NNPCL ya fara dakon mai daga matatar Dangote a karon farko

Matatar Dangote

Asalin hoton, @nnpclimited/X

Lokacin karatu: Minti 3

Babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya fara dakon mai daga matatar mai ta Dangote dake birnin Legas.

Dama dai NNPCL ɗin ya sanar cewa a yau Lahadi 15 ga watan Satumba zai fara ɗauko man daga matatar da ta fi kowacce girma a nahiyar Afirka.

Tun a ranar Asabar NNPCL ya ce ya shirya manyan motocin dakon mai a harabar matatar da ke unguwar Ibeju-Lekki a birnin Legas, domin lodin man.

Kawo yanzu kusan manyan motocin dakon mai 300 ne ke harabar matatar inda tuni suka fara loda man.

Tankoki 10 ne ake iya yi wa lodi a lokaci guda a matatar, yayin da saura za su jira a kammala loda wa wasu sannan suma su isa wurin lodin.

Mamba a kwamitin shugban ƙasar kan saye da sayar da man, Zacch Adedeji, ya ce daga ranar 1 ga watan Oktoba NNPLC, zai fara jigilar ganga 385,000 a kowace rana, kuma kamfanin zai sayi tataccen man ne da kuɗin kasar wato naira.

“Ina mai farin cikin sanar da cewa an kammala duk wani shiri na fara jigilar rukunin farko na mai daga matatar Dangote,” in ji mista Adedeji.

Saura yarjejeniyoyin da kwamitin ya cimma sun haɗa da sayen da man dizel daga matatar ga kowane mai sha'awa, to amma NNPCL ne kawai matatar za ta sayar wa man fetur.

Ana dai sa ran shigar man Dangoten kasuwa, zai kawo sauƙi ga matsalar mai da ƙasar ke fuskanta a baya-bayan nan.

Abin da ya kamata ku sani a kan matatar mai ta Dangote

NNPCL

Asalin hoton, NNPCL/X

Matatar wadda ke yankin Ibeju-Lekki a birnin Legas na da faɗin hekta kusan 2,635.

A cewar Rukunin Kamfanonin Dangote, matatar man ita ce irinta mafi girma a duniya da ke da cibiya guda ɗaya da ke iya tace ɗanyen mai har ganga 650,000 a kullum.

Matatar na da ƙarfin da za ta wadatar da buƙatar Najeriya dangane da man fetur har ma a yi ragowar da za a fitar wajen domin sayarwa.

An tsara matatar yadda za ta iya tace nau'ika da dama na ɗanyen man fetur, ciki har da na ɗanyen man ƙasashen Afirka da wasu na Gabas ta Tsakiya da kuma na Amurka.

Matatar Dangoten na da tankuna 177 da za su iya ajiye litar mai biliyan 4.742.

A cewar wata sanarwa daga kamfanin, Dangote zai yi amfani da wasu jiragen ruwa na yashe teku mafi girma a duniya domin aikin kwashe yashin gaɓar teku da ya kai zurfin murabba'in mita miliyan 65 a kan yuro miliyan 300.