Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 12/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 12 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Hana Iran mallakar nukiliya ya fi saita farashin fetur muhimmanci - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya ce hana Iran mallakar makamin nukiliya ya fi muhimmanci a kan saita farashin man fetur a yanzu.

    Ya ce a matsayin Amurka ta ƙasar da ta fi samar da man fetur, ita ma tana samun riba sosai idan farashin ya tashi.

    Tun bayan da yaƙin ya ɓarke, farashin gangar ɗanyen mai ya tashi daga dala 73 zuwa kusan dala 100.

    A farkon wannan makon, hedkwatar tsaron Amurka ta bayyana wa majalisar ƙasar cewa kwana shida na farkon yaƙin Iran ya laƙume sama da dala biliyan 11.

  2. 'Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙa 20 a Yobe'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya sun ce sun kashe aƙalla mayaƙan masu iƙirarin jihadi 20 a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan da suka daƙile wasu hare-hare da aka kai kan sansanonin soji a farkon makon nan.

    Mayaƙan Boko Haram da kuma Iswap sun ƙara tsananta hare-haren da suke kai wa sojoji da fararen hula, yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalar tsaron da ta shafe kusan shekaru 16.

    Rahotanni sun ce jerin hare-haren da mayaƙan suka kai a ranar Litinin sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 14, ciki har da sojoji 10 a jihohin Borno da Yobe, kamar yadda majiyoyin farar hula da na soji suka bayyana.

    Mai magana da yawun rundunar soji a yankin, Sani Uba, ya ce a cikin wata sanarwa da aka rubuta ranar Laraba kuma aka fitar ranar Alhamis cewa sojoji sun daƙile “hare-haren da aka tsara tare” da mayaƙan ISWAP wanda suka kai kan sansanin soji a Goniri da ke jihar Yobe daga daren Litinin zuwa safiyar Talata.

    Ya ce “an kashe sama da mayaƙan masu tayar da ƙayar baya 20, ciki har da wani babban kwamandan su mai suna Abu Yusu, wanda aka bayyana a matsayin Munzir na Dursula.”

    Uba ya ƙara da cewa wasu sojoji sun samu raunuka, amma bai bayyana adadinsu ba.

    Wani mazaunin ƙauyen Katarko da ke kusa da wurin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a farkon makon da ya gabata cewa mayaƙan sun kashe sojoji huɗu sannan suka ƙona gine-gine da motocin soji a Goniri.

    Matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 tare da raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

    A makon da ya gabata kuma, mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji bakwai da fararen hula 11 lokacin da suka kai hari kan sansanin soji sannan suka afkawa garin Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza da ke kusa da iyakar Kamaru, inda suka harbe wasu mazauna tare da yin garkuwa da wasu.

    A watan Fabrairu ne Amurka ta fara tura sojojinta zuwa Najeriya domin ba da tallafin fasaha da horo ga sojojin ƙasar wajen yaƙar ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

  3. Ba na wasa da albashin ma'aikata tun da na zama gwamna - Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin biyan ma'aikatan jihar albashinsu na watan Maris domin samun sukunin yin "bikin ƙaramar sallah cikin sauƙi", inda ya ce ba ya wasa da jin dadin ma'aikatan jihar.

    Gwamnan ya bayar da umarnin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktan yaɗa labaransa Abubakar Bawa, a yau Talata.

    Sanarwar ta ce "tun bayan zuwan wannan gwamnati take tabbatar da cewa an biya ma'aikata albashi a kan kari".

    Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya biya bashin kuɗaɗen giratuti da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.

    Gwamna ya buƙaci ma'aikatan jihar da su saka wa gwamnatin jihar ta hanyar mayar da hankali wajen aiki.

  4. Sojojin ruwan Amurka 'ba su shirya' raka jiragen dakon mai ba ta mashigar Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren kula da fannin makamashi na Amurka chris Wright ya ce sojojin ruwan Amurka ba su shirya yi wa jiragen dakon mai rakiya ba ta mashigar Hormuz, a yayin da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ke ci gaba da kawo cikas ga samar da mai a duniya.

    A gefe guda kuma, an kai wa ƙarin wasu jiragen dakon mai 3 hari a yankin Gulf, yayin da ake ci gaba da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

    Mutum ɗaya ya mutu a cikin wani jirgin ruwa mallakar Amurka a gabar tekun Iraki, wanda aka ruwaito cewa wani jirgin ruwa mara matuki dauke da abubuwan fashewa ne ya auka masa.

    An kuma kai hari kan wani jirgin ruwan dakon man da ke kan hanyar zuwa tashar jirgin ruwa na Iraki.

    Jirgin ruwa na uku wanda na China ne, wani makami mai linzami ne ya kai masa hari kusa da mashigar Hormuz.

    Iran na ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami kan makwabtanta da suka hada da Bahrain, Oman, Dubai da Qatar.

  5. Iran za ta ɗauki fansar mutanenta da aka kashe - Mojtaba Khamenei

    ....

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce Iran za ta ɗauki fansar mutanenta da aka kashe, ciki har da yara da ɗaliban makarantar Minab.

    Ya bayyana hakan ne a sanarwarsa ta farko da ya fitar tun bayan da aka naɗa shi a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar wanda gidan talabijin gwamnatin ƙasar ta karanto.

    "Dole ne mu nemi adalci ga mutanen Iran da suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai, za mu ɗauki fansa, ba za mu manta da jinin waɗanda aka kashe ba," in ji sanarwar.

    Sabon jagoran ya kuma nemi a rufe sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

    Ya kuma jaddada cewa Iran za ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz, yana mai cewa wannan mataki na daga cikin hanyoyin da ƙasar za ta bi wajen kare muradunta.

