Manyan abubuwa takwas game da rayuwar marigayi Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Lokacin karatu: Minti 7

Tsohon shugaban Najeriya, ɗaya daga cikin ƴansiyasa na ƙasar da aka fi nuna wa ƙauna, ya rasu yana da shekara 82.

Ɗan siyasa wanda siyasarsa ta sha bamban da ta saura, ya kasance mara son hayaniya kuma mai jajircewa.

Buhari ya kasance sahun gaba a cikin shugabanni Najeriya ƙalilan da ake yi wa kallon masu gaskiya.

Tsohon babban mai taimaka masa kan yaɗa labarai Femi Adesina, ya ce "babu ta yadda za a yi ka alaƙanta Buhari da rashawa".

Akasarin waɗanda ke ƙaunar Buhari sun yi hakan ne sanadiyyar ɗabi'unsa na gaskiya da son bin doka.

BBC ta duba wasu muhimman abubuwa da suka faru a rayuwar tsohon shugaban ƙasar:

Rayuwar maraici

An haifi Muhammadu Buhari ne a watan Disamban 1942 a Daura da ke jihar Katsina, shekaru 18 kafin samun ƴancin kan Najeriya.

Mahifinsa wanda Bafulatani ne ya rasu tun lokacin da Buhari ke da shekara huɗu a duniya, inda ya girma a hannun mahaifiyarsa ƴar ƙabilar Kanuri.

A wata tattaunawa cikin shekara ta 2012, Buhari ya faɗi cewa shi ne na 23 a cikin ƴaƴan mahaifinsa, kuma na 13 a wurin mahaifiyarsa.

Ya bayyana cewa abin da kawai zai iya tunawa game da rayuwa tare da mahaifinsa shi ne wani lokaci da doki ya kayar da su, shi da mahaifinsa da wani ɗan'uwansa.

Tarwatsa samamen sojojin Chadi a Najeriya

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Muhammadu Buhari

Daya daga cikin abubuwan da suka ƙara ɗaga sunan Buhari a Najeriya shi ne jagorantar wata bataliyar Najeriya a wani ƙwarya-ƙwaryar rikici da aka samu tsakanin Najeriya da maƙwaftciyarta, Chadi.

Lamarin ya faru ne a shekara ta 1983, lokacin da sojojin Chadi suka mamaye wasu tsibirai na tafkin Chadi.

Buhari ya jagoranci bataliyar da ta kora sojojin na Chadi daga yankin.

Mulkin soja

A watannin ƙarshe na shekara ta 1983 ne sojoji suka tunsturar da gwamnatin shugaban Najeriya na wancan lokaci, Shehu Shagari.

Buhari wanda a lokacin yake da muƙamin manjo-janar ya zama shugaban mulkin soja bayan juyin mulkin.

Buhari ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka kitsa juyin mulkin, kawai an ɗora shi ne, inda ya ce kuma daga baya ainahin waɗanda suka ɗora shin suka cire shi.

Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa ya taka rawa a juyin mulkin na Shagari fiye da yadda yakan bayyana.

Mulkin nasa bai yi tsawo ba, inda aka yi masa juyin mulki bayan wata 20.

Yaƙi da rashin ɗa'a

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A tsawon lokacin da Buhari ya mulki Najeriya a matsayin soja, abubuwa da dama sun sauya.

Abin da aka fi tunawa kan mulkin nasa na farko su ne tsarinsa na yaƙi da rashin ɗa'a, sai kuma yaƙi da rashawa.

Kimanin ƴan siyasa 500 ne gwamnati ta ɗaure a wani mataki na yaƙi da rashawa da ɓarnata dunkiyar al'umma.

Wasu sun kalli waɗannan tsare-tsare na gwamnatin Buhari a matsayin kama-karya, wasu kuma na kallon hakan a matsayin abin a yaba wajen yaƙi da rashawa, abin da ya yi wa ƙasar katutu kuma yake hana ta ci gaba.

Waɗannan matakai na daga cikin abubuwan da suka sa Buhari ya samu laƙabin mai gaskiya.

A wani ɓangare na shirin yaƙi da rashin ɗa'a, an tursasa wa mutane bin layi a wurin hawa mota, an kuma tursasa wa waɗanda ake zargi da ɓoye kaya fitowa da su su sayar.

An kuma riƙa hukunta ma'aikatan gwamnati da ke zuwa ofis a latti, cikin irin wannan hukunci har da tsallen kwaɗo.

Sauye-sauye ne da ba a saba gani ba, sai dai wasu sun ce lamarin ya zama tamkar danniya, musamman ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na samar da dokar taƙaita ƴancin ƴan jarida.

Wani abu da ake tunawa da shi a cikin matakan da gwamnatin Buhari ta wancan lokaci ta ɗauka shi ne sauya takardar naira, inda aka ƙayyade lokacin da mutane za su iya sauya tsofaffi da sabbi.

Haka nan an kulle shahararren mawaƙin nan Fela Kuti bisa zargin safarar kuɗi.

Ɗauri bayan juyin Mulki

Bayan shafe wata 20 a kan Mulki, abubuwa sun yi ƙamari, kuma a wannan lokaci ne aka tuntsurar da gwamnatin Buhari, inda Janar Ibrahim Babangida ya karɓi mulki.

Bayan hamɓarar da shi ne kuma aka kulle shi har tsawon wata 40 a garin Benin City.

An saki Muhammadu Buhari a watan Disamban 1988, bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Asusun Rarar Man Fetur (PTF)

Tun bayan sakin sa Muhammadu Buhari ya koma yin rayuwa mai sauƙi.

