Manyan ayyukan da za a riƙa tuna Muhammadu Buhari da su

Asalin hoton, Nigeria Presidency
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Lokacin karatu: Minti 8
A ranar Lahadi ne tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan bayan fama da jinya, lamarin da ya jefa Najeriya da ƴan ƙasar cikin jimami da alhini.
Marigayin ya yi mulkin ƙasar ne sau uku, inda ya fara da mulkin soja a shekarar 1983 bayan sojoji sun yi juyin mulki.
A zamanin mulkinsa na soja ne ya ƙaddamar da yaƙi da rashin ɗa'a, lamarin da ya sa ake masa kallon shugaban da ya yi ƙoƙarin tabbatar da ɗa'a da gyara halayyar ƴanƙasar.
Mulkinsa na soja bai daɗe ba, domin shi ma an masa juyin mulki bayan kusan shekara biyu yana karagar mulkin ƙasar.
Daga baya ya koma siyasa, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau uku a shekarun 2003 da 2007 da 2011, amma bai samu nasara ba. Sai a zaɓen 2015 ne ya samu nasarar lashe zaɓen shugabancin ƙasar, inda ya yi mulkin wa'adi biyu a jere tsakanin 2015 zuwa 2023.
A daidai lokacin da ake jimamin rasuwar mamacin, BBC ta duba wasu muhimman ayyuka da matakai da ya ɗauka a zamanin da yake mulkin ƙasar.
Yaƙi da Boko Haram

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Daga cikin muhimman abubuwan da marigayin ya yi kamfe da su a yaƙin zaɓe akwai yaƙi da cin hanci da rashawa da fatattakar mayaƙan Boko Haram waɗanda suka daɗe suna addabar arewacin Najeriya.
Buhari ya hau mulki ne a daidai lokacin da matsalar tsaro, musamman ta Boko Haram ta ƙaru sosai, lamarin da yake cikin abubuwan da suka dusashe tauraron tsohon shugaban ƙasar Jonathan, har mutane suka yi adawa da mulkinsa, suka fara buƙatar 'canji'.
A zamanin mulkinsa, jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarar ƙwato garuruwa da dama da Boko Haram suka ƙwace, inda mutan da dama masu gudun hijira suka koma muhallansu.
Haka kuma an taƙaita ayyukan ƙungiyar zuwa wasu yankuna maimakon gawurta da suka yi, tare da faɗaɗa kai hare-hare a jihohin arewa maso gabas, da ma wasu jihohin arewa ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Duk da cewa ba a ƙarar da mayaƙan na Boko Haram ba, za a iya cewa a zamanin mulkinsa an rage ayyukan su sosai.
Sufurin jirgin ƙasa

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin manyan ayyukan da marigayin ya yi a zamanin mulkinsa, akwai dawo da sufurin jirgin ƙasa, wanda a zamanin gwamnatinsa aka gyara tare da zamanantar da ayyukansa da faɗaɗa sufurinsa zuwa wasu biranen ƙasar.
Daga cikin ayyukan titin dogon da ya yi da suka fi jan hankali akwai na Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2016, wanda har sai da ya kai ana shan wahala wajen samun tikitin shiga saboda yawan fasinja.
Akwai kuma titin jirgin ƙasa na Itakpe zuwa Wari, wanda shi me ya sauƙaƙa tafiya zuwa yankin Neja Delta na ƙasar.
Akwai kuma babban titin jirgin ƙasa na Legas zuwa Ibadan.
Haka kuma a zamanin mulkinsa ne aka fara aikin titin jirgin ƙasa daga birnin Kano a Najeriya zuwa Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, aikin da ake cigaba da yi har zuwa yanzu.
An kuma ƙaddamar da sabunta hanyar dogon Fatakwal zuwa Maiduguri, wanda zai ratsa ta cikin jihohin kudu maso gabashin Najeriya a shekarar 2021, duk da ba a samu nasarar kammala aikin ba.
Noma

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wa'adin mulkinsa na farko ne marigayin ya ƙaddamar da shirin ba manoma lamunin noma mai suna Anchor Borrowers' Programme (ABP), wanda aka ƙaddamar a shekarar 2015.
A ƙarƙashin shirin, an raba kuɗi naira biliyan 800 ga manoman ƙasar domin su noma abincin da ƴanƙasar ke buƙata domin ƙasar ta ciyar da kanta ba tare da dogaro da shigar da abinci daga wasu ƙasashen ba.
Bayan ƙaddamar da shirin tallafawa manoman ne gwamnati ta hana shigar da abinci daga ƙasashen waje zuwa ƙasarta, musamman nau'ukan abincin da za a iya nomawa a ƙasar, lamarin da ya daɗaɗa wa manoman ƙasar matuƙa saboda irin ribar noma da suka samu a lokacin.
Haka kuma a watan Maris na shekarar 2017 marigayin ya amince da shiga yarjejeniyar samar da takin zamani na Presidential Fertiliser Initiative (PFI) wanda aka tsara a watan Disamba na shekarar 2016, lokacin Sarkin Maroko Mai alfarma Mohammed VI ya kai masa ziyara a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, inda suka gana domin haɗaka domin ciyar da ƙasashensu gaba.
A yarjejeniyar aka tsara samar da takin zamani ne mai rahusa da magoman Najeriya, domin samar da buhu miliyan 60 na kilogram 50 na takin zamanin tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.
N-Power: Rabon tallafi

