Manyan gyare-gyaren da aka yi wa dokar zaɓen Najeriya

Asalin hoton, X/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan ƙudurin dokar zaɓen ƙasar na 2026, wanda aka yi wa gyaran fuska.
Shugaban ya sa hannu kan dokar – wadda ta ƙunshi ƙa'idojin yin zaɓukan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomin yankin birnin tarayya - ne ranar Laraba a Abuja, gaban manyan jami'an gwamnati.
A lokacin sanya hannu kan dokar, Tinubu ya ce "babu batun siyasa a cikin wannan gyare-gyare. Abu ne na tsari. Ƙoƙari ne na cike giɓi da ƙarfafa tsari da kuma samar da tsaftatacciyar hanya ga masu tsarawa da kuma masu yin zaɓuka."
Shugaban na Najeriya ya sanya hannu kan dokar ne kwana ɗaya bayan hargitisn da aka samu a zaurukan majalisar tarayyar ƙasar game da amincewa da gyaran da aka yi wa dokar.
Dokar wadda majalisar dattijai da ta wakilai suka amince da ita a ranar Talata ta bayar da damar tura sakamako daga rumfunan zaɓe ta laturoni da kuma ta takarda kamar yadda aka saba, ta yin amfani da fom ɗin EC8A.
Amincewa da dokar na zuwa ne bayan doguwar muhawara game da shaɗara ta 60, wadda ke magana kan tsarin da za a bi wajen tura sakamako daga rumfar zaɓe zuwa ga rumbun tattara sakamakon zaɓen hukumar Inec, wato IRev.
A ranar Talata majalisar wakilai ta bi ra'ayin majalisar dattijai wajen amincewa da yin amfani da laturoni da kuma yin amfani da takardar da aka saba wajen tura sakamako.
Sashen ya bayar da dama ga jami'an hukumar Inec su yi amfani da takardar tura sakamako idan na laturoni ya gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Muhimman sauye-sauye da ke cikin dokar zaɓen
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Majalisar dattijan ta yi gyara ga shaɗara ta 28 ta dokar zaɓen, inda ta rage lokacin fitar da tsare-tsaren zaɓe daga kwana 360 zuwa 300.
Wannan ya bai wa hukumar zaɓen Najeriya damar tsara yin zaɓuka tsakanin watannin Disamban 2027 zuwa Janairun 2027.
Wani ɓangare na shaɗarar ta 28 da aka yi wa gyaran fuskar ta ce "Hukumar za ta wallafa tsare-tsaren yin zaɓe kwana 300 kafin ranar da za a gudanar da zaɓe a ƙarƙashin wannan doka, ta wallafa sanarwa na kowace jiha da kuma yankin Babban birnin tarayya".
Haka kuma majalisar dattawan ta gyara a sashe na 28 na kundin dokar zaɓe, inda ta rage wa'adi fitar da sanarwar zaɓen zuwa kwana 300, maimakon 360.
Wannan ya sa hukumar INEC ke da ƴancin saka ranar zaɓe a tsakanin watan Disamban 2026 zuwa Janairun 2027.
Wurin da aka gyara ya koma, "INEC za ta ayyana sanarwar lokacin zaɓe a jihohi da babban birnin tarayya Abuja a kwanakin ba su yi ƙasa da kwana 300 ba."
Haka kuma ƴan majalisar sun amince da gyaran ne bayan shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ya ce bayan nazarin dokokin, wa'adin kwana 360 da yake cikin sashe na 28 zai sa dole a gudanar da zaɓen a cikin azumin baɗi, wanda a cewarsa hakan ya kamata a yi gyara.
Ya ce gudanar da zaɓe a lokacin Ramadan zai iya shafar zaɓen, domin mutane da dama ba za su samu karsashin zuwa zaɓen ba.
Haka kuma ƙudurin ya buƙaci a yi nazari ɓangarori iri su 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93, da 143.
