Wane giɓi rasuwar Muhammadu Buhari za ta samar a siyasar Najeriya?

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buhari ya tsaya takarar shugabancin Najeriya sau uku kafin ya lashe zaben karo na hudu
    • Marubuci, Azeezat Olaoluwa, BBC News
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist Reporter
  • Lokacin karatu: Minti 5

Rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari babu shakka ta samar da giɓi a siyasar Najeriya musamman a arewacin ƙasar.

Masu fashin baƙi na ganin rasuwar tsohon shugaban ƙasar ka iya haifar da wani ƙokari daga ƴan siyasar arewacin ƙasar na maye gurbinsa musamman a daidai lokacin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara ƙaratowa.

A yankin arewacin ƙasar an ayi wa Muhammadu Buhari ba kawai a matsayin ɗan siyasa ba har ma da kasancewarsa mahaɗa tsakanin talakawa da masu faɗa a ji.

Mutum ne da yake da mabiya na ga-ni-kashe ni a yankunan karkara da biranen yankin arewacin Najeriya.

Ƙimar da yake da ita a zukatan talakawa ta sa shi ne mutum ɗaya tilo da yake iya samun miliyoyin ƙuri'u a takararsa in ko a 2011ya samu ƙuri'a miliyan 12 musamman daga arewacin ƙasar.

Buhari ne ɗan siyasar da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2015 a jam'iyyar APC ta haɗaka kuma ya samu nasarar lashe zaɓen da yawan ƙuri'u miliyan 15.4, bayan bai wa shugaba mai ci, Goodluck Jonathan tazarar ƙuri'u fiye da miliyan 2.5.

Kuma wannan nasara ta sake fito da ƙimar da Buhari yake da ita a matsayin ɗan siyasa mafi ƙarfi a Najeriya.

Wasu daga cikin kalaman da ya yi a lokacin rantsuwarsa ta kama aiki da suka kaɗa hantar masu faɗa a ji a ƙasar sun haɗa da "Ni ba na kowa ba ne, kuma ni na kowa ne."

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buhari ne mutum na farko da ya kayar da shugaban ƙasa mai ci a zaɓe.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Kalamansa sun girgiza masu faɗa a ji abin da ya janyo da dama daga cikinsu suka fice suka bar ƙasar," in ji Farfesa Khalid Aliyu, Sakatare Janar na Jama'atu Nasril Islam, JNI.

Gimba Kakanda, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan bincike da alƙaluma a ofishin mataimakin shugaban ƙasar, ya ce Buhari ya bai wa jama'a da dama mamaki waɗanda a baya suka ƙi shi saboda kallon da suka yi masa na wanda zai nuna kaɓilanci kuma ba zai yi wani ƙoƙari na haɗa kan al'ummar ƙasar ba.

"Ya nuna cewa a shirye yake ya yi aiki da dukkannin sassan ƙasar. Kuma kalamansa na ranar rantsuwarsa a 2025 sun tabbatar da hakan," in ji Gimba.

Sai dai kuma ba kowa ba ne ya gamsu da salon kamun ludayin nasa.

Ɗan jarida Nicholas Ibekwe ya yi imanin cewa kalaman tsohon shugaban na ranar rantsuwa a takarda suke kawai ba a aikace ba

"Bai gwada abin da ya faɗa ba a lokacin yana mulki. Ya bai wa manyan muƙamai ga ƴan arewaci. Kenan me hakan yake nufi?" in ji Ibekwe.

"Kawai dai Buhari ya kasance ɗan siyasa mai kwarjini amma babu wani lokaci da ya taɓa zagayawa a arewacin ƙasar domin koya jajanta wa al'ummar yankin ko wani abu, sai dai kawai a lokutan da yake da buƙata."

Ɗan siyasa mai amana

Duk da cewa Buhari ya fuskanci suka a lokacin wa'adinsa na farko dangane da yadda ya riƙe sha'anin tsaro da tattalin arziƙi da rashawa da cin hanci, ya sake samun damar wa'adi na biyu a 2019. Kuma mafi yawancin ƙuri'un nasa sun samu ne daga arewacin ƙasar.

A zaɓen 2023, Muhammadu Buhari ya sake kafa tarihi a lokacin da yake shirin barin ofis bisa ƙoƙarinsa na ƙin yarda ya goyi bayan wani ɗan takara a jam'iyyar. Wannan ne karon farko da shugaba mai ci ya ƙi fitowa ya zaɓi mutumin da yake so ya gaje shi a zaɓen cikin gida na jam'iyyarsa.

