Abu 5 da suka fito game da Buhari watanni biyar bayan rasuwarsa

Asalin hoton, Getty Images
Littafin da Dakta Charles Omole ya rubuta dangane da marigayi shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fito da wasu abubuwa muhimmai dangane da tsohon shugaban ba da ba a sani ba.
Littafin mai taken "Daga Soja zuwa Dattijo, Abubuwan da Muhammadu Buhari ya bari", ko kuma "From Soldier to Statesman, The Legacy of Muhammadu Buhari," ya yi waiwaye kan rayuwar Buhari daga ƙuruciya zuwa rasuwarsa.
An dai ƙaddamar da littafin ne a makon da ya gabata kuma batutuwan da ke ƙunshe a littafin sun tayar da ƙura saboda yadda littafin ya tuntuɓi makusantan Buhari walau iyali ko kuma na aiki.
BBC ta yi nutso cikin wannan littafi inda ta zaƙulo wasu abubuwan da ƴan Najeriya da dama ba su sani ba dangane da tsohon shugaban ƙasar nasu.
An zarge ni da shirin kashe Buhari - Aisha

Mai ɗakin tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari ta ce yana ɗaya daga cikin dalilan ƙamarin rashin lafiyar da Buhari ya yi shi ne kulle mata ƙofa da marigayin ya yi na ɗan wani lokaci bisa zargin za ta kashe shi.
Aisha Buhari ta faɗi haka a shafi na 574 na littafin "From Soldier to Statesman, The Legacy of Muhammadu Buhari", da Dakta Omole ya rubuta.
"Sun ce ina son na kashe shi ," ta faɗa cikin takaici kamar yadda mai littafin ya nuna. Ta kuma ci gaba da cewa "mai gidana ya yarda da abin da suka faɗa masa, na tsawon mako guda ko makamancin haka....inda ya fara rufe ɗakinsa, ya sauya wasu ɗabi'unsa."
Sakamakon rashin ganawa da ita ya sa ba ya samun irin abinci da sauran nau'ikan abubuwan da ya saba ci ko sha.
Aisha Buhari ta ƙara da cewa kafin su shiga fadar shugaban ƙasa tana kula da mai gidan nata domin duk abincin da yake so yana samu.
To sai dai kuma ta ce bayan shigarsu fadar shugaban ƙasa, ba sa kula da yadda yake cin abinci, inda ta ce akwai lokacin da "ya shafe shekara guda ba tare da cin abincin rana ba saboda haka ta ce "yana da tarihin rashin isasshen abinci a tare da shi"
Yadda 'shan taba sigari' ya shafi lafiyar Buhari

Asalin hoton, Presidency
Saɓanin yadda aka yi ta samun raɗe-raɗi da rahotanni masu karo da juna dangane da haƙiƙanin cutar da ta yi ajalin tsohon shugaban, Dakta Omole, a littafin nasa ya ji ta bakin mai ɗakinsa wadda ta warware zare da abwa.
Kafin wannan littafin nan an ta yaɗa jita-jita cewa "gubar da aka saka wa " Buhari tun yana shugaba ce ta yi tasiri a lokacin rashin lafiyar tasa ta ƙarshe.
A shafi na 576 na littafin, Aisha Buhari ta nuna cewa ɗaya daga cikin dalilan da suka ƙara ta'azzara cutar da mai gidan nata ke fama da ita shi ne 'shan taba sigari' da ya yi lokacin yana da ƙuruciya sai kuma cutar lumoniya da ta zamo ajalinsa.
Baya ga wannan Aisha ta kuma nuna yadda sanyin na'urar sanyaya ɗaki da shekarun aikin soji inda suke aiki a cikin ruwa da kuma tsufa duka suka taru suka ta'azzara cutar da ta zamo ajalinsa.
Sabi'u Tunde, mai karfin faɗa a ji

A shekaru 8 na mulkin marigayi Muhammadu Buhari, sunan da ya fi amo a bakin ƴan Najeriya shi ne na Sabi'u Tunde wanda shi ne mataimaki na musamman ga shugaban kuma ɗan ƴar uwar Buhari.
A cikin shafi na 549 na wannan littafi, Aisha Buhari ta nuna yadda mataimakin na musamman ga marigayi shugaba Buhari ya zama mai ƙarfin sa wa da hanawa, a tsakanin ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati.
"Yana da iko sosai a kan mafi yawancin ministoci," in ji Aisha Buhari, a cikin littafin "From Soldier to Statesman, The Legacy of Muhammadu Buhari.
Abin da ya sa Buhari bai goyi bayan Osinbajo ba

Asalin hoton, Presidency
Dakta Omole ya ce bisa bayanan da ya tattara ya gano dalilin da ya hana Buhari goyon bayan mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo domin yi takara tare da Bola Tinubu wanda yake neman kujerar a lokacin.
"Ban san Osinbajo ba. Ta hanyar Tinubu na san shi," in ji marigayi Buhari.
Dakta Omole ya ƙara da cewa duk da irin maƙarƙashiyar da ƴan baranda suka yi na ganin Tinubu bai kai labari, amma Buhari ya ƙi bin ra'ayinsu kasancewar ya tsaya kai da fata wajen ganin an bi tsarin jam'iyya.
Bugu da ƙari, Omole ya rubuta cewa abin ma da ya fi bai wa Buhari haushi kan neman takarar Osinbajo shi ne "yadda kawai ya sanar da shi maimakon neman shawararsa ko kuma tuntuɓar sa kafin ayyana burin nasa."
Shirin ƙaƙaba Ahmed Lawan

Asalin hoton, Lawan Ahmed/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Littafin na Dakta Omole ya yi bayani kan yadda wasu da ake ganin ƴan baranda ne a fadar shugaban ƙasa da ke bayar da umarnin ƙarya da sunan shugaba Buhari, inda marubucin littafin ya rawaito abin da tsohon Sifeto Janar na ƴansanda yake faɗi
" Da safiyar ranar zaɓen cikin gida (na APC) wasu manya masu faɗa a ji - wasu mutane makusantan Buhari suka samu Darekta Janar na SSS da IGP da Darekta Janar na NIA..
"Sun fada mana umarnin shugaban ƙasa cewa su kai jami'an tsaro domin tabbatar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a zuwan ɗantakarar da kowa ya amince da shi," in ji tsohon Sifeto Janar na ƴansanda, Alƙali Baba.
Sai dai kuma tsohon Sifeton Janar na ƴansanda ya ce shi ya ƙi yarda ya bi umarnin kuma ya fada wa sauran jami'an na tsaro cewa shi ba zai yi ba, inda daga baya dukan su suka nemi ganawa da shugaban ƙasa.
"Da mu ka gan shi sai muka shaida masa cewa an kammala komai a filin taron. Sai muka nemi sanin ko akwai wani umarnin bayan wannan. Amma bai faɗi komai ba."











