Za mu buɗe fada, mu naɗa hakimai - Rarara

Dauda Kahutu Rarara

Asalin hoton, Dauda Kahutu Rarara/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya ce zai yi amfani da sarautarsa ta ƙasar Hausa domin haɗa kan mawaƙa tare da inganta sana'arsu.

Mawaƙin ya bayyana haka ne a zantawarsa da BBC Hausa, inda ya ce zai buɗe fadarsa ta sarauta, sannan zai naɗa hakimai da wakilansa da za su taimaka masa wajen gudanar da sarautar.

A kwanakin baya ne Sarkin Daura Umar Faruq ya naɗa mawaƙin a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, a wani ƙasaitaccen biki da aka yi a fadar sarkin Daura da ke jihar Katsina.

A zantawarsa da BBC, Rarara ya ce, "na ji daɗi sosai da wannan sarauta ko muƙami. Kuma jin daɗin ya ta'allaƙa ne da yadda mutane suka karɓi naɗin," in ji shi.

Ya ce sarautar ta ƙara haska masa wasu abubuwa na rayuwa, musamman ganin yadda ya taso, da matakin da yake kai a yanzu na rayuwa.

"Ka ga ni almajiri ne, yayana ne ya saka ni a mota daga Kahutu aka kai ni jihar Kano domin karatun Qur'ani. Daga lokacin zuwa yanzu idan na duba rayuwata, sai in ga to me (ake buƙata) domi a kai maƙura?."

Ya ce a harkar waƙa da yake yi, yana ganin ya kai maƙura, domin a cewarsa, "a wannan rukunin da nake ciki, babu wani abu da ya ce wannan sarautar a gurina. Waƙa nake yi, kuma aka ce yau ni ne Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa baki ɗaya, gaskiya babu abin da ya wuce wannan a wajena. Babu wani biki da ya fi wanan."

Daga almajiranci zuwa sarautar waƙa

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon

Ya ƙara da cewa asali karatun Qur'ani mahaifinsa ya yi tunanin zai gada, inda ya bayyana cewa har yanzu abokan mahaifinsa sukan yi mamakin idan suka ji waƙoƙin da yake yi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"A cikin almajiran mahaifina, guda shida ne suka rubuta Qur'ani, kuma ya yi tunanin zan wuce su a karatu. Amma haka Allah ya so, ni waƙa zan yi."

A game da yadda ya samu sarautar sarƙin waƙar, ya ce ya samu labarin akwai waɗanda suka so sarautar, kuma akwai waɗanda suke so a naɗa wasu mawaƙan daban-daban sarautar ta ƙasar Hausa.

"Amma shi sarki ya duba abubuwa da yawa, da kan shi ya nanata cewa 'mun ba ka wannan sarautar ne saboda ka cancanta, kuma kana waƙa yadda ake so a yi.' don haka ina farin ciki."

Rarara ya ce za a iya samun sarkin ƙasar Zazzau ko Dutse ko sarkin waƙar wata masarautar, amma a cewarsa duk sarautun na waƙa sun bambanta da sarautarsa da ƙasar Hausa.

"Saboda sarkin waƙar Hausa ne kuma yana amsa muryar ƙasar Hausa baki ɗaya musamman mawaƙa a Najeriya da ma na Afirka."

Mawaƙin ya ce an ba Naziru sarkin waƙa, kuma an ba Aminu Ala sarauta, "kuma duk inda na gansu sarki nake kiransu. Amma yanzu ni na ƙasar Hausa ne, ai ya kamata a ɗan saka ni a sama. Sai dai idan an yi na Usmaniyya, ka ga wannan zai iya fin na jihohi."

Ya ce zai naɗa hakimai, ya buɗe fada, "kuma za mu yi duk abin da ya kamata wajen inganta sana'ar. Zan buɗe wajen koyon waƙa, sannan mu jawo masana na ɓangaren Hausa mu yi aiki tare. Kuma dukkan muna fata da izinin Allah dukkan mawaƙanmu za su ci amfanin wannar sarautar."