Yadda ake kaffara da ramuwar azumi

Wata mace tana addu'a kusa da wani masallaci

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

A matsayinsa na farilla ga musulmi, azumin Ramadana, kamar yadda adinin Musulunci ya tanadar akwai hanyoyi biyu na rama azumin da ya kuɓuce bisa dalilai daban-daban.

Addinin ya tanadi hanyoyi guda biyu, kaffara da ramako domin rama azumin da ya kuɓuce wa musulmi.

Kaffara da ramuwar azumi abubuwa ne guda biyu da addini ya tanadar ga waɗanda wasu dalilai suka sanya ba su yi azumi ba ko kuma azumin nasu ya karye bisa wasu dalilai.

Mece ce kaffarar azumi

Sheikh Abu Qatada Muhammad ɗaya daga cikin limaman masallacin Juma'a na Usman bin Affa da ke Gadon Qaya a birnin Kano, ya ce Kalmar kaffara na nufin wata ibada da Allah ke wanke bayinsa daga wani zunubi da suka aikata.

''Kaffara na nufin wanke zunubi ko laifi, wato ka aikata laifi kaza, to ka yi kaza sai ka wanke kanka daga laifin da ka yi,'' in ji malamin.

Akwai abubuwan da haifar da kaffara a lokacin azumin watan Ramadan, kamar yadda malamin ya yi bayani.

  • Cin abinci ko abin sha da gangan a lokacin da azumi ke bakin mutum
  • Kusantar iyali da gangan kuma da rana
  • Ƙaƙaro amai da gangan
  • Wasa da al'aura domin biya wa kai buƙata da gangan
  • Tsoho ko tsohuwar ba za su iya yin azumin watan Ramadan.
  • Mai shayarwar da ta ajiye azumi.
Wasu mata suna shan ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Yadda ake kaffarar azumi

Malamai sun yi bayanin cewa yadda ake yin kaffara ya dangatan ga dalilin da ya janyo wa mutum kaffarar.

Ƴanta baiwa: Sheikh Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin Juma'a da ke garin Okene ya cega wanda ya sadu da iyalainsa da rana cikin watan Ramadan, kaffarsa shi ne ''ƴanta baiwa, idan hakan bai samu ba to sai ya yi azumin wata biyu, in hakan ma bai samu ba to sai ya ciyar da miski 60, kamar yadda ya zo a hadisi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Azumin wata biyu: A cewar Sheikh Abu Qatada Muhammad duk mutumin da ya ci ko ya sha da gangan da rana cikin wata Ramadan, ko kuma ya ƙaƙaro amai da gangan a lokacin da yake azumi.

''Zai yi azumin wata biyu ko kwana 60 a ajere ba tare da tsallake ko da kwana guda ba, domin wanke kansa daga laifin da ya aikata'', in ji limamin Juma'ar.

Ciyarwa: Abu Qatada Muhammad ya ce wani nau'in kaffarar shi ne ciyarwa maimakon ramako.

''Wannan ya shafi tsoho ko tsohuwa ko kuma majinyacin da ya yanke ƙauna daga warkewa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa abin da rukunin waɗannan mutane za su yi na kaffara shi ne su ciyar da mutum guda a kocewa rana da ya kasance ba su yi azumin ba.

''Za su iya ciyarwa da abinci dafaffe, ko ɗanye, kuma sau ɗaya za su ciyar da miskini guda a akocewa rana a madadin azumin wannan ranar da ba su yi ba'', a in ji shi.

Ciyarwa da azumi: Malamin ya ce ga mace mai ciki ko mai shayarwa da ta ajiye azumi, kuma ganganci ya sa ba ta rama ba, har wani Ramadan din ya zagayo, to bayan wucewarsa idan zai rama shi, duk guda da ya yi sai ya ciyar da miskini, kamar yadda malamin ya yi ƙarin haske.

Me ke janyo ramuwar azumi?

Wasu mutane suna cin abinci

Asalin hoton, Getty Images

Ramuwa ko ramako kamar yadda limamin Juma'ar ya yi bayani shi ne rama azumi guda da wani dalili ya janyo karyewarsa.

Ya bayyana wasu abubuwa ko uzurorin da ke janyowa mai azumi ramako, kamar haka:

Rashi lafiya: Wannan nassi ne ƙarara ya zo da shi daga al'qur'ani mai girma cewa duk mutumin da ba shi da lafiya to ya ajiye azumi daga baya ya rama shi, a cewar malamin.

Tafiya: Kamar yadda nassi ya ambaci rashin lafiya, haka nan ya ambaci tafiya, kamar yadda malamain ya bayyana.

Duk mutumin da yake da uzurin tafiya halastacciya to musulunci ysa ba shi damar ajiye azumi kuma daga baya sai ya rama adadin ranakun da ya sha azumin a lokacin tafiyar.

Zuwan jinin al'ada: Ga mata masu al'ada su ma musulunci ya yarje musu su ajiye azumi a duk lokacin da jinin ya zo musu, da kuma tsawon kwanakin da za su ɗauka suna jinin.

''Daga baya kuma sai su rama adadin kwanakin da suka sha azumin bayan sallah'', kamar yadda ya yi bayani

Mace mai ciki: Ita ma mace mai ciki wasu malaman suna bayar da fatawar ta ajiye azumi idan cikin yan ba ta wahala, daga baya sai ta rama, kamar yadda ya yi bayani.

Yadda ake rama azumi

Yadda ake yin ramuwar azumin da ya kuɓucewa mai azumi shi ne, ama adadin kwana kin da ka sha azumin.

Malamin ya ce a nan iya kwanakin da kaɗai ka sha azumin za ka rama, ba tare da ƙari ko ciyarwa ba.

''Kamar yadda nassin alƙur'ani ya bayyana cewa ku rama iya kwanakin da kuka sha azumin'', a cewa malamin.