Asalin hoton, N-Power 2020 registration
Rabon tallafi daban-daban na cikin muhimman ayyukan da Buhari ya aiwatar a zamanin mulkinsa a Najeriya, wanda yawancin ƙasar, musamman matasa da dama suka ci moriya kai-tsaye.
A shekarar 2016 ce ya ƙaddamar shirin raba tallafi ga ƙanana da matsakaitan masu sana'a a ƙasar, a ƙarƙashin wani shiri na musamman mai suna National Social Investment Programme (NSIP), wanda akwai ɓangarorin tallafi da dama a ƙarƙashinsa.
A cikin shirin ne aka ɗauki ma'aikatan N-power, inda aka ɗauki matasa masu shekaru tsakanin 28 zuwa 35 aiki aka tura su wuraren da ake buƙatar aikinsu, kamar ɓangaren noma da koyarwa, inda aka riƙa biyan su alawus na naira 30,000 duk wata na twason shekara biyu, sannan aka ɗauki wasu.
Akwai kuma rabon kuɗin tallafi na kai-tsaye ga masu ƙaramin ƙarfi da ake kira Conditional Cash Transfer wato CCT, wanda a cikinsa ne aka riƙa rabon tallafi ga talakawan ƙasar.
A ƙarƙashin ne aka raba jari ga ƙananan masu sana'a da kasuwanci, inda aka riƙa ba su tallafin tsakanin naira 10,000 zuwa 100,000 domin su ƙara jari tare da inganta harkokin kasuwancin da suke yi.
Akwai kuma tallafin ciyar da ɗaliban makaranta, inda aka ɗauki ma'aikata musamman mata a garuruwa suna aikin dafa abincin da ake ciyar da ɗaliban makarantun gwamnati, lamarin da ya samar da ayyukan yi ga masu aikin dafa abincin, sannan ya rage wa iyaye ɗawainiyar ciyar da yaran kafin su tafi makaranta.
Akwai kuma tallafin Covid-19 da gwamnatin ta raba ta hannun bankin Nirsal, wanda ƴan Najeriya da dama suka samu domin rage raɗaɗin da annobar da jefa mutane a ciki.
Sannan gwamnatin ta ba jihohin ƙasar da Abuja kuɗaɗe domin gudanar da ayyukan rage raɗaɗi a jihohinsu.
Tituna

