Ko farashin kayan masarufi ya sauya yayin da aka shiga Ramadan?

Kasuwa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da aka shiga azumin watan Ramadan na bana, wato shekarar 2026, Musulmi a Najeriya na shiga kasuwanni domin sayen kayan azumi musamman kayan masarufi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ƙididdiga ta ƙasar wato NBS ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu da kashi 15.1% a watan Janairun bana.

Wannan sauyin ya faru ne sakamakon daidaita tsarin lissafin da hukumar ke amfani da shi domin ya dace da yanayin kasuwanci a ƙasar.

Hakan ya sa farashin kayan masarufi ya ragu idan aka kwatanta da kashi 27.6% a bara. To sai dai, duk da wannan kyawun ƙididdigar a takarda, wasu na ganin cewa ba su gani a ƙasa ba.

Sai dai da yake jawabi kan alƙaluman masanin tattalin arziki a Najeriya, Alhaji Shuaibu Idris ya ce ko da lissafin hukumar NBS daidai ne, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi domin magance matsalar daga tushe.

"Gaskiya ne farashin kayan masarufi ya sauka, musamman a ƙauyuka. Duk wanda ke zaune a ƙauye ya san haka, amma a birane shin farashin burodi ya sauka? bai sauka ba. Farashin sufuri misali daga Legas zuwa Kaduna ya sauka? bai sauka, ashe ke nan akwai buƙatar a riƙa nazari sosai da kula da alƙaluman kafin a yanke hukunci," in ji shi.

Wannan ya sa muka zanta da wasu daga cikin waɗanda suka yi sayayya na azumin Ramadan domin jin yaya azumin na bana ya zo musu.

'Yadda azumin ya zo'

Hajiya Fatima daga jihar Legas ta ce kayayyaki sun ɗan sauka idan aka kwatanta da yadda farashin suke a baya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ka ga a baya buhun shinkafa yana kai naira dubua 80 zuwa 85, amma yanzu ana samu a naira dubu 60, na gida ana samu har a naira dubu 50. A baya na saya buhun wake naira dubu 90, amma yanzu ya koma har naira 60," in ji ta.

Ta ƙara da cewa sauran kayayyakin buƙata irin su albasa da tumatur da ire-irensu ma duk sun sauka.

"Maganar albasa da tattasai sai godiya ga Allah. Ka ga tumatur ma ya sauka sosai, a baya kwando ya kai har dubu 20, amma yanzu bai wuce naira dubu 3 ba," in ji ta a tattaunawarta da BBC.

A nasa ɓangaren, Malam Abubakar shi ma daga Legas ya ce farashin kayayyaki ya sauka sosai, amma daga zuwan azumi, wasu kayayyakin sun ɗan ƙara tsada a wasu kasuwannin.

"Kafin azumi ya zo, babban kwanon shinkafa ya sauka, har ya koma zuwa tsakanin naira 2,200 zuwa baira 2,100. Amma yanzu da azumi ya ƙarato, ya ɗan tashi," in ji shi a zantawarsa a BBC.

Sai dai ya ce ba shi da matsala da ɗan rashin da farashin kayayyakin ya yi, "matsalarmu rashin kuɗi."

A jihar Kaduna, Malam Ɗanjuma Muhammmad ya ce azumin bana ya zo masa ne a yanayi na babu yabo, babu fallasa.

"Kamar kullum sai dai godiya ga Allah. Mun yi sayayya daidai gwagwardo, Kayayyakin masarufi sun ɗan sauka idan aka kwatanta da azumin bara, amma sai dai babu kuɗi a hannun jama'a."

Ya ce akwai buƙatar gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wa mutane domin rage musu raɗaɗi.

A Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Hajiya Maryam Ibitoye ta ce wannan shekarar kayayyakin masarufi sun fi sauƙi da rahusa.

"Gaskiya zan iya bana abubuwa sun fi sauƙi, yazu haka ma ina da matsala, saboda na yi tunanin attarugu yana tsada kamar bara. Da yake aike na yi, sai aka kawo min attarugun kusan ninki uku na bara.

"Ko shinkafa ma an samu sauƙi. Na samu buhun shinkafa a naira dubu 53. Kin ga kuwa an samu rangwame matuƙa idan aka kwatanta da azumin bara," in ji ta a tattaunawarta a BBC.

A nata ɓangare, Aishatu Adamu a Abuja, ta ce ta shiga kasuwa, kuma babu abin da za ta ce sai dai godiya ga Allah.

"Kayan gwari da sauran kayan buƙata sun yi rahusa idan aka kwatanta da abin da aka samu a bara. bara magyaɗa kusan naira dubu 3, amma bana ya sauka sosai. Muna godiya ga Allah," in ji ta.