Mun yi maraba da hukuncin kotun jiha a kan babban taronmu na ƙasa — PDP

Umar Iliya Damagum

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu jiga-jigan babbar jami'iyyar adawar Najeriya ta PDP sun soma martani game da hukuncin da wata babbar kotun jiha ta yanke na ba wa jam'iyyar damar ci gaba da shirye shiryen gudanar da babban taronta na kasa da ta tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwambar 2025.

Wannan matakin dai na zuwa ne kwanaki bayan wata babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin hana gudanar da taron.

Dattawan jam'iyyar ta PDP na ganin matakin na kotun da ke jihar Oyo ta dauka a matsayin abin maraba.

Dattawan sun ce a shirye s uke su gudanar da babban taron na kasa a lokacin da aka tsara.

Sanata Umar Tsauri, na daga cikin 'yan kwamitin amintattu na jam'iyyar ta PDP ya shaida wa BBC yadda suka yi maraba da wannan mataki na kotun.

Ya ce,"Kamar ace mutum ne ya yi jifa, sai kuma ya jefi abin da ake so, to yanzu kowa ya san wannan hukunci shi ne dai-dai domin kafin hukuncin ya kamata jama'a sus ani cewa kotun koli ta kasa sau uku tana yanke hukunci akan cewa dukkan matsalar shugabancin jam'iyya na jam'iyya ne kotu babu ruwanta."

Sanata Tsauri, y ace," Idan na samu wata kotu ta yanke hukunci wanda ya fi wannan misali kotun daukaka kara ta ce mu dakata da taron, to sai mu dakata, amma idan aka samu akasin haka, to hukuncin da kotun jihar Oyo ta yanke mu dama ya yi mana sai mu yi taronmu."

"Mu jam'iyyarmu ta PDP tana bin doka kwarai da gaske, a don haka yanzu mu zamu ci gaba da shirye-shirye na yin babban taronmu na kasa a lokacin da aka tsara." In ji shi.

Dan jam'iyyar ta PDP, ya ce,"Mu ba sabon abu ne mu samu kanmu cikin irin wannan hali , to amma da mun shiga daki muna da shugabannin na gari aka tattauna da an fito daga dakin sai ka ga kowa na fara'a."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai masana lamuran siyasa a Najeriya na ganin hukunce- hukuncen sun ci karo da juna, kuma suna ma iya dagula rikicin siyasar da ya dabaibaye jama'iyyar.

Farfesa Abubakar Kari, malami ne a bangaren nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa, wannan yanayi da jam'iyyar ta PDP ta tsinci kanta, yanayi mai tayar da hankali kwarai da gaske kuma ya yi kama da wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya.

Ya ce," A lokacin da aka yi dambarwar zaben 12 ga watan Yulin 1993, dalilan kotu masu matsayi daya su rika yanke hukuncin da ke karo da juna, wannan dalilin sojoji suka yi amfani da shi suka soke zaben, a don haka wannan yanayi da PDP ke ciki a yanzu za iyi mummunan tasiri ba jam'iyyar PDP kadai ba har ma da bangaren shari'a domin da sannu a hankali shi me sashen zai fada cikin dambarwa kuma hakan ba za iyi wa kasar kyau ba."

"Idan mambobin jam'iyyar PDP ba suyi karatun ta nutsu ba, sun zauna sun sasanta kansu ba, to wannan hali da ake ciki a jam'iyyar zai rage mata karsashi da martaba a idon duniya." In ji shi.

Duk da wannan hukuncin kotun ya cire duk wasu matsalolin doka d ake kokarin jinkirta gudanar da taron, har yanzu ba a ji irin matakin da bangaren Samuel Anyawu da ake ganin na hannun daman ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ne, ya dauka ba.