Gwamnatinsa ta assasa asusun muhimman ayyuka na Presidential Infrastructure Development Fund (PIDF) a shekarar 2018 domin nemowa tare da kammala muhimman ayyuka da ma fara sababbi.
A watan Janairun 2019 kuma sai ya sanya hannu a doka ta musamman ta Order 7, wadda aka tsara domin gudanar da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni. A ƙarƙashin wannan shirin ne aka samu kuɗaɗen gudanar da wasu muhimman ayyuka a ƙarƙashin shirin SUKUK Bond.
Manyan ayyukan da ya yi a ɓangaren tituna sun haɗa da kammala aikin titin Lagos-Ibadan da gadar Neja ta biyu da sabuntawa tare da faɗaɗa titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano.
A cikin wani jawabi da ministan ayyuka a zamanin mulkin marigayin, Babatunde Fashola ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da aikin faɗaɗa titin Kano-Maiduguri da kuma gyara titin Vandeikya-Obudu-Obudu.
Ya ƙara da cewa akwai gyara titin Sokoto-TambuwaI-Jega-Kontagora-Makera mai nisan kilomita 155.
Haka kuma akawai tituna da dama da gwamnatinsa ta yi a ƙarƙashin shirin asusun haɗaka na SUKUK.
Asusun bai ɗaya
Da yake yaƙi da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Buhari ya yi alƙawari a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, sai ya kasance ƴan ƙasar sun zuba idon domin matakan da zai ɗauka.
A zamaninsa aka ɗabbaƙa amfani da asusun bai ɗaya domin gudanar da harkokin gwamnati, wato TSA.
Asali dai an fara maganar TSA a shekarar 2012, amma ba a fara amfani da tsarin ba a hukumance.
A watan Satumban shekarar 2015 ne gwamnatin Buharin ta bayar da umarni ga dukkan ma'aikatun gwamnatin tarayya su fara amfani da asusun gwamnatin ƙwaya tal na bai ɗaya.
Daga lokacin zuwa watan Fabrailun 2017, babban bankin ƙasar wato CBN ya tara sama da naira tiriliyan 5.24, sannan ya rufe asusun ma'aikatun ƙasar sama da 20,000.
Haka kuma an ɗabbaƙ amfani da tsarin biyan albashi na Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS) da kuma lambar Bank Verification Number (BVN) domin rage rashawa a ƙasat.
Gyara hali
A watan Satumban shekakar 2016 ne marigayin ya ƙaddamar da wani shirin na musamman da aka yi wa laƙabi "change begins with me" wato sauyi na fara ne daga kaina wanda aka tsar domin gyara tunanin ƴan ƙasar da sauya ɗabi'unsu.
Dama tun asali an san shi da kasancewa mutum mai yaƙi da rashin ɗa'a tun a zamanin mulkinsa na farko a mulkin soja, inda a wancan lokacin ya assasa shirin raƙi da rashin ɗa'a.
Da yake ƙaddamar da shirin a lokacin, Muhammadu Buhari ya ce ya assasa shirin ne abubuwa ba sa tafiya daidai a ƙasar, inda ya ce yana ganin idan ƴanƙasar suka fara gyarawa, komai zai gyaru.
Ministan yaɗa labarai na lokacin, Lai Mohammed ya ce shirin zai ilmantar da mutane a kan mahimmancin kyautata ɗabi'u, inda ya ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen farfaɗo da ƙima da riƙon amana da kuma kwatanta kyawawan hallaya, a duk inda mutum ya tsinci kansa.
Shirin fallasa ɓarayin gwamnati
Wani shiri na gwamnatin Buhari da ya ɗauki hankali shi ne shirin fallasa ɓarayin gwamnati mai suna 'whistelblower'.
A ƙarƙashi shirin, duk wanda ya fallasa sata, za a ba shi kashi biyar da kuɗin da aka ƙwato.
Ministan kuɗi na lokacin, Femi Adeosun ta ce sun samu bayanai sama da dama kuma sun samu nasarar ƙwato wasu maƙudan kuɗaɗe.
Daga cikin muhimman ƙwato kadarori da aka yi a ƙarƙashin wannan shirin, akwai ƙwato dala miliyan 9.8 daga wani tsohon babban ma'aikacin NNPC, da kuma dala miliyan 40 da ake zargin na ma'aikatar tattara bayanan sirri wato NIA a Ikoyi da ke Legas da sauran su.
A watan Nuwamban shekarar 2017 Adeosun ta ce sun biya masu fallasar naira miliyan 421.33 a matsayin ladar aikinsu 421.33.
Dokar man fetur
A ɓangaren man fetur da iskar gas, wani babban mataki da Buhari ya ɗauka da ya kawo sauyi a ɓangaren shi ne sanya hannu da ɗabbaka dokar man fetur ta Petroleum Industry Act (PIA).
A lokacin masu ruwa da tsaki a ɓanaren man fetur sun yaba masa bisa ɗaukar wannan matakin.
A lokacin ne kamfanin samar da man fetur na ƙasar ya koma kamfani mai zaman kansa wato NNPCL, wanda aka yi a shekarar 2022.
Sannan an kafa Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA da kuma hukumar kul da harkokin man fetur wato NUPRC duk a ƙarƙashin dokar.
Yaƙi da rashin ɗa'a
A tsawon lokacin da Buhari ya mulki Najeriya a matsayin soja, abubuwa da dama sun sauya.
Abin da aka fi tunawa kan mulkin nasa na farko su ne tsarinsa na yaƙi da rashin ɗa'a, sai kuma yaƙi da rashawa.
Kimanin ƴan siyasa 500 ne gwamnati ta ɗaure a wani mataki na yaƙi da rashawa da ɓarnata dunkiyar al'umma.
Wasu sun kalli waɗannan tsare-tsare na gwamnatin Buhari a matsayin kama-karya, wasu kuma na kallon hakan a matsayin abin a yaba wajen yaƙi da rashawa, abin da ya yi wa ƙasar katutu kuma yake hana ta ci gaba.
Waɗannan matakai na daga cikin abubuwan da suka sa Buhari ya samu laƙabin mai gaskiya.
A wani ɓangare na shirin yaƙi da rashin ɗa'a, an tursasa wa mutane bin layi a wurin hawa mota, an kuma tursasa wa waɗanda ake zargi da ɓoye kaya fitowa da su su sayar.
An kuma riƙa hukunta ma'aikatan gwamnati da ke zuwa ofis a latti, cikin irin wannan hukunci har da tsallen kwaɗo.
Sauye-sauye ne da ba a saba gani ba, sai dai wasu sun ce lamarin ya zama tamkar danniya, musamman ƙoƙarin da gwamnatin ta yi na samar da dokar taƙaita ƴancin ƴan jarida.