Haka kuma majalisar ta rage wa'adin miƙa sunayen ƴan takara zuwa kwana 120 maimakon kwana 180.
Sannan dole Inec ta fitar da sunayen ƴan takara da ta tantance a cikin aƙalla kwana 60 kafin zaɓe maimakon kwana 150 da yake a baya.

Asalin hoton, X/Bola Tinubu
Haka kuma an ɓarje-gumi kan lokacin gudanar da zaɓen, musamman inda Sanata Opeyemi ya buƙaci a dakatar da amince da gyare-gyaren da aka yi, a koma kwamiti a sake dubawa.
Ya ce lokacin da INEC ta sanar domin gudanar da zaɓen na watan Fabrairun 2026 ya samu suka daga wasu masu ruwa da tsaki, inda ya ce ya saɓa da wa'adin aƙalla kwana 360 kafin ƙarewar wa'adin waɗanda suke mulki.
Sanatan mai wakiltar Ekiti ta Tsakiya ya ce wa'adin na aƙalla kwana 360 wanda yake ƙunshe a sashe na 28, zai iya tilastawa a gudanar da zaɓen mai zuwa a cikin Ramadan.
Haka kuma ƴan majalisar sun gano wasu saɓani a wasu wurare da dama na kundin, ciki har da sashe na 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93, da 143.
Rikita-tikita a majalisar wakilai
Tun da farko, an samu rikita-rikita a ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, bayan ƴan majalisa sun nuna rashin amincewa da wasu ɓangarorin dokar zaɓen.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan dokoki da tsare-tsare, Francis Waive ne ya gabatar da ƙudurin buƙatar majalisar ta janye matsayarta ta farko kan yanayin aiksa sakamakon zaɓen domin amincewa da tsarin da majalisar dattawa ta amince da shi.
Da shugaban majalisar Tajudeen Abbas ya buƙaci a gudanar da ƙuri'ar murya, sai muryar nuna rashin amincewa ta fi ƙarfi, amma shi sai ya ce ta masu amincewar ce ta amo.
Hakan ya sa wasu ƴan majalisar suka nuna rashin amincewa.
Ƴan majalisar sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu har suka fito harabar majalisar suna bayyana rashin jin daɗinsu.
Sun bayyana buƙatarsu ta lallai sai an tabbatar da aika sakamakon zaɓen kai-tsaye ta intanet daga akwatunan zaɓe zuwa shafin intanet na IREV na hukumar INEC.
An ji lokacin da masu zanga-zangar suke ta ihuce-ihucen cewa, "ba za mu amince ba, Akpabio ka amince da buƙatarmu," kamar yadda suka bayyana.
Wasu kuma cewa suka riƙa yi, "dole a yi amfani da ƙuri'armu."
Ita dai tun da farko, majalisar dattawa ta amince a riƙa aika sakamakon zaɓen ne kai-tsaye ta intanet, amma a wuraren da babu intanet ta amince a yi amfani da takardu a rubuta sakamakon.
Amma ita majalisar wakilai sai ta nace cewa dole a tabbatar da an aika sakamakon ta intanet ne kawai kai-tsaye, lamarin da ƙungiyoyi masu sa ido suka bayyana da wani matakin da zai rage maguɗi.
Matsayar guda biyu mabambanta sun haifar da ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa domin gudanar da gyare-gyare.
A lokacin ne Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya kafa kwamitin mutum 12 domin zama da ƴan majalisar wakilai domin haɗa rahotannin majalisun biyu wuri ɗaya.
Yanzu dai an amince da cewa za a riƙa aika sakamakon zaɓen ne kai-tsaye daga akwatin ɗaya ta intanet, amma a wuraren da babu intanet mai kyau, za a iya amfani da takardar EC8A domin rubuta sakamakon zaɓen, sannan baturen zaɓe da wakilan jam'iyya ko ƴan takara suka sa hannu.







