Ko sabuwar matatar man Dangote za ta magance matsalar man fetur a Najeriya?

Asalin hoton, FACEBOOK/Buhari Sallau
A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar matatar mai mallakin mutum mafi arziƙi a Afirka, Aliko Ɗangote.
An ƙaddamar da matatar ce kimanin shekaru 67 bayan da Najeriya ta fara samar da ɗanyen man fetur a 1957.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubale daban-daban a ɓangaren na man fetur.
Najeriya ta faɗo zuwa ta biyu a jerin kashashen nahiyar Afirka mafiya fitar da man fetur, inda a yanzu take a bayan Angola.
Wasu daga cikin abubuwa da ke haifar wa Najeriyar samun koma baya a yawan man da take hakowa a kullum sun hada da satar danye man ta barauniyar hanya, da barnata danyen man ta hanyar fasa bututan mai da kuma rashin tsaro.
Tun bayan da aikin samar da tatar man ya kankama al’ummar Najeriya sun zaku su ga fara aikinta, kasancewar suna kyautata zaton cewa za ta kawo sauki ga samuwar man fetur a fadin kasar.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Mene ne zai sauya?
Dakta Ahmed Adamu, masani ne kan man fetur a Najeriya, ya ce matatar man fetur ta Ɗangote za ta amfani Najeriya ne idan aka ɗauki wasu muhimman matakai biyu:
Samar da isasshen danyen mai: Dakta Ahmed Adamu ya ce matuƙar ana son matatar ta yi aiki yadda ya kamata ta yadda za ta samar da sauƙi, to dole ne sai an samar mata da isasshen ɗanyen mai.
A cewar sa yanzu haka Najeriya ba ta samar da isasshen ɗanyen mai da zai wadaci matatar sanadiyyar matsaloli na fasa bututai da kuma satar ɗanyen mai.
Ya ƙara da cewa matuƙar babu isasshen ɗanyen man fetur ɗin hakan zai tilasta wa matatar nemo ɗanyen mai a wasu ƙasashen, wanda hakan zai ƙara tsadar ɗanyen man da take buƙata.
Cire tallafin man fetur: Dakta Adamu ya ce ya kamata a cire tallafin man fetur ta yadda za a sakar wa matatar mara wajen sayar da man fetur a Najeriya kamar yadda ake sayarwa a sauran ƙasashe ba tare da tarnaƙi ba.
Ya ce kasancewar matatar kamfani ne mai zaman kansa ya kamata a bar shi ya yanke hukunci a kan farashin da yake son sayar da tataccen man fetur ɗin.
A cikin bayanin nasa, dakta Ahmed ya ce samar da matatar man fetur a Najeriya zai rage wa ƙasar wahalar da take sha wajen samun kuɗaɗen shiga na ƙasashen ƙetare kamar dalar Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Sabuwar matatar ta Dangote za ta zama mafi girma a Afirka idan ta fara aiki nan da 'yan makwanni.
Idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.
An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta tsakiya da yankin Amurka.
Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.
Wani bayani da rukunin kamfanonin Dangote ya fitar ya ce an yi amfani da na’urorin yashe ƙasa mafiya girma a duniya, inda aka yashe ƙasa mai yawan gaske a wurin, aka kuma kashe kuɗi kimanin yuro miliyan 300 a aikin.

Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU
An dai ƙiyasta cewa Najeriyar na da ɗanyen man fetur da ya kai yawan kimanin ganga biliyan 16 zuwa 22 jibge a ƙarƙashin ƙasa.











