Rayuwar Muhammadu Buhari cikin hotuna

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 6
Rayuwar Muhammadu Buhari ta jiɓanci sauye-sauye a harkokin mulkin Najeriya tsawon shekara 50 da suka gabata.
Tsohon shugaban ƙasar wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekara 82 da haihuwa, ya fara zama shugaba ne bayan wani juyin mulki, sannan wata gwamnatin soja ta ɗaure shi, sai kuma ya farfaɗo tare da sauya siffa bayan shekaru da dama.
An sha ganinsa sanye da baƙin gilashi sanye da hularsa zanna kuma yana yawan murmushi. Ya ƙarar da mafi yawan rayuwarsa wajen hidimar al'umma.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A wannan hoton na sama, a ɗauke shi ne a 1977 tare da Sarkin Sweden Carl XVI Gustaf da kuma Sheikh Ahmed Zaki Yamani na Saudiyya.
Buhari ya fara ayyukan soja kai-tsaye bayan kammala makaranta.
Zuwa lokacin da aka ɗauki wannan hoton, har ya zama kwamandan yanki.
'Yan shekaru bayan haka, sai sojoji suka hamɓarar da gwamnatin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Shehu Shagari a 1983.

Asalin hoton, Sygma via Getty Images
Duk da cewa Buhari ya karɓi muƙamin shugabancin, ya musanta cewa shi ne ya jagoranci juyin mulkin yana cewa manyan kwamandoji ne kawai suka ɗora shi. Amma wasu na cewa tabbas ya taka rawa a juyin mulkin.
Bayan mulki ba sani ba sabo na shekara biyu, an hamɓarar da gwamnatin tasa. Sabuwar gwamnati ta yi masa ɗaurin talala tsawon shekara uku.
A 2003, Buhari ya yanke shawarar sake neman mulki, amma wannan karon a tsarin dimokuradiyya, inda ya yi takara a jam'iyyar adawa ta All Nigerian Peoples Party (ANPP).

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A nan, shi ne a ɓangaren dama tare da abokin takararsa Chuba Okadigbo a hagu, da kuma shugaban ANPP Don Etiebet.
Olusegun Obasanjo ne ya doke Buhari a zaɓen na 2003, kafin ya sake yin takarar a 2007 da 2011 ba tare da nasara ba.
Duk da wannan rashin nasara, ya samu magoya baya kuma ya kama zuciyar matasa da alƙawarinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma matsalar tsaro.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Buhari ya fi shahara da samun magoya baya a arewacin Najeriya, inda ya fito.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
A nan, wani allo ne aka girke a birnin Kaduna lokacin zaɓen 2015, wanda ke cewa "Baba Buhari" kawai za su zaɓa.
Daga baya aka zaɓe shi bayan doke shugaba mai-ci Goodluck Jonathan, kuma ya zama mutum na farko da ya yi hakan a ƙasar.
An ɗauki daidai lokacin da Goodluck ya kira Buhari ta waya domin taya shi murna.

Asalin hoton, Red Media Africa
Bayan shiga ofis, Buhari ya fuskanci matsaloli, inda tattalin arzikin Najeriya ya faɗa masassara a karon farko cikin shekara 10, matsalar tsaro ma ta ƙaru.
Lokacin da matarsa Aisha - hotonta a ƙasa - ta soki gwamnatin tasa, shugaban ya jawo cecekuce bayan ya siffanta ta a matsayin mai yi masa hidima.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Duk da ƙalubalen da ya fuskanta a wa'adin farko, an sake zaɓar sa a 2019.
Ya ziyarci ƙasashe da yawa na duniya a matsayin shugaban ƙasar da ta fi girman tattalin arziki a Afirka.

Asalin hoton, John Stillwell/Getty Images
Sarauniyar Ingila kenan Elizabeth take gaisawa da Buhari yayin taron ƙasashen rainon Ingila a 2015.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Kafin haka a 2015, ya samu tarɓa daga shugaban Amurka na lokacin Barack Obama a fadar White House.

Asalin hoton, Getty Images
A 2018 kuma, Buhari ya zama shugaba na farko daga yankin hamadar Saharar Afirka da ya gana da shugaban Amurka na lokacin Donald Trump.

Asalin hoton, Hindustan Times via Getty Images
Bayan rasuwarsa a wani asibiti a Landan, wasu kan soki Buhari da cewa ya murƙushe 'yan'adawa da karya alƙawarin da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
A wajen wasu kuma, gwarzo ne wanda ya yi ƙoƙarin sauya al'amuran da suka lalace matuƙa.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
An yi jana'izarsa ranar Talata a garin Daura da ke jihar Katsina, wanda nan ne mahaifarsa.
Kamar yadda ake gani a hoton sama, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ke zaune a kujera a gaban gawar marigayin, yayin da sauran shugabanni - ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima - ke yin bankwana da ita.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
An binne gawar tasa ne a cikin gidansa na Daura. A wannan hoton, wasu daga cikin 'ya'yansa da makusanta ne ke gyarawa da saka gawar a cikin ƙabari ranar Talata.

Asalin hoton, Reuters











