Su wane ne manyan ƴansiyasar Najeriya da suka rage a PDP?

Nyesom Wike da Goodluck Jonathan da Bala Mohammed

Asalin hoton, FB/GETTY

Bayanan hoto, Nyesom Wike da Goodluck Jonathan da Bala Mohammed
Lokacin karatu: Minti 7

Yawan gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya ya ragu zuwa takwas, bayan fitar gwamnan Enugu Peter Mbah da na Bayelsa Douye Diri a cikin makon nan.

Wannan sauye-sauyen sheƙa sun ƙara raunana babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya wadda take da gwamnoni 12 bayan babban zaɓen ƙasar na 2023.

A yanzu jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar na iko ne da jihohi 24 daga cikin 36 na ƙasar, yayin da PDP ke da takwas.

LP da APGA da NNPP kuma kowacce tana da jihohi ɗaɗɗaya.

Waɗanne gwamnoni ne suka saura a cikin PDP?

Wasu gwamnonin jam'iyyar PDP alokacin taron da suka gudanar a jihar Zamfara cikin watan Agustan 2025, sai dai wasu daga cikinsu a yanzu sun sauya sheƙa

Asalin hoton, FB/DAUDA LAWAL

Bayanan hoto, Wasu gwamnonin jam'iyyar PDP alokacin taron da suka gudanar a jihar Zamfara cikin watan Agustan 2025, sai dai wasu daga cikinsu a yanzu sun sauya sheƙa

Ya zuwa ranar 15 ga watan Oktoban 2025, gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar PDP waɗanda har yanzu suke cikin jam'iyyar su ne:

  • Ahmadu Fintiri - Jihar Adamawa (Arewa maso Gabas)
  • Bala Mohammed - Jihar Bauchi (Arewa maso Gabas
  • Caleb Mutfwang - Jihar Filato (Arewa ta tsakiya)
  • Agbu Kefas - Jihar Taraba (Arewa ta tsakiya)
  • Dauda Lawal - Jihar Zamfara (Arewa maso Gabas)
  • Seyi Makinde - Jihar Oyo (Kudu maso Yamma)
  • Siminalayi Fubara - Jihar Rivers (Kudu maso Kudu)
  • Ademola Adeleke - Jihar Osun (Kudu maso Yamma)

Waɗanda aka zaɓa ƙarƙashin PDP amma suka sauya sheƙa su ne:

  • Umo Eno - Jihar Akwa Ibom (Kudu maso Kudu)
  • Sheriff Oborevwori - Jihar Delta (Kudu maso Kudu)
  • Peter Mbah - Jihar Enugu (Kudu maso Gabas)
  • Douye Diri - Jihar Bayelsa (Kudu maso Kudu)
Enugu state govnor Peter Mbah during im defection ceremony go di APC

Asalin hoton, Peter Mbah/X

Waɗanne manyan ƴan siyasa ne suka saura a jam'iyyar?

Baya ya gwamnoni masu faɗa a ji a jam'iyyar, kamar Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na na jihar Oyo, ana ganin cewa har yanzu akwai sauran ƴan siyasa masu ƙwari wadanda masana siyasa ke ganin za su iya tantance makomar jam'iyyar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu daga cikinsu su ne:

Nyesom Wike:

Duk da cewa yana riƙe da muƙamin minista a gwamnatin jam'iyyar APC mai mulki, har yanzu ƙarfin faɗa a ji da Wike ke da shi a cikin jam'iyyar abu ne ƙarara.

A tsawon shekaru, Wike ya kasance ƙusa a jam'iyyar PDP a kudancin Najeriya. A lokacin da yake gwamna ya yi hadaka da ƴan siyasa, ya tallafa wa ƴan takara da kuɗaɗe har suka samu nasara a zaɓuka, sannan alaƙarsa da ƴan siyasa a fadin Najeriya ta sanya shi ya zama jigo a jam'iyyar.

Sai dai har yanzu ana tantama kan rawar da zai iya takawa a zaɓe mai zuwa.

Ahmed Muhammed Makarfi:

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na riƙo. Shi ne gwamnan jihar Kaduna na tsawon shekara takwas daga shekarar 1999, sannan bayan haka ya zama sanata.

Yana daga cikin ƴan siyasa waɗanda ke da matuƙar tasiri, kuma a lokuta da dama ke sanya baki wajen ganin PDP ta samu mafita daga rikice-rikice.

Goodluck Jonathan:

A baya-bayan nan sunan Jonathan na yawan fitowa a labarai a matsayin wanda jam'iyyar PDP ke ganin zai iya ceto ta daga garari, musamman idan ya amince cewa zai tsaya mata takara a 2027.

