Ayyuka huɗu da rundunar tsaro ta mutum 2000 za ta yi a Kano

Kano

Asalin hoton, SSA II On Social Media Kano State.

Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun assasa rundunar tsaron askarawan jihar ne na sa-kai domin taimakawa jami'an tsaron tarayya na sojoji da ƴansanda domin tabbatar da tsaron al'umma.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da sababbin dakarun askarawa 2,000 da gwamnatin jihar ta horas, tare da ba su kayan aiki da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Gwamnatin jihar ta ce za a rarraba rundunar a ƙananan hukumomi daban-daban domin tabbatar da tsaro a kasuwanni da makarantun da unguwanni da sauran muhimman wurare.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta jaddada cewa ƙaddamar da rundunar na daga cikin ƙoƙarin da take yi na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma bai wa al'umma kwarin gwiwar rayuwa cikin aminci.

Ta yi kira ga mazauna jihar da su ba da haɗin kai tare da tallafa wa rundunar domin ta samu nasara a aikinta na kare lafiyar jama'a.

Daga cikin jami'an tsaron akwai maza 1,870 da mat 130, sannan gwamnan ya ƙaddamar da motoci ƙirar hilux guda 88 da babura guda 440.

Wane aiki askarawan za su yi?

Kano

Asalin hoton, SSA II On Social Media Kano State.

A lokacin bikin ƙaddamar da askarawan, gwamna Yusuf ya umarce su da su kasance masu gaskiya da amana, sannan ya faɗa musu cewa an ɗauke su aiki ne domin kare al'ummarsu.

Ya ce tabbatar da tsaron jihar Kano na cikin manyan muradun gwamnatinsa, sannan ya ƙara da zaman lafiya ginshiƙi ne wajen inganta tattalin arziki da ilimi da walwalar al'umma.

A nasa ɓangaren, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya yaba da ƙoƙarin na gwamnatin Kano, inda ya yi alƙawarin bayar da haɗin kai da goyon baya musamman wajen kare bakin iyakoki.

Radda ya ce samun haɗaka tsakanin jihohi na da matuƙar alfanu wajen tabbatar da tsaron jihohin arewa maso yammacin ƙasar.

Ayyukan da za su yi sun haɗa da:

  • Yaƙi da masu garkuwa da mutane
  • Yaƙi da shaye-shaye
  • Yaƙi da ƙwace
  • Kariya a birane da ƙauyuka

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwao da mataimakin gwamnonin Zamfara da Sokoto da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi da sauran sarakuna da jami'an gwamnati a ciki da wajen jihar.

Me hakan yake nufi ga sha'anin tsaro a Najeriya?

Kano

Asalin hoton, SSA II On Social Media Kano State.

A kwanakin baya da aka fara ƙaddamar da askarawan nan a jihohin arewacin Najeriya, BBC ta zanta da masana tsaro domi sanin yadda ayyukan askarawan zai kasance.

Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja Najeriya ya ce wannan yana nuni da irin gazawar tsarin tsaro na gwamnatin tarayyar Najeriyar, inda ta bar al'amarin sakaka a hannun jihohi.

"Kafa rundunar tsaro ba mafita ba ce, ya kamata majalisar ƙasa ta sauya kundin tsarin mulki domin samar da ƴansandan jihohi cikin tsari ta hanyar ba su cikakken horo da sauransu", in ji Malam Kabiru.

To sai dai Barrister Bualama Bukarti wanda masanin tsaro ne kuma lauya mai zaman kansa a Birtaniya ya ce "duk da cewa bai zama lallai wannan tsari ya zama shi ne mafita ba, amma ba za ka soki jihohin ba saboda duk wanda ruwa ya ci, to ko takobi ka miƙa masa zai kama ne."

Mene ne illar tsarin ko alfanunsa?

Malam Kabiru Adamu ya ce abin da jihohin Zamfara da Katsina suka kusan dukkan jihohin Najeriya na da irin tsarin ko da kuwa ba a hukumance ba.

Masanan guda biyu sun ƙara da cewa idan dai dai har gwamnatin tarayya ba za ta nemi majalisar dokoki ta yi doka kan irin wannan tsari, to shirin na da ƙalubale babba.

"Tunda dai da alama gwamnati ta gaza, to dole ne a yi doka domin tsaftace tsarin yadda ba za a bar abin kara zube ba." In ji Barrister Bulama Bukarti.

Masanan sun kuma lissafa wasu matsaloli na tsarin ɗaukar matasa aikin sa-kai kamar haka:

  • Za a iya samun yawaitar makamai a hannun ƴanƙasa wanda hakan zai haifar da ƙarin matsalar tsaro a nan gaba.
  • Ƙarancin horo ga mai riƙe da makamai da ka iya haifar da wuce gona da iri.
  • Rashin cikakkun bayanai dangane da mutanen da aka ɗiba, inda wasu ma ba su da halayya mai kyau.
  • Ɗaukar hukunci a hannunsu musamman ma cin zarafin wanda ba su ji ba ba su gani

Mece ce mafita?

Malam Kabiru Adamu da Barrister Bulama Bukarti sun amince cewa kafa rundunar tsaro ba mafita ba ce ga jihohin da ke fama da matsalar.

To sai dai sun amince cewa a rashin uwa a kan yi uwar ɗaki, inda suka ce ya kamata majalisar ƙasa ta sauya kundin tsarin mulki domin samar da ƴansandan jihohi.

A cewarsu ƴansandan jihohi za su fi zama cikin tsari da samun cikakken horo kasancewar doka ce ta kafa su.

To amma masanan sun ce idan ba a iya samun dokokin ba to sai a bi wasu shawarwari da suka bayar kamar haka:

  • Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin yadda za a riƙa kafa irin waɗannan ƙungiyoyi a jihohi na bai-daya.
  • Tabbatar da cewa waɗannan matasa za su yi aiki ne kaɗai yayinda suke cikin rakiyar jami'an tsaro domin gudun arangama.
  • Lallai a tanadi rumbun tattara bayanan matasan da irin horon da aka ba su da kuma makaman da aka ba su, kuma za a cimma hakan ne a ƙarƙashin ma'aikatar tsaro ko kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.