Abin da ya kamata ku sani kan babban taron PDP na ƙasa

Asalin hoton, Social Media
Babbar jam'iyyar hamayyar Najeriya, PDP na gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanni.
Taron mai cike da taƙaddama na gudana ne a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin ƙasar.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana game da taron, inda wasu mambobin jam'iyyar suka buƙaci kotu ta soke taron, yayin da wasu kuma suka garzaya kotu domin samun damar gudanar da taron.
Jam'iyyar PDP na fama da taƙaddama da rikice-rikice tun bayan babban zaɓen 2023, inda ta sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa.
Tun bayan zaɓen jam'iyyar ta sauke shugabanta Iyorchia Ayu, tare da naɗa Iliya Damgum a matsayin shugabanta na riƙo, sai dai wannan bai yayyafa wa rikicin da ya turnuƙe a cikinta ruwa ba, sai ma ya zama kamar an ƙara iza wutar rikicin.
PDP ta riƙa rasa wasu daga cikin gwamnoninta da ƴan majalisar dokoki, bayan da suka riƙa ficewa tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki, saboda abin da suka kira rikicin da jam'iyyar ke fama da shi.
Me ake sa ran cimmawa a taron na yau?
Mataimakin daraktan yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa BBC cewa maƙasudin taron shi ne zaɓen sabbin shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa.
''Kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyarmu ya tanada, duk bayan shekara huɗu za a gudanar da taro domin zaɓen sabbin shugabanni'', in ji shi.
"Saboda haka wannan taro namu biyayya ce ga dokar jam'iyyarmu, da ta tanadi hakan'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ƙara da cewa a taron ne jam'iyyar za ta zaɓi sabbin shugabannin da za su gudanar da al'amuran jam'iyyar har nan da shekara huɗu masu zuwa.
Sai dai wannan batu shi ne ya janyo rikici na baya-bayan nan da ya sake turnuƙe jam'iyyar.
Su wane ne ƴantakarar shugaban jam'iyyar?

Asalin hoton, Kabiru Tanimu Turaki/Facebook
Bayan matakin da ta ɗauka na ware wa arewa maso yammacin ƙasar muƙamin shugaba, jam'iyyar ta sanar da cewa Kabiru Tanimu Turaki shi ne ɗan takara na masalaha, bayan wani taro da ta gudanar a cikin dare, ranar 22 ga watan Oktoba.
A lokacin da ya sanar da matakin, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce Turaki ne zai wakilci yankin a babban zaɓen jam'iyyar da za a gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Sai dai ba kowane ɗan jam'iyyar ne ya amince da wannan mataki ba, lamarin da ya kai ga cewa ɗaya daga cikin ginshiƙan jam'iyyar, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya kai ƙara kotu.
A jajibirin taron ne wata babbar kotun tarayya ta tabbatar wa Lamidon da ƴancinsa na tsayawa takara.
Waɗanda suka nuna sha'awar yin takara
Malam Ibrahim shekarau
Tsohon gwamnan na jihar Kano, na daga cikin mutanen da suka nuna sha'awar tsayawa takarar shugabancin PDP.
Cikin wata hira da BBC a baya-bayan nan Shekarau ya ce sun tattauna da Tanimu Turaki da nufin samun masalaha a tsakaninsu, kodayake bai bayyana abin da tattaunawar tasu ta haifar ba.
Kawo yanzu dai bai bayyana janyewarsa daga takarar ba.
Sule Lamido
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya nuna sha'awarsa ta zama shugaban babbar jam'iyyar hamayyar ta Najeriya.
Sai dai Sule Lamido bai iya sayen fom ba, sakamakon abinda ya kira ''ƙin'' sayar masa da fom din da PDP ta yi.
To sai dai Ibrahim Abdullahi ya ce Sule ya je sayen fom ɗin ne a makare, bayan ƙarewar wa'adin lokacin da ka ɗiba na sayar da shi.
''Ya zo sayen fom bayan an gama sayar da fom, an riga an fitar da jadawali na sayarwa da cikawa da na mayarwa wata uku kafin ranar da ya zo neman fom'', in kakakin na PDP.