Duk da cewa a lokacin da yake mulki ya sha suka daga kowane ɓangare na ƙasar kan gaza fitar da Najeriya daga halin ƙunci da rashin tsaro, amma dattakon da ya nuna bayan shan kaye a hannun jam'iyyar adawa a zaɓen 2015 ya sanya ana ganin sa da mutunci da ƙima.

Wannan ya sanya har wasu ke marmarin ganin ya sake shiga fagen siyasa, domin akwai rawar da suke ganin zai taka.

Babu shakka matuƙar tsohon shugaban na Najeriya ya amince cewa zai wa PDP takara a 2027, wannan zai iya yin tasiri ga makomar jam'iyyar.

Sule Lamido:

Duk da cewa a baya-bayan nan Sule Lamido ya bayyana cewa yana tare da ƴan adawa masu haɗakar yunƙurin kayar da Tinubu a 2027, babu wanda yake tantama game da kasancewar Sule a matsayin uba kuma jagora a PDP.

A kodayaushe yakan bugi kirjin cewa yana daga cikin wadanda suka assasa jam'iyyar PDP, kuma ba zai fita daga cikinta ba.

Sai dai ko yana da tasirin da zai iya taimaka wa jam'iyyar fita daga cikin halin da take ciki na rikita-rikita?

Mu'azu Babangida Aliyu:

Tsohon gwamnan jihar Neja ya kasance ɗaya daga cikin gwamnonin Najeriya da aka jin su a lokacin da yake kan mulki, sai dai tun bayan da ya yi kusufi ba a cika jin duriyarsa ba.

Sai a baya-bayan nan lokacin da ya gargaɗi PDP kan yin taka-tsantsan da ƴan saiyasa waɗanda suka fita daga jam'iyyar kuma suke neman su dawo.

Ko Babangida Aliyu zai taka rawa wajen tsamo jam'iyyar daga halin da take ciki?

Ƴanmajalisar dokokin tarayya da suka bar PDP tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu

Wasu mashahuran ƴan majalisar wakilai da kuma sanatoci da suka sauya sheƙa daga PDP su ne:

  • Sanata Adamu Aliero - (Kebbi ta tsakiya)
  • Sanata Abdulrahaman Kawu Sumaila (Kano)
  • Sanata Yahaya Abdullahi - (Kebbi ta arewa)
  • Sanata Garba Maidoki - (Kebbi ta kudu)
  • Sanata Ekong Sampson - (Akwa Ibom ta kudu)
  • Sanata Etim Bassey - (Akwa Ibom ta arewa maso gabas)
  • Sanata Ned Nwoko - (Jihar Delta)
  • Sanata Francis Fadahunsi - (Osun ta gabas)
  • Sanata Olubiyi Fadeyi - (Osun ta tsakiya)
  • Sanata Samaila Dahuwa - (Bauchi ta arewa)
  • Adamu Tanko - Gurara/Suleja/Tafa (Neja)
  • Abdullahi - Bakori/Danja (Katsina)
  • Aliyu Illiyasu - Safana/Butsari (Katsina)
  • Salisu Majigiri - Mashi/Dutsi (Katsina)
  • Christian Nkwonta - Ukwa ta gabas/Ukwa ta kudu (Abia)
  • Erhiatake Ibori-Suenu - Ethiope ta kudu (Delta)
  • Magaji Gwamna - Jaba/Zango Kataf (Kaduna)
  • Salisu Garba - Koko/Besse/Mayama (Kebbi)
  • Abdullahi Dabai - Bakori/Danja (Katsina)
  • Yusuf Galambi (Jigawa) NNPP zuwa APC
  • Aliyu Wadada (Nasarawa) - SDP zuwa APC Nasarawa
  • Kabiru Alhassan Rurum (Kano) - NNPP zuwa APC
  • Abdullahi Sani Rogo (APC) - NNPP zuwa APC

Ɗaukacin ƴan majalisar wakilan tarayya daga jihar Delta sun bayyana cewa sun sauya sheƙa a watan Afrilu, bayan da gwamnan jihar Sheriff Oborevwori, tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa da dukkanin ƴaƴan jam'iyyar PDP na jihar suka bayyana sauya sheƙarsu.

