Ƙasashen da azuminsu zai fi tsawo a 2026

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata 17 ko Laraba 18 ga watan Fabrairu ne ake sa ran za a fara azumin watan Ramadan na shekarar miladiyya ta 2026 a Najeriya da wasu ƙasashen da dama a sassan duniya.
Azumin watan Ramadan na cikin rukunnan Musulunci guda biyar, wanda hakan ya sa azumin ya zama tilas a kan dukkan musulmi a faɗin duniya, matuƙar sun cika sharuɗan azumin.
Haka kuma ana azumin ne na kwana 29 ko 30 a watan daga hudowar Alfijir zuwa faɗuwar rana.
Sai dai ana samun bambancin yanayin tsawon azumin, inda hakan ya sa lokutan yake bambanta a ƙasashe da dama a faɗin duniya.
A lokacin zafi, ƙasashen da ke arewacin duniya kamar na Turai suna shafe yini mai tsawo kafin su yi buɗa-baki, yayin da wasu ƙasashen Afirka kuma ke fuskantar matsanancin zafi a lokutan bazara, wanda hakan ya sa lokacinsu yake bambanta.
Ganin yadda ake samun bambancin lokutan ne ya sa BBC ta yi nazari kan sa'o'in azumi na wasu ƙasashen duniya.
Dalilin da ya sa ake samun bambancin lokaci

Domin jin dalilan da suka sa ake samun bambancin lokaci azumi a ƙasashe daban-daban, BBC ta zanta da ɗan kwamitin duba wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril, wanda ya ce akwai wasu abubuwan dubawa.
Ya ce duk da cewa wajibi ne azumin a kan kowa da kowa, tsawon azumin yau da kullum yana bambanta sosai, kuma a cewarsa ya danganta da yanayin ƙasa da lokacin shekara.
"A wasu sassan duniya, Musulmai na iya yin azumi fiye da awa 20 a rana, yayin da a wasu wuraren kuma, lokutan azuminsu ba zai wuce awa 10 ba," in ji shi a zantawarsa da BBC Hausa.
Wuraren da azuminsu ya fi tsawo
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Simwal Usman Jibril ya ce ana yin azumi mafi tsawo ne a yankunan arewacin turai da yankunan Arctic, inda hasken rana ke ƙaruwa har zuwa maraice a lokacin bazara.
Biranen da ke da wasu lokutan azumi mafi tsawo sun haɗa da:
- Tromso - Norway kimanin awa 20 zuwa 22
- Reykjavik - Iceland kimanin awa 20 zuwa 21
- Murmansk - Rasha kimanin awa 20 ko fiye da haka
- Stockholm - Sweden kimanin awa 18 zuwa 19.
A game da dalilan da suka waɗannan biranen za su fuskanci lokaci mai tsawo, masanin ya ce, "saboda suna da nesa da shatn layin tsakiyar duniya, inda lokutan hasken rana ke ƙaruwa sosai yayin da lokacin bazara ke gabatowa."
Ya ce idan Ramadan ya faɗa a kusa da lokacin bazara, rana tana kasancewa a bayyane na tsawon lokaci, wanda ke tsawaita lokacin azumi.
A cewarsa, "saboda Ramadan yana bin kalandar watan Musulunci, wanda ke kusan raguwa na kwana 10 zuwa 11 fiye da shekarar rana. Watan Ramadan yana canzawa a kowace shekara, wannan na nufin lokutan azumi suna canzawa daga shekara zuwa shekara."
Ya ƙara da cewa ana shiga cikin mawuyacin hali a wuraren da rana ba ta faɗuwa wasu lokutan, inda ya ce "wasu malaman Musulunci suna ba wa Musulmai da ke wannan yankin fatawar bin wasu qasashe kaman Makka ko na wurin da ya fi kusa da su da ake samun dare da rana a kullum."
Wuraren da azumi zai fi gajarta
A game da wuraren da azuminsu ke gajarta, masanin ya ce Musulmai da ke sassan kudancin duniya suna fuskantar gajerun lokutan azumi. Biranen da ke da gajerun lokutan azumi sun haɗa da:
- Ushuaia - Argentina kusan awa 10 zuwa 11
- Punta Arenas - Chile kusan awa 10 zuwa 11
- Christchurch - New Zealand kimanin awa 11
- Cape Town - Afirka ta Kudu kimanin awa 11 zuwa 12.
Ya ƙara da cewa idan Ramadan ya faɗa a watan Maris ko Afrilu, "yana daidai da kaka a kudancin duniya, kuma lokaci ne da kwanaki ke ƙara gajarta. Sannan kuma waɗannan yankuna suna cikin matsakaicin layin da ke raba duniya gida biyu, don haka ba su cika haɗuwa da matsanancin hasken rana ba."
Yanayin azumin Najeriya
Simwal ya ce akwai wasu wurare a wasu ƙasashen da ke kusa da layin rabin duniya, waɗanda ya ce lokutan azuminsu ba su cika canzawa sosai ba a kusan kowace shekara.
Biranen da suke a ƙarƙashin wannan mataki su ne:
- Abuja - Najeriya
- Jakarta - Indonesia
- Kuala Lumpur - Malaysia
- Nairobi - Kenya
Simwal ya ce galibi waɗannan biranen suna samun lokutan azumi na kimanin awanni 12 zuwa 13.
Ya ce hakan na faruwa ne saboda yankunan da ke kusa da layin rabin duniya, waɗanda ya ce suna fuskantar kusan daidai lokacin da suke samun hasken rana da duhu a duk shekara, tare da ƙarancin bambancin yanayi a lokutan fitowar rana da faɗuwar rana.
Da me ake ƙayyade tsawon azumi?
Simwal ya ce akwai abubuwan da ake amfani da su wajen ƙayyade lokuta da tsawon azumi. Mahimman abubuwan da ke tasiri ga tsawon azumi su ne:
- Layin da ya raba duniya kashi biyu
- Yanayi,
- Ɓangaren duniya biyu na arewaci da kudanci
- Kalandar Musulunci ta wata-wata.
"Duk da cewa lokutan azumi na iya bambanta sosai, Ramadan ya kasance watan da Musulmai a duk duniya ke ibadan, azumi, addu'a, sadaka da salloli ba tare da la'akari da tsawon lokacin da a kan yi azumin ba," in ji Simwal a zantawarsa da BBC Hausa.











