KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga 1 zuwa 7 ga watan Maris 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. An hana Adama Traore ɗaga ƙarfe a West Ham

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin West Ham Nuno Espirito Santo ya dakatar da Adama Traore daga ɗaga ƙarfe a dakin motsa jiki da ke filin atisayen kulob ɗin.

    Nuno ya bayyana ƙirar ɗan wasan gefen a matsayin "abin mamaki", amma ya gargaɗi Traore mai shekara 30 cewa ya riga ya yi nauyi dayawa.

    A baya ɗan ƙasar Sifaniyan ya yi ikirarin cewa ba ya ɗaga ƙarfe, amma abokin wasansa Crysencio Summerville ya wallafa wani bidiyo a shafinsa sada zumunta da ke nuna Traore yana danna ƙarfe mai nauyin 145kg a filin atisayen kungiyar da ke Rush Green a makon jiya.

    "Na gaya masa ya ɗan ƙauracewa ɗakin motsa jiki, yana ɗaya daga cikin abubuwan da nake ganin ya kamata ya gane. Nauyin da yake ɗauka ya isa haka.'' In ji Nuno

    Traore ya buga wa Fulham wasanni 20 a dukkan gasanni a kakar wasa ta bana kafin ya koma West Ham a watan Janairu kan yarjejeniyar da ta kai fam miliyan biyu.

  2. Flamengo ta sallami Filipe Luiz a matsayin kocinta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An kori tsohon ɗan wasan baya na Chelsea Filipe Luis a matsayin kocin Flamengo sa'o'i kaɗan bayan da ƙungiyar ta Brazil ta samu nasara da ci 8-0 a wasan kusa da na ƙarshe na Campeonato Carioca a ƙarshen mako.

    Luis, mai shekaru 40, ya jagoranci Flamengo ta lashe kofuna bakwai a cikin wasanni 100 da ya yi tun bayan maye gurbin tsohon kocin Brazil Tite a watan Satumban 2024.

    Flamengo ta yi rashin nasara a gasannin 2026, inda ta zama ta biyu a Supercopa do Brasil da Recopa Sudamericana a watan jiya.

    Amma, bayan kammala nasara da jimillar ci 11-0 a kan Madureira bayan nasarar da ta yi a daren ranar Litinin da ci 8-0 a wasansu na biyu, za ta samu damar lashe kofin Carioca karo na uku a jere inda za ta kara da Fluminense a wasan ƙarshe na ranar Lahadi mai zuwa.

    Sai dai Luis ba zai jagoranci ƙungiyar a wannan wasan ba bayan da ta fitar da wata ƴar gajeriyar sanarwa da ke bayyana korar shi.

    Daga cikin nasarorin da ya samu Luis, wanda ya lashe gasar Premier da Chelsea a ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho a 2015, ya jagoranci Flamengo zuwa lashe gasar Copa Libertadores a 2025.

    Flamengo ta kuma kai zagayen ƙungiyoyi 16 na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na bara, inda ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 4-2.

  3. Real Madrid ta sake yin tuntuɓe a La Liga

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta rasa damar rage tazarar da ke tsakaninta da Barcelona a saman teburin la Liga zuwa maki ɗaya bayan da ta sha kashi a hannu Getafe da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasan Bernabeau.

    Martin Satrianone ya zura Getafe ƙwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci kiuma Madrid ta klasa farkewa har aka tashi wasa.

    Wanna sakamakon dai na nufin Madrid ta yi rashin nasara a gasar sau biyu ke nan ka jere bayan da ta sha kashi a hannun Osasuna da ci 2-1.

    Yanzu dai Kocin Madrid Alvaro Arbeloa ya yi rashin nasara sau huɗu cikin wasanni 12 da ya yi.

    Madrid za ta kara da Celta Vigo ranar Juma'a yayin da take ƙoƙarin kaucewa shan kashi na uku a jere a gasar.

  4. Ya kamata mu rage yawan katin da muke samu - Rosenior

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Chelsea Liam Rosenior ya koka kan yadda ƴanwasansa ke karɓar kati da kuma yanayin kwallayen da ake zura mata a raga a wasanninta na baya bayan nan.