Asalin hoton, Mansur Ahmed/Facebook
Masalaha za a yi ko zaɓe?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jami'in na yaɗa labaran jam'iyyar ya ce ai dama jam'iyyar ta jima tana tattaunawa kan batun masalahar ɗan takarar da zai iya zama shugaban jam'iyyar.
''Dama shi sulhu an riga an yi shi, kuma wanda jam'iyya ke son zama shugabanta shi ne Kabiru Taminu Turaki, saboda ya samu amincewar gwamnoni da wasu manyan arewa na PDP'', in ji shi.
Dangane da samun goyon bayan wani tsagi, kuwa Ibrahim Abdullahi ya ce ai dama jam'iyyar ta saba haka, kuma gwamna daya ma na iya kawo dan takara kuma a yi shi.
''Domin Wike ya taba yin haka, ya kawo Chief Uche Secondus, ya kuma kawo Iyorchia Ayu, sannan ya nemi goyon bayan sauran gwamnoni suka kuma amince masa'', in ji shi.
''Shi kuma yanzu Turaki yana samun goyon bayan duka gwamnoni da wasu jiga-jigan jam'iyar arewacin kasar ciki har da shugaban riƙon jam'iyyar na yanzu Iliya Damagum'', in ji mai magana da yawun PDPn.
Ya kuma ƙara da cewa akwai yiwuwar yin masalaha ga sauran kujerun da ake takara bisa amincewar yankunan da aka ware wa muƙaman.
Dambarwar da aka sha kafin taron
A ranar 4 ga watan Nuwamba babbar kotun jihar Oyo ta umarci PDP ta ci gaba da shirin taron bayan wani ƙorafi
Mai Shari'a Ladiran Akintola ya umarci jami'an PDP da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na dakile ko karya jadawalin da aka fitar, sannan ya umurci hukumar zabe ta tura jami'anta domin sa ido.
"Wannan mataki babbar nasara ce ga jam'iyya domin yanzu kwamitin shirya taron NCOC na da damar kammala shirye-shiryen karɓar sama da wakilai 3,000 da ake sa ran halartarsu daga jihohi daban-daban," a cewar PDP cikin wata sanarwa a lokacin
To sai dai a ranar Talata 11 ga watan Nuwamba wata babbar kotun a Abuja ta sake bayar da umarnin dakatar da shirin gudanar da taron sakamakon ƙarar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya shigar.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin ne tana cewa har sai ta kammala sauraron ƙorafin na Sule, sannan ta hana hukumar zaɓe zuwa domin saka ido a zaɓen.
Alƙalin ya ƙara da cewa ya aminta da ƙorafin da Sule ya shigar na cewa PDP ba ta wallafa jadawalin yin taron ba saboda mambobinta su sani kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Shawarar Bukola Saraki
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya shawarci jam'iyyar ta PDP mai adawa ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a jihar Oyo saboda umarnin kotunan.
Saraki ya bayar da shawarar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X ranar Laraba bayan wata ganawa da kwamatin sasanta 'ya'yan jam'iyyar ƙarƙashin jagoracin Hassan Adamu.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala game da halascin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.
Sai dai Ibrahim Abdullahi ya ce jam'iyyar za ta yi aiki ne da hukuncin kotun farko da ya bai wa PDP damar gudanar da taron nata.
Ya kuma zargi jam'iyyar APC mai mulki da kawo wa jam'iyyar tasgaro a babban taron nata.
''Gwamnati mai ci ce ke amfani da kotu domin kawo wa jam'iyyarmu karan tsaye'', kamar yadda ya yi iƙirari.
A baya dai APC ta sha musanta yin katsalandan a harkokin cikin gida na jam’iyyun hamayya.