Sauya sheƙar ƴan majalisar dokokin jihohi

Gwamnan jihar Delta da sauran shugabannin jam'iyyar APC lriƙe da tutar jam'iyyar bayan sauya sheƙa daga PDP

Asalin hoton, Rt Hon Sheriff Oborevwori/X

  • Majalisar dokokin jihar Bayelsa: Lokacin da gwamna Duoye Diri ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa ya fice tare da shugaban majalisar dokokin jihar Hon. Abraham Ingobere, da ƴan majalisar jihar, da shugabannin ƙananan hukumomi da kwamishinoninsa da duk wani mai riƙe da muƙamin siyasa.
  • Ƴanmajalisar tarayya da na jihar Delta: A ranar 28 ga watan Afurilu, gwamnan jihar Bayelsa Sheriff Oborevwori ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa shi da ɗaukacin shugabancin jam'iyyar PDP a jihar ta Delta, daga matakin gunduma har zuwa jiha, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
  • Jihar Enugu — Lokacin da gwamna Peter Mbah ya sauya sheƙa a ranar 14 ga watan Oktoba, ya ce ɗaukacin ƴansiyasa na jihar, waɗanda suka haɗa da wakilan majalisar dokokin tarayya, da na jiha, da na majalisar zartarwar jihar, da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da masu riƙe da muƙaman gwamnati da kuma sama da kashi 80% na shugabannin jam'iyyar a jihar sun bi sawun shi.

Me ya sa gwamnoni ke fita daga PDP?

Akasarin gwamnoni da sauran ƴan siyasa da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa na kafa hujja ne da ƙoƙarin ganin ana ɗasawa da al'ummarsu a matakin tarayya.

Gwamna na baya-bayan nan da ya sauya sheƙa, Peter Mbah na jihar Enugu ya ce matakin ba abu ne mai sauƙi ba.

Ya ce al'ummar Kudu maso Gabas sun kwashe kimanin shekara 30 suna biyayya ga PDP ta hanyar ba ta cikakken goyon baya da sadaukar da rayuwarsu gare ta, amma duk da haka ba ta martaba su yadda ya kamata.

"A duk lokacin da suke ɗaukar wani mataki a matakin tarayya, ba sa ɗaukar mu da muhimmanci."

Ya ƙara da cewa "a yanzu PDP ba ta da nagartar zama jam'iyyar da za a bi domin cimma muradun yankin. Domin cika burinmu, za mu karkata zuwa ga ɓangaren da zai martaba mu da kuma ƙarfafa manufofinmu."

Shi ma gwamna Diri na jihar Bayelsa, wanda ya bar PDP bayana-bayan nan ya ce ya sauya sheƙa ne "bisa dalilai bayyanannu".

Me sauya sheƙar ƴan'adawa ke nufi ga siyasar Najeriya?

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, sanata Seriake Dickson wanda ya sake jaddada mubaya'arsa ga PDP, ya ce gwamnonin da ke sauya sheƙa suna wofintar da dimokuraɗiyya ne.

Wani farfesa kan harkokin shari'a a jami'ar Jihar Rivers, Ritchard Wokocha ya ce yawaitar masu ficewa daga PDP a baya-bayan nan na nuna cewa jam'iyyar na rasa karsashinta.

Farfesa Wokocha ya ce a kudu maso kudancin Najeriya inda, PDP ce ke iko da yankin kafin yanzu, inda a yanzu gwamnan jihar Rivers ne kaɗai ya rage a jam'iyyar yayin da akasarin gwamnonin suka sauya sheƙa zuwa APC.

"Yanzu da kusan dukkanin gwamnonin suka koma APC, hakan na nufin cewa jam'iyyar PDP ta suma, domin a jihar Rivers ne kawai gwamnan bai fito fili ya bayyana cewa ya fita daga jam'iyyar ba, saboda haka za a iya cewa ta kusa mutuwa a kudu maso kudu."

Ya ƙara da cewa hakn na nufin karsashi da kuma damar da PDP ke da shi a matakin ƙasa baki ɗaya na zagwanyenwa, kuma idan ba a yi hankali ba "za ta iya mutuwa baki ɗaya."

A cewarsa, irin wannan lamari zai iya haifar da tsarin jam'iyya ɗaya a Najeriya, idan aka yi la'akari da irin tururuwar da ƴan adawa ke yi zuwa jam'iyya mai mulki.

Farfesa Wokocha ya ce wannan na nuna yadda tsarin shafa zuma a baki da kuma barazana ke aiki, kuma manufar hakn shi ne tabbatar da sake komawar shugaban ƙasa kan mulki a karo na biyu.

"Wannan na nufin cewa ba masu kaɗa ƙuri'a ne suka fi muhimmanci a siyasar Najeriya ba, ba masu kaɗa ƙuri'a ne ke tantance wanda zai jagoranci ƙasar ba, shi ya sa suke janye masu riƙe da mukamai a jihohi domin kauce wa duk wata turjiya," in ji shi.

Taswirar Najeriya bisa la'akari da jam'iyyar siyasa da ke mulkin jiha
Bayanan hoto, Taswirar Najeriya bisa la'akari da jam'iyyar siyasa da ke mulkin jiha