    Kungiyar Rosenior ta sake samun wani jan kati a wasan da suka sha kashi a hannun Arsenal da ci 2-1 inda aka danna wa Pedro Neto katin gargadi biyu.

    Hakan na nufin Chelsea ta samu jan kati bakwai a gasar Premier bana kaɗai, tana kuma da guda tara a duk gasa a kakar wasan bana.Na tam

    "Ina tsammanin, a matsayin mu na kungiya, kuma da ni a matsayin jagora, dole ne mu dauki alhakin wasu abubuwan da muka yi a cikin wasa, musamman kan abubuwan da suka shafi ladabi a fagen wasa." in ji Rosenior bayan da suka sha kashi a hannun Arsenal.

    Ya ƙara da cewa "Abu ne da na yi tunanin mun magance. Mun yi wasanni 10 ba tare da jan kati ba, yanzu [mun samu] biyu a wasanni biyu kuma wannan matsala ce da ya kamata mu magance cikin gaggawa."

    Chelsea za ta buga wasanta na gaba a gasar Premier a ranar Laraba mai zuwa inda za ta fafata da Aston Villa a filin wasan Villa Park.

  5. Teburin gasar Premier bayan wasannin mako na 28

    Yadda teburin gasar Premier ya kasance bayan wasannin mako na 28.

    ...

    Asalin hoton, Premier League/FB

  6. Messi ya zura ƙwallo biyu a wasan Miami da Orlando a gasar MLS

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi ne ya zura ƙwallaye biyu a wasan da Inter Miami ta doke Orlando City da ci 4-2 a fafatawar da suka yi a Florida.

    Zakarun da ke riƙe da kofin, wadanda suka yi rashin nasara a wasansu na farko a kakar wasa ta bana da Los Angeles FC a watan da ya gabata, sun kusa sake shan kaye lokacin da Marco Pasalic da Martin Ojeda suka ci wa Orlando ƙwallo biyu cikin mintuna 25.

    Amma bayan da ɗan wasan tsakiya Mateo Silvetti ya jefa ƙwallo bayan an dawo hutun rabin lokaci ya bai wa Miami fatan cewa za su iya taɓuka abin kirki,

    Gwarzon ɗan wasan Argentina ya mai shekaru 38 ya zura ƙwallonsa ta farko a kakar wasa ta bana inda ya jefa ƙwallo a minti na 57

    Messi ya tabbatar da nasarar ƙungiyarsa a 90 jefa ƙwallonsa na biyu daga bugun tazara.

    Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau takwas a yanzu ya zura ƙwallaye 898 wa ƙungiyoyi da kuma ƙasarsa, ciki har da 79 a wasanni 90 da ya buga wa Miami.

    Nasarar ita ce ta farko da Miami ta yi a cikin ziyara tara zuwa Orlando, kuma yanzu za su fuskanci wasa a gidan DC United ranar Asabar.

  7. Arsenal ta ci gaba da riƙe wuta a saman teburin Premier

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ci gaba da zama kan teburin gasar Premier a Ingila bayan ta lashe wasanta da Chelsea da ci 2-1.An dai ci duka ƙwallayen ne ta hanyar bugun ƙusurwa.

    Duk da cewa Arsenal ba ta buga ƙwallo mai ƙayatarwa ba a wasan, to amma nasarar da ƴanwasanta suka yi na zura ƙwallo biyu ta sanya ƙungiyar ta ci gaba da zama ɗare-ɗare kan teburi da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City wadda ke a matsayi na biyu.

    A yanzu Arsenal ta ci ƙwallaye 16 ke nan ta hanyar ko dai bugun tazara ko na ƙusurwa a wannan kaka, inda ta fi kowace ƙungiya ta wannan fanni a kakar.

    A wasan na ranar Lahadi, mai tsaron baya William Sliba ne ya jefa ƙwallon farko ta hanyar kara wa ƙwallon kai bayan bugun ƙusurwa da Bukayo Saka ya ɗauko.

    Sai dai gab da zuwa hutun rabin lokaci Chelsea ta rama ta hanyar bugun ƙusurwa, inda Piero Hincapié ya ci gida, ya kara wa ƙwallon kai ta faɗa ragar Arsenal.

    Can bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Jurrien Timber ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Chelsea bayan bugun kusurwa da Declan Rice ya ɗauko.