Me ya sa ƴansiyasar Najeriya ke rububin ziyartar Buhari?

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana cigaba da tattaunawa a fagen siyasar Najeriya kan yadda jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar ke rububin ziyartar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna, lamarin da wasu ke cewa akwai alamar tambaya.
A baya-bayan nan ƴansiyasa da manyan jami'an gwamnati na yawan kai wa tsohon shugaban ziyara tun bayan da ya koma gidansa na Kaduna daga Daura, inda ya shafe shekara biyu tun bayan sauka daga mulki.
Bayan da Muhammadu Buhari ya sauka daga mulkin Najeriya a ƙarshen wa'adinsa a shekarar 2023, sai ya koma garinsa na Daura da zama.
Lokacin yana can ma an kai masa ziyara, amma ziyarar ta ƙaru bayan ya koma Kaduna, kuma ta fi jan hankali.
Duk da cewa yawancin masu ziyarar ba su bayyana siyasa a matsayin maƙasudin ziyarar ba, masu sharhi da dama na ganin lamarin ba zai rasa nasaba da siyasar shekarar 2027 ba.
A siyasar Najeriya, an daɗe ana ganin irin haka, musamman a jamhuriya ta huɗu, inda tsofaffin sojoji suka kasance iyayen gida a siyasar ƙasar, wanda hakan ya sa ƴansiyasa ke ziyartarsu domin neman goyon bayansu ko kuma aƙalla neman tabarrakin siyasa.
An sha ganin ƴansiyasa suna ziyartar tsofaffin shugaban Najeriya irin su Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Olusegun Obasanjo da Abdulsalami da Abubakar da sauransu, lamarin da za a iya cewa an fara sunnatar da shi a siyasa.
Me hakan ke nufi?

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook
Domin jin abin da hakan ke nufi a siyasance, BBC ta tuntuɓi Dakta Kabiru Sa'id Sufi, malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa, inda ya ce neman tabarraki.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin harkokin siyasar ya ce tun kafin a kawo wannan gaɓar dama jiga-jigan ƴan siyasa musamman waɗanda suka yi aiki da shi suna kai masa ziyara.
Sai dai ya ce ziyarar su Atikun ta sha bamban, "saboda mutane ne da tafiyarsu ba ɗaya ba ce a siyasance. Yanzun ma za a iya cewa har yanzu Atiku yana PDP, shi kuma El-Rufai yana SDP," in ji shi.
Sai dai ya ce yana ganin yunƙuri ne na tuntuɓa, "suna so jama'a su ga kamar sun samu albarka daga manyan ƙasa."
Amma a game da ko ana zuwa ziyarar ne domin neman 'guguwar Buhari' da ake tunanin tana sauya ra'ayin masu zaɓe musamman a arewacin Najeriya, sai Sufi ya ce ba ya tunanin haka.
"Gaskiya ba na tunanin haka, ba na jin ana masa wannan kallon yanzu duba da cewa tun bayan saukarsa daga mulki kusan bai shiga wani abu da ya shafi siyasa ka'in da na'in ba, ko na tallata wani ko makamancin haka. Kawai dai ziyara ce ta neman tabarraki ba lallai ta cewa ana ganin yana da wannan tasirin ba a siyasance," in ji Dr Sufi.
Ya ce ko da neman tabarrakin ne, "ka ga ai shugabannin APC sun kai masa ziyara. Idan ma tabarrakin su Atiku suka je nema, ko kuma wani tagomashin suka je nema, suna ganin sun shafe wannan tagomashin da ziyarar da su Atikun ta samar."
Kasancewar ba Buhari ba ne kaɗai tsohon shugaban da jiga-jigan ƴansiyasa suke kai wa ziyara, Dakta Sufi ya ce ana musu kallon waɗanda suke da tsawatarwa, "waɗanda za su iya ba da shawara ko da kuwa ba sa cikin siyasa."
"Ina gani ƙoƙari na nuna wa al'umma cewa su masu biyayya ne ga mazan jiya. Suna nuna cewa sun samu tabarrakin waɗanda suke kai wa ziyarar ko da kuwa ba za su taya su yaƙin zaɓe ba, kuma ko da ba su saka baki ba, amma a kan yi amfani da shi a matsayin wani abu da zai taimaka siyasarsu."
Komawar Buhari Kaduna da ƙaruwar ziyarar ƴansiyasa

Asalin hoton, Bashir Ahmad
A watan Fabrairun wannan shekarar ta 2025 ne Muhammadu Buhari ya yi sallama da Daura domin komawa Kaduna.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna Uba Sani da wasu jiga-jigan ƴansiyasa ne suka raka shi zuwa gidan nasa da ke tsakiyar birnin Kaduna.
Ana cikin haka ne guguwar siyasa a ƙasar ta canja, inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya soki gwamnatin Tinubu da gaza cika alƙawura da watsi da wasu ƴan jam'iyyar.
Ziyara ta ƙarshe da ta fi ɗaukar hankalin al'umma ita ce wadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya kai wa tsohon shugaban ƙasar, inda jim kaɗan bayan hakan ya ayyana ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar SDP, wani lamari da ake ganin zai sauya salon siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen shekara ta 2027.
Da yake jawabi kan ficewar tasa daga APC, El-Rufai ya ce bai bar jam'iyyar mai mulki ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun.
"Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma'a na faɗa masa cewa zan bar jam'iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba," in ji shi.
Jawabin na El-Rufai ya tayar da ƙura, inda daga bisa Buhari ya fitar da sanarwar cewa shi yana nan daram a APC.
Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakinsa, Garba Shehu ya fitar, inda ya ce ba ya so ya bar kowa a cikin ruɗani game da inda yake, domin a cewarsa ba zai taɓa juya wa jam'iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara har ya yi shugabancin ƙasa na wa'adi biyu baya ba.
"Ni ɗan APC ne, kuma na fi so ana alaƙanta da jam'iyyar, sannan zan yi duk mai yiwuwa wajen tallata jam'iyyar."
A makon jiya ne dai tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar ya ziyarci Buharin a Kaduna.
Daga cikin waɗanda suka raka Atiku akwai tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ƴansiyasa.
Sai dai Atikun bai yi ƙarin haske kan ko akwai wani abu mai alaƙa da siyasa da suka tattauna da tsohon shugaban ƙasar ba a lokacin ziyarar, inda suka ce ziyara ce kawai ta gaisuwa da zumunci.
Kwatsam bayan ziyarar su Atiku, sai shugabannin APC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje, suka kai masa ziyara a gidan nasa na Kaduna.
Sai dai kamar yadda Dakta Sufi ya bayyana, bayan ziyarar shugabannin APC a gidan Buhari, Ganduje ya ce duk wata haɗaka da ake shirin ƙullawa ba za ta ci nasara ba.
Ganduje ya ce ziyarar su Atikun ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa ''suna son ƙulla wata haɗaka ce da ba za ta yi tasiri ba."
''Daga abin da muka gani mutane ne da ba za su iya haɗuwa ƙarƙashin inuwa guda ba'', in ji shi.
Shugaban jam'iyyar ta APC ya ce a shirye suke kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.
Ganduje ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam'iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin.










