Ƙalubale huɗu da ke gaban Kabiru Turaki, sabon shugaban PDP

..

Asalin hoton, PDP

Lokacin karatu: Minti 4

A ƙarshen makon nan ne babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, PDP ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon shugabanta, duk da irin jimirɗar da aka yi fama da ita gabanin zaɓen.

An samu umarnin kotu har guda uku da suka nemi jam'iyyar ka da ta gudanar da taron nata na ranar 15 ga watan Nuwamba a jihar Oyo.

Rikicin da jam'iyyar ke fama da shi ya i ci ya i cinyewa, ta yadda abubuwa daban-daban ke ɓullowa game da jam'iyyar a kullu-yaumin.

A ƙarshen mako, lokacin taron da ta yi a jihar Oyo, jam'iyyar ta sanar da sallamar wasu daga jikin jigajiganta, kamar Ministan Abuja Nyesom Wike, da sakatarenta Samuel Anyanwu da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose da sauran su.

Sai dai hatta a ranar Litinin, Anyanwu, wanda aka sanar da korar sa daga jam'iyya ya sanar da kiran wani taron gaggawa na shugabannin jam'iyyar da kuma kwamitin amintattunta, wanda zai gudana a ranar Talata.

Babu tabbas kan yadda taron zai gudana, ganin cewa jam'iyyar ta zaɓi sabon shugaba, Tanimu Turaki da sakatarenta na ƙasa Taofeek Arapaja.

Wannan ya sa masu fashin baƙi ke yi wa sabon shugaban jam'iyyar ta hamayya kallon wanda zai yi fama da ƙalubale wajen gudanarwar jam'iyyar.

Ƙalubalen da ke gaban Turaki

Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS kuma masanin kimiyyar siyasa a Najeriya ya ce sabon shugaban jam'iyyar ta PDP babu shakka zai fuskanci ƙalubale.

Masanin kimiyyar siyasar ya lissafa wasu ƙalubale guda huɗu da ya ce su ne suka kamata sabon shugaban na PDP ya tunkara.

  • Daƙile rikice-rikice: Malam Kabiru ya ce babban abin da ya kamata sabon shugaban ya sa a gaba shi ne ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikice-rikicen da jam'iyyar take fama da su waɗanda suka faru gabanin babban taron da lokacin taron.
  • Sasantawa: Dole ne sabon shugaban ya tabbatar ya bi waɗanda aka ɓata wa, ko kuma suke ganin an ɓata musu domin ya ba su haƙuri a koma a yi tafiya bai ɗaya. Waɗanda suka tafi kotu da ma waɗanda suka fice daga jam'iyyar duka sai an bi su an ba su haƙuri sannan a koma da su cikin jam'iyyar.
  • Gina sabuwar jam'iyya: Bayan samun nasarar kawar da rikice-rikice da sasantawa da waɗanda aka ɓata mawa, to abu na gaba shi ne sake gina jam'iyyar musamman wajen fuskantar hamayya a Najeriya.
  • Dawo da martabar jam'iyya a idanun ƴan ƙasa: Dole ne sabon shugaban ya yi ƙoƙarin nuna wa ƴan Najeriya cewa jam'iyyar za ta yi sabuwar tafiya kuma ana buƙatar ƴan ƙasa su yi imani da ita domin ta yi tasirin da ake buƙata a zaɓukan da ke tafe. Hakan ba zai samu ba sai idan sabon shugaban ya iya cimma ƙalubalen guda uku na sama.

Umarnin kotuna masu karo da juna

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

1 - PDP ta fara fuskantar umarnin kotu ne a ranar 31 ga watan Oktoba, lokacin da babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci a dakatar da shirin gudanar da babban taron na ƙasa.

Mai Shari'a James Omotosho ya bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta iya ci gaba da shirin gudanar da taro na 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa PDP ta gaza wajen bin dokokin mulkin jam'iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 game da shirin gudanar da taron.

Lauyan masu ƙorafi ya faɗa wa kotun cewa PDP ba ta gudanar da zaɓukan shugabancin jam'iyyar ba a jihohi 14, inda ya nemi kotun ta duba ko hakan ya saɓa wa doka.

2 -Sai kuma a ranar Talata 11 ga watan Nuwamba wata babbar kotun a Abuja ta sake bayar da umarnin dakatawa da shirin gudanar da taron sakamakon ƙarar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya shigar.

Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin ne tana cewa har sai ta kammala sauraron ƙorafin na Sule, sannan ta hana hukumar zaɓe zuwa domin saka ido a zaɓen.

3 -A wani umarni mai cin karo da wancan, a ranar 4 ga watan Nuwamba babbar kotun jihar Oyo ta umarci PDP ta ci gaba da shirin taron bayan wani ƙorafi.

Mai Shari'a Ladiran Akintola ya umarci jami'an PDP da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na dakile ko karya jadawalin da aka aka fitar, sannan ya umurci hukumar zabe ta tura jami'anta domin sa ido.

Wane ne Tanimu Turaki?

An haifi Kabiru Tanimu Turaki a ranar 3 ga watan Afrilun 1957 a Birnin Kebbi na jihar Kebbi

Ya karanta fannin shari'a a Jami'ar Jos kuma ya kammala a 1985. An kira shi zuwa majalisar lauyoyi ta Bar (Nigerian Bar) a 1986.

Ya zama Babban Lauyan Najeriya (Senior Advocate of Nigeria - SAN) a shekarar 2002, kuma shi ne shugaban kamfaninsa mai suna K.T Turaki & Co

Ya yi aiki a matsayin ministan ayyuka na musamman a ƙarƙashin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan daga 2013 zuwa 2015. Ya kuma rike muƙamin ministan ƙwadago na riƙo, sannan ya shugabanci kwamitin shugaban Kasa kan tattaunawa da samar da zaman lafiya a Arewa

Kafin ya zama shugaban PDP, ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2018 amma bai yi nasarar samun tikitin ba, sannan ya kasance shugaban ƙungiyar tsoffin ministocin PDP (PDP Former Ministers' Forum).

Yana riƙe da sarautun gargajiya da suka haɗa da Dan Masanin Gwandu da Zarumman Kabbi.