Ko taron PDP zai gudana duk da umarnin kotuna da barazanar Wike?

Shugaban PDP na ƙasa Ilya Damagun (tsakiya) da sauran shugabanni a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto, Yanzu haka PDP ta rabu gida biyu bayan ɓangaren Wike ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar Ilya Damagun (tsakiya)
Lokacin karatu: Minti 4

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta ranar Asabar kamar yadda ta tsara duk da umarnin kotuna masu karo da juna.

Umarnin wata babbar kotun jihar Oyo a ranar Alhamis da ya goyi bayan ci gaba da shirin gudanar da taron, shi ne na baya-bayan, inda ta jaddada umarnin da ta bayar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙorafin da mai ƙara ya shigar.

Masu ƙorafin sun nemi kotun ta dakatar da shugaban PDP na ƙasa, Ilya Damagun, da kwamatin gudanarwa, daga hana gudanar da taron kamar yadda aka tsara, bayan umarnin wata kotu da ya ce a dakata.

Tuni PDP ta ce shirye-shirye sun yi nisa a filin wasa na Lekan Salami da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo, inda yayin taron za a zaɓi sababbin shugabanni a muƙamai daban-daban a matakin ƙasa.

A makon da ya gabata ɓangaren da ke biyayya ga Ministan Abuja Nyesom Wike ya dakatar tare da kafa sabon kwamatin amintattu na PDP, wanda shi ne mafi girma a tsarin shugabancin jam'iyyar. Sun kuma dakatar da Ilya Damagun da sauran manyan shugabanni.

Sun ɗauki matakin ne bayan kwamatin gudanarwar PDP ya dakatar da wasu shugabannin jam'iyyar da ke yi wa Wike biyayya, ciki har da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu.

A gefe guda kuma, tsohon Gwmanan Jigawa Sule Lamido ma ya shigar da jam'iyar ƙara yana ƙalubalantar hana shi sayen tikitin takarar shugabancin jam'iyyar na ƙasa kafin zaɓen na ranar 15 ga wata.

Umarnin kotuna masu karo da juna

1 - PDP ta fara fuskantar umarnin kotu ne a ranar 31 ga watan Oktoba, lokacin da babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci a dakatar da shirin gudanar da babban taron na ƙasa.

Mai Shari'a James Omotosho ya bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta iya ci gaba da shirin gudanar da taro na 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Mutum uku da suka shigar da ƙarar abokan siyasar Ministan Abuja Nyesom Wike ne, wanda ya ci alwashin hana gudanar da taron sakamaon rigimar da yake yi da shugabancin jam'iyyar.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa PDP ta gaza wajen bin dokokin mulkin jam'iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 game da shirin gudanar da taron.

Lauyan masu ƙorafi ya faɗa wa kotun cewa PDP ba ta gudanar da zaɓukan shugabancin jam'iyyar ba a jihohi 14, inda ya nemi kotun ta duba ko hakan ya saɓa wa doka.

Kazalika, a kwanan nan Sakataren PDP na Ƙasa, wanda abokin siyasar Wike ne, ya shigar da ƙorafi ga jami'an tsaron Najeriya cewa shugabancin jam'iyyar sun saci sa-hannunsa a takardar da suka aika wa hukumar zaɓe Inec ta sanar da babban taron, zargin da PDP ta musanta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

2 - Sai kuma a ranar Talata 11 ga watan Nuwamba wata babbar kotun a Abuja ta sake bayar da umarnin dakatawa da shirin gudanar da taron sakamakon ƙarar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya shigar.

Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin ne tana cewa har sai ta kammala sauraron ƙorafin na Sule, sannan ta hana hukumar zaɓe zuwa domin saka ido a zaɓen.

Alƙalin ya ƙara da cewa ya aminta da ƙorafin da Sule ya shigar na cewa PDP ba ta wallafa jadawalin yin taron ba saboda mambobinta su sani kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.

Sai dai a ranar Alhamis ya kamata kotun ta bayar da hukuncinta kamar yadda ta tsara, amma sai ba ta yi hakan ba, abin da ya ƙara jefa mai ƙorafin da ma jam'iyyar cikin ruɗani.

3 - A wani umarni mai cin karo da wancan, a ranar 4 ga watan Nuwamba babbar kotun jihar Oyo ta umarci PDP ta ci gaba da shirin taron bayan wani ƙorafi

Mai Shari'a Ladiran Akintola ya umarci jami'an PDP da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na dakile ko karya jadawalin da aka aka fitar, sannan ya umurci hukumar zabe ta tura jami'anta domin sa ido.

"Wannan mataki babbar nasara ce ga jam'iyya domin yanzu kwamitin shirya taron NCOC na da damar kammala shirye-shiryen karɓar sama da wakilai 3,000 da ake sa ran halartarsu daga jihohi daban-daban," a cewar PDP cikin wata sanarwa a lokacin.

'Taro babu fashi'

PDP ta ce ta kaɗu da umarnin kotu na farko, wanda ya nemi a dakata da shiri.

Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Debo Ologunagba ya fitar a yammacin 31 ga watan Oktoba, PDP ta ce "ta kaɗu" da hukuncin kotun, amma ba zai kawo mata tsaiko ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa wani hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan "ya tabbatar da ikon jam'iyya wajen tafiyar da al'amuranta na cikin gida da kanta", sannan ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin.

A ranar Alhamis PDP ta wallafa hotuna da bidiyo na shirye-shiryen taron da ake yi ƙarƙashin Mataimakin Gwamnan Oyo Bayo Lawal, wanda shi ne shugaban ƙaramin kwamatin tsara wurin taro.

A hannu guda kuma, tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya shawarci jam'iyyar tasu ta dakatar da shirin gudanar da babban taron saboda umarnin kotuna kan hakan.

Saraki ya bayar da shawarar ce cikin wani saƙo a dandalin X bayan wata ganawa da kwamatin sasanta 'ya'yan jam'iyyar ƙarƙashin jagoracin Hassan Adamu.

Tsohon shugaban da ya jagoranci majalisa daga 2015 zuwa 2019 ya ce umarnin kotuna masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala game da halaccin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.