Me ya sa har yanzu PDP ta kasa magance matsalolin da ke damunta?

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, sakamakon rushe shugbannin reshen jam'iyyar na jihar Akwa Ibom.
Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba ne ya bayar da sanarwar rushe shugabannin reshen daga muƙamansu, tare da maye gurbinsu da wasu.
To amma matakin ya fuskanci turjiya daga babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu wanda ya soki matakin tare da neman yin watsi da shi.
Yana mai cewa an ɗauki matakin ne ba tare da sanin kwamitin zartarwar jam'iyya na ƙasa ba.
Mista Anyanwu ya ce ya bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar da aka yi wa gyara a 2017, dakatarwar ba ta da wani tasiri
Jam'iyyar dai ta ce tana sane da irin waɗannan matsaloli da take fuskanta a wasu jihohi, kuma tana ƙoƙarin ɗaukar matakan magance su.
Muna ƙoƙarin magance matsalar - PDP
Muƙaddashin jami'in hulda da jama'a na Jami'iyyar Alhaji Ibrahim Abdullahi ya ce sun san matsaloli da ake samu a wasu jihohin ƙasar, kuma tana bakin ƙokarinta wajen magance su.
Ibrahim Abdullahi ya shaida wa BBC cewa akwai jihohi irin su Kebbi da Filato da Cross River.
''A waɗannan jihohi an samu wasu da suka yi gaban kansu wajen naɗa sabbin shugabannin riƙo, wanda hakan kuma ya saɓa wa doka, kuma ba ya kan tsarin jam'iyyarmu'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa a baya-bayan nan shugaban jam'iyyar tare da amincewar kwamitin gudanarwa, sun fitar da wasiƙun da ke ɗauke da jadawalin yadda za a gudanar da zaɓuka a wasu jihohin ƙasar.
''To amma sai wasu suka yi raɗin kansu ba tare da aiki da wancan umarnin, suka yi abin da suke so, saboda wata manufarsu ta daban'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam'iyyar na baƙin ƙoƙarinta wajen ganin ta magance wannan matsaloli.
A watan Maris da ya gabata ma kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya gudanar da wani taro a birnin Abuja, don duba matsalolin da jam'iyyar ke fama da su da nufin warware su.
Mene ne asalin rikicin PDP?

Asalin hoton, PDP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jam'iyyar PDP dai ta faɗa rikicin cikin gida ne tun lokacin zaɓen fitar da wanda zai tsaya mata takara a zaɓen 2023.
A zaɓen ne tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya samu nasarar doke babban abokin hamayyarsa tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.
Bayan zaɓen ne Atiku ya ɗauki tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa a matsayin mataimaki, wani abu da wasu ke ganin bai yi wa Wike daɗi ba, daga nan kuma aka shiga takun-tsaka tsakanin tsagin Wike da na Atiku, lamarin da wasu ke alaƙanta rashin nasarar Atiku a Rivers da shi.
Dokta Yakubu Haruna Ja'e malami a sashen nazarin kimiyar siyasa a jami'ar jihar Kaduna ya ce tun daga wancan lokaci Wike ya ja wata zugar magoya bayansa tare da shiga gwamnatin APC, har ma ya karɓi muƙamin babban ministan Abuja.
''Ya shiga gwamnatin APC ba tare da ficewa daga jam'iyyarsa ta PDP ba, wannan kuma shi ƴan siyasa ke kira anti Party, wato yi wa jam'iyya zagon-kasa'', in ji shi.
Bayan nan an riƙa zargin Wike da hana ruwa gudu a jam'iyyar, wani abu da ake ganin ya kasa daidaita lamuransa, lamarin da ya sa Atiku da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal suka koma haɗakar ADC.
Me ya sa PDP ta kasa rabuwa da matsaloli?
Dokta Yakubu Haruna Ja'e ya ce babban abin da ya hana jam'iyyar daidato shi ne matsalar zagon-ƙasa da wasu mambobinta ke yi.
''Da a ce duka mambobin jam'iyyar za su haɗa kai, su daina ci wa jam'iyyar dunduniya, su mayar da hankali, kowa ya haƙura da son zuciyarsa, to da an kawo ƙarshen matsalar'', in ji shi.
Ya kuma ce wata matsalar da ta hana warware rikicin jam'iyyar shi ne yadda siyasar ƙasar a yanzu ke tafiya na kowa abin da zai samu ne kawai ya sanya a gabansa.
''Da dama ƴansiyasar a yanzu za ka tarar da cewa abin da zai samu ne a gabansa ba jam'iyyar ba'', in ji malamin jami'ar.
Haka kuma masanin siyasar ya bayyana rashin adalci a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ya sa jam'iyyar ta kasa magance matsalolinta.
''Da yawa cikin ƴan jam'iyyar akwai masu ganin cewar ba a yi musu adalci, to idan jam'iyyar ta saurare su ta kuma biya musu buƙatunsu za a samu sauƙin abubuwa'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ce matsalar rashin adalci ne ke haifar da rushe wasu shugabanninta a wasu wuraren.
Wace illa rikicin cikin gida zai yi wa PDP?
Dokta Yakubu Ja'e ya ce idan har jam'iyyar ba ta ɗauki matakin magance rikice-rikicen da take fama da su ba, to lallai za ta iya yi mata babbar illa.
''Matsawar ba ta yi ƙoƙarin magance rikice-rikicenta ba, to za ta iya rasa kambinta na babbar jam'iyyar hamayya'', in ji shi.
A yanzu dai jam'iyyar ce babban jam'iyyar hamayya a ƙasar, inda take gwamnoni 10 da ƴan majalisu masu yawan.
To amma masanin siyasar ya ce idan har jam'iyyar ta gaza warware matsalolinta to ba shakka za ta iya rasa wasu gwamnonin da ma ƴan majalisar a zaɓen 2027 da ke tafe.
Matakan da ya kamata ta ɗauka
Masanin siyasar ya ce akwai matakai da ya kamata jam'iyyar ta ɗauka domin warware matsalolin da take fama da su, kamar haka:
- Hukunta waɗanda suka yi laifi
Ya ce abin da ya kamata jam'iyyar ta yi shi ne hukunta duk wanda aka samu da laifin ci wa jam'iyya dunduniya.
''Babu yadda za a yi wasu suna laifi amma a ƙi hukunta su, sannan a yi tunanin wasu ma ba za su aikata ba'', in ji shi.
- Adalci
Dokta Ja'e ya ce yana da kyau jam'iyyar ta tabbatar da adalci a kan duka mambobinta.
''Idan har ya zama ba a yin adalci wa wasu mambobin jam'iyyar babu yadda za a rikici ya ƙare a jam'iyyar'', in ji shi.
Malamin jami'ar idan jam'iyyar ba ta yi hattara ba, lokaci na dab da ƙure mata, kasancewar an fara mayar da hankali kan zaɓen 2027, kuma tuni jam'iyyar APC mai mulki da sabuwar jam'iyyar ADC sun fara zawarcin wasu daga cikin mambobinta.
- Haƙurƙurtar da waɗanda aka ɓatawa
Wata hanya da PDP za ta magance matsalolin da take fama da su shi ne ta hanyar haƙurƙurtar da mambobinta da aka ɓata wa rai.
Sai dai Dakta Ja'e ya ce a baya jam'iyyar ta gwada wannan hanya amma ba a samu biyan buƙata ba.











