Ko Dangote zai yi nasara kan 'waɗanda suka kankane’ harkar man fetur a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Will Ross
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa regional editor, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 7
Fara aikin matatar man fetur a Najeriya mallakin mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, abu ne da ya kamata ya zamo cikin labari mafi daɗi a ƙasar cikin shekarun nan.
To amma ƴan Najeriya da dama za su auna mizanin alfanun matatar ne kan abubuwa biyu: Shin hakan zai sauƙaƙa farashin man fetur?
Abin takaicin shi ne, da wuya a samu hakan - sai dai idan farashin man fetur ya sauko a kasuwannin duniya.
Sai kuma: ko za mu ci gaba da ganin dogayen layukan man fetur a gidajen mai?
Wataƙila a samu ɓacewar dogayen layukan man fetur ɗin a gidan mai amma wannan ɗin ma ya dogara ne ga ɗabi'ar mutanane da Dangote ya kira "waɗanda suka kankane harkar man fetur".
Tun bayan gano tarin arziƙin ɗanyen man fetur a Najeriya a shekarar 1956, harkar haƙowa da tace ɗanyen man fetur ɗin ya kasance cikin mummunar badaƙala, kuma ana zargin gwamnatocin da suka gabata da hannu a ciki.
Abu ne mai matuƙar wahala mutane su san yadda ake jujjuya kuɗade a ɓangaren, to amma a duk lokacin da ka ga an yi kanun labaran da ke cewa "Kamfanin man fetur na Najeriya ya gaza biyan gwamnati harajin mai har dala biliyan 16", kamar yadda ta faru a shekara 2016, za ka fahimci cewa lallai akwai babbar matsala.
A cikin shekaru biyar da suka gabata ne kawai kamfanin man fetur ɗin na Najeriya ya fara wallafa bayanin hada-hadar kuɗaɗensa.

Asalin hoton, Getty Images
NNPC na samun biliyoyin dala a kowace shekara daga haƙar ɗanyen man fetur.
Sai dai tsawon shekaru, karkashin gwamnatoci da suka gabata, kamfanin ba ya sanya wasu daga cikin kuɗaɗen da yake samu a lalitar gwamnati kamar yadda gwamnonin jihohi da ƴan majalisar tarayya ke zarginsa da yin zuƙe a kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafin main fetur.
NNPC bai ce uffan ba ga buƙatar ji daga gare shi ko kuma mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge, amma a watan Yuni ya musanta cewa ya yi "ƙarin gishiri a bayanansa a wajen gwamnatin tarayya."

Asalin hoton, Getty Images
Bayan hawa kan mulki a watan Mayu 2023, shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur - nan da nan farashin mai ya haura.
Ƙaruwar farashin mai, da ƙarancinsa da kuma ci gaba da faɗuwar darajar kuɗin naira sun janyo kunci ga al'umma a faɗin Najeriya, inda mutane da yawa suka koma amfani da injunan bayar da lantarki domin samun wuta da kuma cajin wayoyinsu.

Ana fatan cewa zuwan matatar mai ta Dangote zai sa a samu saukin cin hanci da almundahana a ɓangaren mai.
Ya san cewa zai harzuka wasu waɗanda suke cin gajiyar almundahanar da ake yi a ɓangaren lokacin da ya fara aikin matatar da ta kai dala biliyan 20.
Sai dai, ya ce bai yi tsammanin zai gamu da irin kalubalen da yake fuskanta a yanzu ba.
"Na san za a samu rikici. Sai dai ba san cewa waɗanda suka kankane ɓangaren mai sun fi waɗanda suka kankane ɓangaren kwayoyi ba," kamar yadda Dangote ya faɗa wa taron masu zuba jari a watan Yuni.
"Ba sa son daina almundahanar da suke yi. Gungun mutane ne masu aikata laifi. Dangote ya zo kuma zai janyo musu cikas. Harkallarsu na cikin haɗari," in ji Emmanuel, wani masani kan ɓangaren mai.
Ƙorafe-korafen jama'a kan NNPC, ya ƙara tabbatar da zargin da ake yi na badakala a harkar mai a ɓangaren.
Matatar Dangote da ke jihar Legas na da girman da za ta iya samar da ganga 650,000 na ɗayen mai a rana.
Za ku yi tunanin cewa kafa kamfanin a Najeriya zai kawo sauƙi wajen samar da mai amma ba haka batun yake ba, sai ma muka ji cewa: "Matatar Dangote ta sayi ɗanyen mai daga Brazil."
Hakan ya biyo saɓani kan samarwa da kuma farashi. Kamfanin NNPC ya yi ƙorafi kan salon tattaunawa kan farashi da Dangote ke yi.
Ɗanyen man Najeriya ba shi da sinadarin farar-wuta (Sulphur) mai yawa sannan kuma ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi daraja a duniya.
Sai dai lokacin da aka fara tattaunawa kan farashin mai, Farouk Ahmed, shugaban hukumar kula da harkokin sayar da mai (NMDPRA), ya zargi Dangote da son "tsawwala kuɗi" a man fetur ɗin sa.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangote ya yi korafin cewa ba a ba shi yawan ɗanyen mai da aka ware masa tun da farko ba, sai dai ko da bayan amincewa da farashin mai, yana buƙatar shigo da ɗanyen mai.
"NNPC ba shi da isasshen ɗanyen mai da zai bai wa Dangote. Duk da irin waɗannan sharuɗɗa na samar wa matatar ɗanyen mai, NNPC ya ƙasa samar da ɗanyen mai sama da ganga 300,000 a rana," in ji Mista Akinosho.
Ya ce hakan ya faru ne saboda NNPC yana biyan bashin da ya riga ya karɓa da ɗanyen mai.
A watan Agusta 2024 kamfanin ya ciyo bashin dala biliyan uku daga Afreximbank. Inda zai biya bashin da gangar ɗanyen mai miliyan 164.
A watan Satumba, NNPC ya sanar da cewa bashi ya yi masa katutu. An ruwaito cewa ana bin sa bashin da ya kai dala biliyan shida na mai da aka shigo da shi cikin ƙasar.
Man fetur ɗin da Najeriya ke samarwa ya ragu a ƴan shekarun nan daga ganga miliyan 2.1 a rana a 2018 zuwa kusan ganga miliyan 1.3 a rana a 2023.
NNPC ya sha bayyana cewa satar ɗanyen mai na daga cikin dalilai da ke janyo raguwar samar da mai a ƙasar.
Ya ce a cikin mako ɗaya kaɗai - daga 28 ga Satumba zuwa 4 ga Oktoba - an samu bayanai na satar ɗanyen mai har 161 a faɗin yankin Neja Delta da kuma "gano" haramtattun matatun mai 45.
Sai dai Ms Anku ta yi imanin cewa "NNPC da kuma ɓangaren mai ya zuzuta batun satar ɗanyen mai."
"Korafi ne da za a iya karɓa," in ji ta.
Ta kuma ce akwai wasu abubuwa da ke janyo raguwar samar da mai da suka haɗa da kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa da ke sayar da rijiyoyin man su - inda wasu daga ciki ba za su iya aiki yadda ya kamata ba bayan samar da mai na tsawon shekara 60.