Kusan an daina jin ɗuriyarsa har sai lokacin da shugaban mulkin soji na Najeriya Sani Abacha ya naɗa shi shugaban Asusun Rarar Man Fetur na Najeriya (PTF).

Asusun na samu kuɗinsa ne daga rara da aka samu bayan ƙara farashin man fetur, inda ake amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan raya ƙasa.

An bayyana PTF a matsayin shiri wanda ya yi nasara, sanadiyyar irin tallafin da shirin ya bayar a ɓangarori daban-daban na ci gaban ƙasa.

Yin takar sau uku ba tare da nasara ba

...

Asalin hoton, Buhari Sallau

A farkon shekarun 2000 ne Muhammadu Buhari ya shiga harkar siyasa, lamarin da ya zamo wata doguwar tafiya mai cike da faɗi-tashi a ƙoƙarinsa na komawa kann muƙamin shugaban ƙasa.

A shekarar 2003 ya yi takarar shugaban ƙasa, sai dai ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Olusegun Obasanjo.

Ya sake yin takarar shugaban ƙasa a 2007, inda nan ma Umaru Musa Yar'adua na jam'iyyar PDP ya kayar da shi.

A 2011, bayan ya yi takara a karo na uku ba tare da nasara ba, Buhari ya bayyana aniyarsa ta janyewa daga siyasa.

A lokacin ya ce "wannan shi ne na uku kuma na ƙarshe gare ni, ba zan sake fitowa takarar shugaban ƙasa ba, ba na buƙatar komai kuma babu wani abu da zan sake faɗi wanda ban faɗa ba".

Mulkin farar hula

...

Asalin hoton, Buhari Sallau

To sai dai wasu abubuwa biyu sun sake mayar da Buhari cikin fagen siyasa gabanin zaɓen 2015.

Yayin da Goodluck Jonathan ya kusa kai rabin wa'adin mulkinsa, farin jinisa ya yi ƙasa sosai. Matsalar tsaro, musamman ta Boko Haram, da ƙaruwar matsin rayuwa da zarge-zargen rashawa sun sa tauraruwar Jonathan ta dusashe.

Daga nan ne wasu ƴan siyasa na ƙasar suka yi amfani da damar, inda suka haɗa tsantsar farin jinin da Buhari ke da shi da kuma fusatar da al'umma suka yi da gwamnatin Tinubu domin kai Buhari kann mulki.

Da haka ne Buhari ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015, inda ya zama ɗan adawa na da ya kayar da shugaban da ke kann mulki tun bayan komwara ƙasar kann tafarki na dimokuraɗiyya a 1999.

Buhari ya hau mulki a matsayin wanda ake wa kallon 'mai tsantsar gaskiya', inda ya bayyana dukiyar da ya mallaka, wadda ake ganin ba ta kai ta kawo ba.

Salon maganarsa babu ɓoye-ɓoye, wani abu da a wani lokacin ya zame masa mai amfani, wani lokacin kuma akasin haka.

Sai dai mulkin nasa ya faɗo a daidai lokacin da duniya ta ci karo da koma-bayan tattalin arziƙi, musamman bayan annobar korona.

Har zuwa saukar sa mulki, ana tafka muhawara kann gaba aka ci ko kuma baya a batun yaƙi da rashawa – abin da ya kasance babban alƙawarinsa gabanin hawa mulki.

Ɗaya daga cikin abin da aka fi tunawa da shi a ranar da ya sha rantsuwa shi ne kalaminsa na ''Ni na kowa ne, kuma ba na kowa ba''.

Mutane da dama sun ɗora masa laifin rashin taɓuka abin kirki wajen ceto tattalin arziƙin ƙasa, kuma sun zarge shi da ɗaukan matakai masu tsauri, kamar rufe iyakokin Najeriya da kuma haramta shigo da wasu kayayyaki daga waje.

Sai dai gwamnatin marigayin ta ce ta yi hakan ne da nufin bunƙasa samar da kaya a cikin gida.

Haka nan a ƙoƙarinsa na cika alƙwarin yaƙi da rashawa a farko-farkon mulkinsa ya samar da dokar tara kuɗaɗen gwamnati cikin asusu ɗaya, ya kuma fito da tsarin kwarmata bayanan ayyukan rashawa.

Ya kuma yi ƙoƙarin gyara harkar sojin ƙasar ta hanyar sayo makamai daga waje, lamarin da ya bai wa Najeriya nasara sosai a wurin yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

Jinya

Bayan cimma burinsa na komawa kan mulki, wani babban ƙalubale da Buhari ya ci karo da shi shi ne rashin lafiya da ya addabe shi.

Rashin lafiyar ya sanya Buhari ya kwashe lokaci mai yawa a cikin mulkin nasa wajen neman magani, musamman a wa'adin mulkinsa na farko.

Akwai lokacin da ya kwashe kwana 50 a birnin Landan yana jinya.

Wasu na ganin cewa rashin lafiyar marigayin ta taka rawa sosai wajen gaza cimma wasu daga cikin alƙawurran da ya ɗauka.

Sai dai a tsawon mulkinsa, rashin lafiyar Buhari ta zama sirrin da babu wanda ya sani, sai dai ko ƙila makusantan shi.

Ko a baya-bayan nan, an tambayi ɗaya daga cikin masu magana da yawun tsohon shugaban ƙasar, Garba Shehu kan ko ya san wani abu game da rashin lafiyar marigayin a lokacin da yake kan mulki, sai dai ya ce ba a faɗa masa ba kuma bai nemi sai ya sani ba ganin cewa 'sirri ne na mtum'.