Wane ne Tanimu Turaki: Sabon shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya?

Kabiru Tanimu Turaki

Asalin hoton, @kabiruturakisan

Lokacin karatu: Minti 3

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki SAN, a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.

An zaɓi tsohon ministan ne yayin babban taron jam'iyyar na ƙasa da ke gudana a Ibadan babban birnin Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan sanata Lado Ɗan Marke da ƙuri'u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, da wakilai 3, 131 suka halarta.

Hakan dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta PDP ta dakatar da Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar, yayin da gwamnonin Adamawa da na Fulato suka ƙalubalanci matakin suna masu cewar matakin ka iya ƙara rura wutar rikicin da jam'iyyar ke ciki.

A kujeru biyu ne dai aka yi zaɓe ababban taron jam'iyyar na ƙasa, yayin da dama daga sauran kujerun shugabancin jam'iyyar kuma aka yi maslaha a tsakanin ƴan takara wanda daga bisani aka kira wakilai daga jihohi suka kaɗa ƙuri'unsu kamar yadda dokar hukumar zaɓen Najeriya ta tanada.

Yadda zaɓen ya gudana

Sanata Umar Tsauri, ɗaya ne daga cikin ƴan kwamitin Amintattun jam'iyyar ta PDP, ya shaida wa BBC cewa yanzu an zaɓi sabbin shugabannin jam'iyyar PDP da za su ja ragamar jam'iyyar har zuwa nan da shekaru hudu masu zuwa.

Ya ce,"Yau sabon shugaban jam'iyyar PDP, shi ne Kabiru Tanimu Turaki."

Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya samu ƙuri'u 1,516 daga cikin ƙauri'u 1, 834 da aka kaɗa a yayin zaben.

Gabanin fara gudanar da zaɓen, jam'iyyar ta PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da Samuel Anyanwu, da Kamaluddeen Ajibade, da Ayo Fayose, da Austin Nwachukwu, kan zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

To sai dai jim ƙaɗan bayan fitar da wannan sanarwa ce sai gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya nuna rashin amincewar sa da korar su Wike daga jam'iyyar.

Inda ya ce matakin zai ƙara rura wutar rikicin da jam'iyyar ke ama da shi.

Wani abin jan hakali a game da taron na PDP, shi ne yadda ba a ga fuskokin gwamnonin jihohin Osun, da Taraba, da na Ribas ba, a wajen taron.

Tun dai gabanin taron an samu mabambantan umarni daga kotuna da suka ci karo da juna game da taron, inda wasu suka bai wa jam'iyyar damar ci gaba da taron, yayin da wasu kuma suka hana.

Wane ne Kabiru Tanimu Turaki?

Kabiru Tanimu Turaki

Asalin hoton, Kabiru Tanimu Turaki/Facebook

An haifi Kabiru Tanimu Turaki a ranar 3 ga watan Afrilun 1957 a Birnin Kebbi na jihar Kebbi

Ya karanta fannin shari'a a Jami'ar Jos kuma ya kammala a 1985. An kira shi zuwa majalisar lauyoyi ta Bar (Nigerian Bar) a 1986.

Ya zama Babban Lauyan Najeriya (Senior Advocate of Nigeria - SAN) a shekarar 2002, kuma shi ne shugaban kamfaninsa mai suna K.T Turaki & Co

Ya yi aiki a matsayin ministan ayyuka na musamman a ƙarƙashin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan daga 2013 zuwa 2015. Ya kuma rike muƙamin ministan ƙwadago na riƙo, sannan ya shugabanci kwamitin shugaban Kasa kan tattaunawa da samar da zaman lafiya a Arewa

Kafin ya zama shugaban PDP, ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2018 amma bai yi nasarar samun tikitin ba, sannan ya kasance shugaban ƙungiyar tsoffin ministocin PDP (PDP Former Ministers' Forum).

Yana riƙe da sarautun gargajiya da suka haɗa da Dan Masanin Gwandu da Zarumman Kabbi.