Shugabannin al'umma biyar da suka rasu a Najeriya daga farkon 2025

Edwin Clark, Aminu Ɗantata, Muhammadu Buhari, Sikiru Adetona

Asalin hoton, FB/Multiple

Bayanan hoto, Edwin Clark, Aminu Ɗantata, Muhammadu Buhari, Sikiru Adetona
Lokacin karatu: Minti 5

Kamar yadda Hausawa ke cewa rai baƙon duniya, wannan shekarar ta 2025 ta zo wa ƴan Najeriya da rashe-rashen manyan mutane a jere, lamarin da yakan jefa duk sassan ƙasar cikin alhaini.

Duk da cewa shekarar ba ta daɗe da rabawa ba, an samu shugabannin al'umma masu fada a ji da dama da suka rasu.

Daga ciki akwai ƴan siyasa da attajirai da kuma sarakuna.

BBC ta zaɓo wasu daga cikin su:

Muhammadu Buhari

Baba

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 ne tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu yana da shekara 82 da haihuwa.

Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da jinya da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura da ke jihar Katsina. Muhammadu Buhari shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin da Buharin yake ɗan shekara huɗu.

Buhari ya rayu da ƴaƴa 10 daga matansa guda biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari wadda ita ce take yi masa takaba.

A shekarar 1962 ne Muhammadu Buhari ya shiga aikin soja yana ɗan shekara 19 da haihuwa, inda ya kasance ɗaya daga cikin matasa 70 da aka ɗauka zuwa kwalejin horon sojoji ta Nigerian Military Training wadda daga baya aka sauya mata suna zuwa Nigerian Defence Academy, a 1964.

Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin da ya hamɓarar da Janar Aguiyi Ironsi, inda aka maye gurbinsa da Janar Yakubu Gawon, a 1966.

Manjo Janar janar Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin shekarar 1983 da ya yi sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Alhaji Sehu Aliyu Usman Shagari, inda kuma shi ya zamo shugaban mulkin soja.

To sai dai kuma Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Manjo Janar Buhari juyin mulki a watan Agustan 1985, inda kuma aka tsare shi har zuwa shekarar 1988.

Ya kuma yi mulkin Najeriya wa'adi biyu a jere bayan ya yi takara sau uku bai samu nasara ba, amma sai ya samu nasara a karo na huɗu a shekarar 2015.

Aminu Ɗantata

Sanusi Dantata

Asalin hoton, X/Sanusi Dantata

A ranar Asabar 28 ga Yunin shekarar 2025 ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.

A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa BBC.

Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya shaida wa BBC.

Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha'awarsa cewa "Allah ka kashe ni a wannan gari" a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.

An gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗankasuwar na Najeriya a masallacin Annabi (S.A.W) da ke birnin Madina na ƙasar Saudiyya.

Jana'izar ta gudana ne bayan sallar magariba, inda kuma aka binne gawarsa a maƙabarta Baƙiyya mai tarihi.

An haifi Alhaji Aminu Ɗantata, a shekarar 1931. Shi ne na 15 a wajen mahaifinsa Alhassan Ɗantata, wanda ya haifi ƴaƴa 17 jimilla.

Edwin Clark

Edwin

A daren ranar Litinin, 17 Fabrairu na shekarar 2025 ne, dattijon yankin Neja Delta da ke kudancin Najeriya kuma tsohon kwamashina, Edwin Clark ya rasu, inda ya rasu yana da shekara 97 da haihuwa.

Edwin ya kasance wani babban jigo a yankin kudancin Najeriya, kuma tsohon shugaban ƙungiyar rajin kare yankin Neja Delta ta Pan Niger Delta Forum (PANDEF), inda yake yawan fitowa yana magana kan halin da ƴan yankinsa ke ciki.

An haife shi ne a garin Kiagbodo da ke yankin Ijaw na jihar Delta, ya yi aiki tare da gwamnan mulkin soja Samuel Ogbemudia, da Janar Yakubu Gowon tsakanin shekarun 1966 zuwa 1975.

Yana cikin sanatocin jamhuriya ta uku a zamanin mulkin Shehu Shagari, inda suka yi wata uku a majalisa a shekarar 1983.

Ya riƙe muƙamin kwamashinan yaɗa labarai a shekarar 1975.

Sikiru Adetona - Sarkin Ijebu

Ijebu

Asalin hoton, RNN

An haifi marigayi Sarki Sikiru Kayode Adetona, Ogbagba II, a ranar 10 ga watan Mayun shekarar 1934 a garin Ijebu Ode da ke jihar Ogun.

Sarkin wanda ake kira Awujale of Ijebu Land ya zama sarki na shekarar 1960, inda ya fito daga gidan sarautar Anikinaiya.

Marigayin ya yi kusan shekara 65 yana mulkin masarautarsa, wanda hakan ya sa yake cikin fitattun sarakuna da suka fi daɗewa a sarauta a Najeriya.

Ya rasu ne a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin shekarar 2025 yana da shekara 91.

Sheikh Abdul’aziz Dutsen Tanshi

Tanshi

Asalin hoton, Others

Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya rasu yana da shekara 68 a gidansa da ke Bauchi, misalin ƙarfe 11 na daren Alhamis a ranar uku da watan Afrilun 2025.

An haifi Malam Idris Abdu'aziz Dutsen Tanshi a garin Gwaram da ke ƙaramar hukumar Alƙaleri a jihar ta Bauchi a shekarar 1957.

Marigayin ya yi doguwar jinya kafin rasuwar tasa, inda ya yi yawon neman magani a ƙasashen da suka haɗa da Saudiyya da Indiya.

Sheikh Tanshi ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata guda uku da kuma ƴaƴa 32.