Asalin hoton, Getty Images
Dangote mai shekara 66, wanda shi ne mutum na biyu mafi arziki a Afrika, a cewar mujallar 'Bloomberg Billionaire Index', ya samu arzikinsa ne ta hanyar samar da suminti da sikari.
Ya sha musanta zargin da ake yi cewa ya samu alfarma daga wajen ƴan siyasa da ke kan mulki, waɗanda suka taimaka masa samun tagomashi a kasuwancinsa.
A yanzu akwai waɗanda ke sukar tsare-tsaren Dangote a daidai lokacin da ake samu saɓani tsakaninsa da hukumomi, zargin da ya sake fitowa fili idan aka zo ga batun samar da man fetur a Najeriya.
"Dangote ya buƙaci in daina bayar da lasisin shigowa da mai kuma kowa ya koma saya a wurinsa. Abin da na ce 'a'a saboda ba abu ne mai kyau ga kasuwa ba. Akwai buƙatar makamashi sosai," in ji Ahmed shugaban NMDPRA.
Sai dai Dangote bai ce uffan ba kan zargin, amma ya ce yana da kyau ƴan kasuwa su sayi man fetur daga wajensa a maimakon fita waje.
Saɓani tsakanin kamfanin NNPC da kuma Dangote kan samarwa da kuma farashin man fetur, ya rikiɗe zuwa wani saɓani da ƴan kasuwar mai da suka ƙi sayen mai daga matatarsa.
Lamarin ya kuma haɗa da zargin cewa wasu ƴan kasuwa na sayen mai mara inganci daga Rasha wanda ake haɗawa da wasu abubuwa kafin shigo da shi Najeriya.
Sai dai ba kowane mutum ne ke nuna damuwa ko kuma mamaki kan saɓanin da ake samu ba.
Ms Anku ta yi nuni da darussa da aka koya daga ƴan kasuwa can baya a ƙarni na 19.
"JP Morgans da Stanfords - ba su ji da sauki ba. Haka ne ya sa suka tafi wurin gwamnati don samun goyon baya da kuma tallafi don gina layin dogo da sauransu.
"Ina ganin lamarin a matsayin wasan kwaikwayo kuma abin da aka saba yayin da ake koƙarin canza tsarin tattalin arziki. Akwai masu hasara, za su yi ta suka. Babu wata damar cewa za su hana matatar yin aiki ko sayar da manta a kasuwannin Najeriya... a ganina."
Haka kuma samar da matatar ya janyo cece-kuce kan ingancin man fetur a kasuwanni. Al’amari ne mai muhimmanci idan aka yi la’akari da ɗimbin injunan bayar da lantarki da ke fitar da hayaki a faɗin Najeriya sakamakon ƙarancin lantarki.
"Kowace rana ina tashi da jin warin abin da na tabbata zai iya kashe ni. Hakan ya faru ne saboda rashin ingancin man dizal,” in ji Mista Akinosho.
Yana ganin matatar mai ta Dangote a matsayin wata dama ta samar da ingantaccen man fetur a Najeriya wanda zai fi dacewa ga injuna da kuma lafiyar mutane.
Amma a halin yanzu zai yi wuya ’yan Najeriya, waɗanda ke fama da tsadar rayuwa, su kasance da kyakkyawan fata.
Ana ta cece-kuce tsakanin jami’an matatar man Dangote da ‘yan kasuwa da kuma masu kula da harkokin man fetur a kafafen yaɗa labarai.
An zargi dukkanin ɓangarorin da ɓoye wasu bayanai da alkaluma waɗanda suka sa mutane ke yin hasashen abin da ke faruwa a cikin masana'antar da cewa ba shi da tushe.
"Kowa mai laifi ne. Babu wani gwarzo a nan,” in ji Mista Akinosho.











