Ƴansandan Birtaniya sun kama Andrew kan zargin cin amanar aiki

Asalin hoton, Bav Media
Rundunar ƴansandan yankin Thames Valley a Birtaniya ta fitar da sanarwa a hukumance bayan jami'anta sun kama ƙanin sarkin Ingila Andrew Mountbatten Windsor a ranar Alhamis bisa zargin sa da aikata laifuka da suka saɓa da dokokin aikin gwamnati.
Wannan na zuwa ne bayan rundunar ta ce tana nazarin ƙorafe-ƙorafen da ake yi na zargin cewa Andrew ya fitar da wasu bayanai masu muhimmanci zuwa ga gawurtaccen kawalin nan Jeffrey Epstein. Sai dai Andrew ya musanta zargin aikata wani laifi.
Ga abin da yansanda suka bayyana:
"A cigaba da bincike da muke yi, a yau 19 ga watan Fabrairu, mun kama wani mutum wanda ya haura shekara 60 a yankin Norfolk bisa zarginsa da aikata laifuka, kuma muna ci gaba da bincike a Berkshire da Norfolk.
"Har yanzu mutumin na tsare a hannun ƴansanda
"Ba za mu bayyana sunan mutumin da muke magana a kai ba saboda wasu dalilai. Sannan yana da kyau a fahimci cewa ana gudanar da bincike ne, don haka a bi a hankali domin guje wa ɓata aikin kotu ko aikata laifi.
Jami'in ɗansanda, Oliver Wright ya ce, "mun ƙaddamar da bincike kan zargin aikata laifi.
"Yana da kyau mu kare mutunci da ƙimar binciken da muke yi. Mun fahimci muhimmancin lamarin, don haka za mu bayyana halin da ake ciki a lokacin da ya dace."
Dole doka ta yi aikinta - Sarkin Birtaniya
Da yake jawabi kan kamen, Sarkin Birtaniya ya ce dole a bar doka ta yi aikinta.
"Na samu labarin abin takaici game da zargin Andrew Mountbatten-Windsor ta cin amanar aiki.
"Abin da zai biyo baya a yanzu shi ne cikakken bincike na adalci, wanda kuma kamar yadda na bayyana a baya, za mu ba hukumomin da suke da alhakin bincike duk goyon bayan da suke buƙata," in ji shi.
Ya ƙara cewa da cewa, "ina ƙara nanata cewa dole a bar doka ta yi aikinta. Don haka ba zan ci gaba da magana ba a kan lamarin domin ana gudanar da bincike," in ji shi.











