Wane ne marigayi Aminu Ɗantata?

Asalin hoton, X/Barau Jibrin
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa BBC.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya shaida wa BBC.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha'awarsa cewa "Allah ka kashe ni a wannan gari" a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.
Mustapha ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa sun samu amincewar hukumomin Saudiyya domin binne marigayin a Madina ranar Litinin.
Sai dai tuni aka yi masa sallar jana'iza daga nesa a Masallacin Umar bn Kattab da ke birnin Kano a ranar Asabar.
Tun da farko iyalansa sun ce idan buƙatarsu ta binne shi a Saudiyya za ta ɗauki lokaci to za su mayar da shi Kano domin yin jana'izar tasa a gida.
Mazaunin unguwar Koki da ke ƙwaryar birnin Kano a arewacin Najeriya, Aminu ya bar mata uku, da 'ya'ya 21 - maza biyar, mata 16 - da kuma jikoki 121.
Aminu Ɗantata ɗa ne ga marigayi Alhaji Alhassan Ɗantata, shi ma fitaccen attajiri da ya shahara a ƙarni na 20.
A watan Mayun 2024 Ɗantata ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ziyara a fadar shugaban ƙasa, bayan Tinubun ya kai masa ziyara a Kano kafin babban zaɓen 2023.
Shugaban ƙasar ya bayyana mutuwar Ɗantata a matsayin "rashi ga ƙasa baki ɗaya".
Abu ne mai wuya a iya ƙare tarihin Aminu Ɗantata a labari ɗaya, amma dai mun duba kaɗan daga tarihin rayuwarsa.
Ilimi da kasuwanci

Asalin hoton, X/Sanusi Dantata
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Alhaji Aminu Ɗantata, a shekarar 1931. Shi ne na 15 a wajen mahaifinsa Alhassan Ɗantata, wanda ya haifi 'ya'ya 17 jimilla.
Mutane kan kira shi Aminu Dogo saboda tsawon da yake da shi.
Ya yi karatun firamare a Dala Primary School da ke birnin Kano, da kuma na Islamiyya kafin ya halarci sakandaren da mahaifinsa ya gina.
Iyalin Ɗantata kan fara koyon neman kuɗi tun suna da ƙananan shekaru.
"Mu a dinginmu yaro kan fara neman kuɗi tun yana da shekara biyar ko shida ko bakwai," kamar yadda ya bayyana cikin wata hira ta musamman da kafar talabijin ta Trust TV a watan Mayun 2024.
"Mahaifinmu kan ce mana 'kun ga yadda mutane ke kawo gyaɗa a raƙuma da jakuna, to ya kamata ku ma ku san yadda za ku fara neman kuɗi. Lokacin da muke zuwa makaranta kuma, mahaifinmu kan yi amfani da lokutan hutu yana koya mana yadda za mu yi kasuwanci."
Ya fara nisa a harkokin kasuwanci tun yana shekara 17 lokacin da ya maye gurbin yayansa Ahmadu Ɗantata a matsayin shugaban tashar kasuwancin da mahaifinsu Alhassan ya kafa da ke garin Bichi a jihar Kano.
Kafin rasuwar mahaifin nasu a 1955, Alhaji Alhassan ya kafa kamfani mai suna Alhassan Ɗantata and Sons. Daga baya Aminu ya koma jihar Sokoto, inda ya shugabanci reshen kamfanin a can.
Ya zama mataimakin shugaban kamfanin a 1958, yayin da Ahmadu ke shugaba, sai kuma ya maye gurbin yayan nasa a matsayin shugaba bayan rasuwarsa a 1960.
Ya kafa ko kuma an kafa kamfanoni da dama tare da shi, ciki har da na man fetur mai suna Express Petroleum & Gas Company Ltd, da bankin Jaiz Bank.
Wani kamfaninsa na gine-gine ne ya gina kwalejin horar da tuƙin jirgin sama da ke Zariya a shekarar 1960.
Yana cikin majalisar ƙoli ta farko da ta kafa bankin kasuwanci na gwamnatin Najeriya Nigerian Industrial Development Bank (NIDB), wanda a yanzu ya koma Bank of Industry (BOI).
Zuwa yanzu babu wasu alƙaluma da ke bayyana ɗimbin dukiyar da ya mallaka.
Siyasa

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Duk da cewa Aminu Ɗantata ya fi shahara a fannin kasuwanci da kuma tallafa wa jama'a, ya kuma taɓa harkokin siyasa tun daga shekarun 1963.
Ya taɓa zama ɗanmajalisar wakilai a tsohuwar jihar Kaduna na wa'adi ɗaya lokacin Jamhuriya ta Farko daga 1963 zuwa 1966.
Bayan kifar da gwamnatin farar hula ta lokacin ne kuma ya koma Kano, inda gwamnan mulkin soja Audu Bako ya naɗa shi kwamashinan harkokin kasuwanci a 1968.
Ɗantata ya ce yayin da ake shirin shiga Jamhuriya ta Biyu, sai wasu mutane da dama suka fara neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Wasu kuma sun nemi ya tsaya takarar gwamnan Kano, cikinsu har da tsohon ɗan gwagwarmaya kuma ɗansiyasa Mallam Aminu Kano. Sai dai bai amince da kiran nasu ba.
"Dalilin da ya sa na ƙi yarda shi ne, a matsayina na ɗankasuwa ina ganin Allah ya riga ya zaɓa min hanyar da zan iya taimakawa wajen cigaban jihata, da ƙasata, da ma al'umma baki ɗaya," in ji shi cikin hirar ta Trust TV.
"Saboda haka babu wani dalili da zai sa na koma siyasa."
Filaye da gidajen da Aminu Ɗantata ya mallaka
Ɗaya daga cikin abubuwan da mazauna jihar Kano suka fi sanin Aminu Ɗantata da shi shi ne yawan filaye da gidaje, har wasu ma na tunanin shi kansa bai san yawan filayen da yake da su ba.
Tabbas haka lamarin yake, domin kuwa ya faɗa da bakinsa cewa bai san adadin filayen da ya mallaka ba a rayuwarsa, kuma abin asali ya samo.
Mahaifinsu Alhassan na da filayen da ba su san yawansu ba, a cewarsa.
Alhaji Alhassan ya dinga bi yana sayen filaye a duk inda ake da tashoshi na jirgin ƙasa a faɗin Najeriya saboda yadda suke saukewa da kuma loda kayayyakinsu na gyaɗa da sauransu.
"[Sayen] fili babbar hanya ce ta riƙe jari," in ji Aminu Ɗantata. "Ina da filaye a duka faɗin Najeriya. [Kuma] har a inda ma wasu ba su iya samun damar sayen fili, ni ina da su.
"Ina da su a Saudiyya, da Dubai, da Masar, da Ingila, da Jamus, da Amurka. Lokacin da na tura yara makaranta, sai na sayi wani gida a Florida [Amurka].
"Ba na jin zan iya faɗa muku yawan filayen da na mallaka."











