an ɗauki hotonsa tare da Epstein a wurin shaƙatawa na Central Park a New York. Hulɗarsa da Epstein ta sa masarautar ta yanke shawarar tuɓe masa rawani.

Yayin wata hira da BBC a 2019, tsohon yariman wanda ya san Epstein tun 1999, ya ce ya je New York ne domin ɓatawa da shi. Ya ce ya yi nadamar zama a gidansa lokacin da ya je.

Wata mai zargin Epstein da lalata mai suna Virginia Roberts - wanda ta sauya zuwa Virginia Giuffre - daga baya ta yi zargin cewa an tilasta mata yin jima'i da Andrew a farkon shekarun 2000 lokacin da take shekara 17.

Andrew ya musanta iƙirarin kuma ya ce ba zai iya tuna wani hoto da aka taɓa ɗaukar su tare ba a Landan.

Amma a 2022 ya biya Virginia miliyoyin dala domin sasanta lamarin zargin cin zarafinta da ya yi a wajen kotu.

An kama Epstein a New York ranar 6 ga watan Yulin 2019 bayan ya koma Amurka daga Faransa a jirginsa.

Masu shigar da ƙara sun nemi a ƙwace gidansa na New York, inda suka zargi cewa a nan ya aikata mafi yawan laifukan.

Epstein ya sha musanta zarge-zargen. Bayan kotu ta ƙi bayar da belinsa an ci gaba da tsare shi a gidan yarin New York.