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buhari ya yi takara har karo uku ba tare da samun nasara ba, inda ya yi nasara a karo na huɗu a 2015.

Maimakon hakan sai Buhari ya goyi bayan mutumin da jam'iyyar tasa ta fitar a matsayin ɗan takararta, ta yadda ya samar da tsaftataccen tsarin fitar da ɗan takara ba tare da son kai ba.

"Abu ne mai kyau yadda bai goyi bayan kowa ba sai dai kawai ya zama jagora. Bai shiga ya zaɓar wa jama'a ɗan takara ba," in ji Farfesa Aliyu na JNI.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa ƙin amincewa ya fitar da ɗan takarar da yake so ya daƙile damar da yake da ita na ƙara kafa daula a siyasance.

Buhari dai bai taɓa ɓoye tunanin da yake da shi dangane da makomarsa bayan sauka daga shugabancin ƙasar ba, inda ya ce zai koma mahaifarsa ya fuskanci noma da kiwo.

Haka kuma ya yi inda ya kama hanyar zuwa Daura jim kaɗan bayan miƙa mulki ga Shugaba Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

"Rasuwarsa za ta haifar da giɓi babba. Mun ga yadda bayan komarwasa Daura yadda jama'a suka yin tururuwa zuwa Daura domin kai masa ziyara da kuma neman shawarwari, in ji Farfesa Aliyu.

"Akwai yiwuwar goyon bayan da yake dashi a arewacin ƙasar a ƙarshe-ƙarshen mulkinsa amma kuma magoyansa da dama sun ragu a ƙarshen zangon mulkin nasa duk da cewa da dama magoya bayan nasa sun ci gaba da yin imani da shi har zuwa ƙarshen mulkin," in ji Gimba Kakanda.

"Irin wannan ƙauna ga wani ɗan siyasa ba abu ne gama-gari ba kuma na nuna irin ƙaunar da jama'a suke yi masa da kuma alaƙarsa da su."

To sai da ɗan jarida Ibekwe na da ra'ayin cewa rasuwar Buhari ba za ta bar wani giɓi ba a siyasance a arewacin ƙasar.

"Mabiyansa a koyaushe shi kawai suke so kuma suke zaɓa," in ji shi.

" A duk lokacin da bai tsaya takara ba a zaɓe to za ka ga magoya bayan nasa sun zaɓi mutanen da suke so daban-daban."

Babu 'Sak' a zaɓen 2027

Yanzu haka an binne fitaccen ɗan siyasa mai kwarjini da talakawa ke ƙauna, Muhammadu Buhari, masana da ƴan Najeriya da dama na tambayar ko ta yaya hakan zai shafi nasarar jam'iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar na 2027.

Ɗan jarida Mannir Ɗan Ali ya ce rasuwar Buhari ta haifar da wani yanayin siyasa a arewacin Najeriya na kowa zai tsaya da ƙafarsa.

"Zamanin yin 'sak' ya wuce, duk wani ɗan siyasa da ke son tsayawa takara a nan gaba to sai ya tsaya da ƙafarsa sannan kuma sai ya nuna abin da zai iya yi wa jama'arsa kafin su zaɓe shi." In ji Mannir.

Shi ma Gimba Kakanda ya yi imanin cewa rasuwar Buhari za ta haifar da sabon tsarin siyasa a arewacin Najeriya.

"Akwai yiwuwar za mu ga sabbin fitattun ƴan siyasa maimakon mutum ɗaya mai ƙarfin faɗa a ji a yankin inda kuma sassan yankin da ƙabila ka iya taka muhimmiyar rawa," in ji Kakanda.

Akwai damuwa dangane yiwuwar Shugaba Tinubu na tabbatar da farin jininsa a arewacin ƙasar ba tare da goyon bayan Buhari ba.

Hakan na nufin duk ƴan siyasa da suka dogara da farin jinin Buhari domin a zaɓe su yanzu za su fuskancin ƙalubalen dogaro da kansu.

Farfesa Aliyu ya ce yanzu za a samu ƴan siyasar da za su fara nuna wa talakawa cewa za su share musu hawaye.

"Duk wanda ke son zama jagoran talakawa, to dole ne sai ya san cewa farin jinin Buhari bai samu saboda arziƙin da yake da shi ba. Kuɗi ba ya samar da farin jini da ɗaukaka. Halayya da rashin son kai da bautata wa al'umma ne ke samar da farin jini da kwarjini," in ji Farfesa.