Wane ne Muhammadu Buhari?

Asalin hoton, Getty Images
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura da ke jihar Katsina. Muhammadu Buhari shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin da Buharin yake ɗan shekara huɗu.
Buhari ya rayu da ƴaƴa 10 daga matansa guda biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari wadda ita ce take yi masa takaba.
Muhammadu Buhari ya halarci makarantar allo sannan ya yi kiwon shanu, kafin ya shiga makarantar firamare a garin Daura da Mai'Adua inda ya kammala a 1953.
Daga nan kuma marigayin ya tafi zuwa makarantar sakandare ta Katsina Provisional Secondary School daga 1956 zuwa 1961.
Buhari ya samu gurbin halartar wani kwas a Burtaniya a 1960.
Aikin soji

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 1962 ne Muhammadu Buhari ya shiga aikin soja yana ɗan shekara 19 da haihuwa, inda ya kasance ɗaya daga cikin matasa 70 da aka ɗauka zuwa kwalejin horon sojoji ta Nigerian Military Training wadda daga baya aka sauya mata suna zuwa Nigerian Defence Academy, a 1964.
Haka kuma ya halarci wani kwas na ƙananan sojoji a kwalejin Aldershot da ke Burtaniya daga 1962 zuwa 1963. Kuma a watan janairun 1963 ne ya samu matsayin Second Lieutenant kuma ya jagorancin rundunar sojin ƙasa ta Second Infantry Battalion da ke Abeokuta.
Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin da ya hamɓarar da Janar Aguiyi Ironsi, inda aka maye gurbinsa da Janar Yakubu Gawon, a 1966.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga bisani kuma aka naɗa shi shugaban hukumar NNPC wadda aka fara kafawa a shekarar 1977.
Manjo Janar janar Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin shekarar 1983 da ya yi sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Alhaji Sehu Aliyu Usman Shagari, inda kuma shi ya zamo shugaban mulkin soja.
To sai dai kuma Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Manjo Janar Buhari juyin mulki a watan Agustan 1985, inda kuma aka tsare shi har zuwa shekarar 1988.
Tauraruwar Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka ba shi muƙamin ministan man fetur da ma'adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin sojin janar Obasanjo.
A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada Buhari shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kuɗaɗen rarar man da ƙasar ta samu a wannan lokaci domin gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.
Kuma ayyukan da Buhari ya yi wa Najeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu ya sa wasu 'yan Najeria son ganin ya sake zama shugaban ƙasar.
Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan sabuwar jahar Arewa maso Gabas da janar Murtala Ramat Muhammed ya ƙirƙiro.

Asalin hoton, Getty Images
Siyasa

Asalin hoton, Getty Images
Sau biyu Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin tutar jam'iyyar ANPP a 2003 da 2007, waɗanda duka bai samu nasara ba.
Rashin nasarar da ya yi karo biyu bai sauya masa ra'ayi game da siyasar Najeriya ba, kuma ya ƙaddamar da tashi jam'iyyar da ya kira CPC wadda a ciki ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da aka yi a shekarar 2011.
Sakamakon cimma haɗakar jam'iyyu da aka sanya wa suna APC, Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zaɓen shekarar 2015, inda ya kayar da abokin takararsa, Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP mai mulki.
Muhammadu Buhari ya sake samun damar yin tazarce a karo na biyu a 2019, bayan kayar da abokin takararsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.
Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, bayan samun nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga nan ne kuma Buhari ya koma mahaifarsa ta Daura inda bayan kimanin shekara guda sai koma birnin Kaduna ya ci gaba da zama.

Asalin hoton, Getty Images
Rashin lafiya a 2017

Asalin hoton, Presidency 2027
Shugaba Buhari ya shafe tsawon lokaci yana jinya a shekarar 2017, inda har ya shafe sama da kwana 100 yana jinya a Birtaniya.
Wannan al'amari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a ciki da wajen kasar.
A lokacin da rudani ya yawaita kan halin da shugaban ke ciki da kuma rashin jin ta bakin makusantansa game da ainihin abin da ke damun shugaban.
Ga jerin lokutan da shugaba Buhari ya yi fama da jinya:
- 19 ga watan Janairu - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya".
- 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya.
- 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba.
- 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
- 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba.
- 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku.
- 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu.
- 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya.
- 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya.
- 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London.
- 23 ga watan Yuli - Wasu gwamnoni da shugaban jam'iyyar APC sun ziyace shi a London.
Rashin lafiyar Buhari a 2025

Asalin hoton, Bashir Ahmed/Facebook
Ƴan Najeriya sun wayi garin ranar 3 ga watan Yulin 2025 da rahotannin da ke cewa an garzaya da tsohon shugaban Najeriyar, Muhamamdu Buhari zuwa wani asibiti a birnin London da ke Burtaniya.
An dai kwana biyu ba a ji ɗuriyar tsohon shugaban ba tun bayan komawarsa birnin Kaduna da zaman bayan kwashe kimanin shekaru biyu a mahaifarsa ta Daura bayan saukarsa daga Mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
BBC ta nemi jin ta bakin Malam Garba Shehu, tsohon maitaimaka wa Muhammadu Buhari a fannin yaɗa labarai.
Malam Garba Shehu ya ce Buhari ya tafi Burtaniya ne domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma daga baya sai ya kamu da rashin lafiya.
"Ina so in tabbatar muku cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na rashin lafiya. Yana samun magani a Birtaniya.
"Idan kuka tuna, Buhari ya sanar da kowa cewa zai je duba lafiyarsa na shekara-shekara. Ya kamu da rashin lafiya ne a can, amma ina farin cikin sanar da ku cewa yana samun sauƙi a yayin da ake ci gaba da jinyarsa.". In ji Garba Shehu.
Ya ƙara da cewa, "Muna addu'ar Allah ya ba shi cikakkiyar lafiya."
Sai dai kuma Garba Shehu bai bayyana irin rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita ba ko sunan asibitin da yake jinya a ciki ba.
To amma rahotanni na rawaito wasu majiyoyi daga makusanta da iyalan tsohon shugaban cewa yana sashen kulawa da marasa lafiya na musamman bisa fuskantar rashin lafiya mai tsanani.