    A ranar Litinin ne aka ayyana Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran addinin Iran na uku inda hukumomi da cibiyoyi daban-daban na gwamnatin Iran, ciki har da gwamnati da ɓangaren shari’a da na tsaro da kuma soji, suka bayyana goyon bayansu ga sabon jagoran tare da yin mubaya’a gare shi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke yawo a kafafen yaɗa labarai game da lafiyar sabon jagoran.

  6. Rasha ta yi kira ga Amurka da Isra’ila su daina kai wa Iran hari

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta yi kira ga Isra’ila da Amurka da su daina kai hare-hare kan Iran inda ta ce ya kamata su koma teburin tattaunawa don warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ce yanayin jin kai a yankin yana cikin mawuyacin hali, kuma ƙara tashin hankali a yaƙin na daga cikin abubuwan da ke haifar da damuwa mai tsanani.

    “Rasha za ta ci gaba da yin duk abin da take iya yi don kawo ƙarshen rikici a Gabas ta Tsakiya,” in ji ta.

    Haka kuma, mai magana da yawun ma’aikatar ta kara da cewa: “Bisa ga rahotannin hukuma, adadin wadanda hare-haren ya shafa a Iran na da yawa.”

  7. 'Amurka ta yi asarar dala biliyan 11.3 a satin farko na yaƙi da Iran'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin sojin Amurka sun shaida wa Majalisar Dokokin ƙasar cewa Amurka ta yi asarar dala biliyan 11.3 a satin farko na yaƙi da Iran kamar yadda labaran CBS suka ruwaito.

    Rahoton ya nuna cewa wannan adadin bai haɗa da kuɗaɗen shirye-shiryen kwashe kayan aikin soja kafin harin farko da aka kai a ranar 28 ga Fabrairu ba.

    Sanatan Democrat, Chris Coons, ya bayyana wa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa: "Ina tsammanin adadin gabaɗaya zai fi haka sosai."

  8. Iran ta ƙaddamar da sabbin jerin hare-hare kan Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sashen hulɗa da jama’a na Rundunar Juyin Juya Halin Iran ya sanar da cewa sun kai sabbin jerin hare‑hare kan wurare a Isra’ila.

    Rundunar ta bayyana cewa wannan shi ne “jerin hare‑hare na 41” da ta kai kan “Tel Aviv da Al-Quds da aka mamaye” da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da dama.

  9. Babu wata barazana daga wani ɗan siyasa dake a ƙarƙashi na - Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa a ƙarƙashinsa da zai iya zama barazana ga dimokuraɗiyya ko dokar ƙasa.

    Tinubu ya faɗi hakan ne a wani taron buɗe-baki da shugabannin jamʼiyyun siyasa a Fadar shugaban ƙasa.

    Ya ce, “Ni dan ga-ni-kashe-nin dimokuradiyya ne. Masu rinjaye za su samu abin da suke so, marasa rinjaye ma za su samu abin da suke so, siyasa ta fi daɗi idan kai ne ke samun nasara.”

    Shugaban ya nanata cewa dokar ƙasa da dimokuraɗiyya za su ci gaba da zama ginshiƙai masu ƙarfi a mulkinsa.

    Tinubu ya kuma jaddada cewa ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin jamʼiyyu abu ne mai muhimmanci domin gina tsarin zabe da cibiyoyi masu gaskiya.

    Shugaban kuma bayyana cewa dole ne dokar ƙasa ta yi mulki a kowace dimokuraɗiyya inda ya tabbatar wa shugabannin jam’iyyu cewa za a gudanar da zabuƙa cikin gaskiya a ƙarƙashin mulkinsa

  10. Mutum 64 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa a kudancin Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga hukumomin yankin kudancin Habasha sun bayyana cewa ambaliyar ruwa dazaftarewar ƙasa sakamakon ruwan sama mai ƙarfi sun kashe mutum 64, yayin da ba a san inda mutum 95 suke ba.

    Shugaban ƴansanda a yankin Gamo, Abraham Buha, ya bayyana cewa an samu mutuwar mutanen ne a ƙananan hukumomin Kamba, Gacho Baba, da Bonke na Gamo.

    A baya dai, gwamnatin Gamo ta bayyana cewa mutum 52 ne kawai suka mutu a yankin Mazo Deysa na ƙaramar hukumar Gacho Baba.

    Jami’an gwamnatin tarayya da na yankin sun kai ziyara ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, yayin da ayyukan ceto da bincike ke ci gaba.

  11. Iran ta kai sabbin hare-hare a Isra'ila da Iraq da Bahrain da Oman

    ...

    Rahotanni na cewa hare-haren da Iran ta kai sun shafi wasu wurare a Isra'ila da Iraq da Bahrain da Oman, lamarin da ya haddasa gobara da kuma tsaikon ayyukan man fetur a wasu sassan yankin.

    A kudancin Iraq kusa da tashar jiragen ruwa ta Basra, wasu tankokin dakon mai biyu sun kama da wuta, abin da ya tilasta dakatar da aiki a tashoshin man fetur na ƙasar.

    Rahotanni sun ce an ceto mafi yawan ma’aikatan jiragen, sai dai mutum ɗaya ya mutu.

    A Bahrain kuma, gobara mai ƙarfi ta tashi bayan an kai hari kan tankunan adana man fetur da ke kusa da filin jirgin saman ƙasa da ƙasa.

    Hukumomi sun ce hayaƙin da ke tashi yana da yawa matuƙa, don haka suka buƙaci mutane su rufe tagogin gidajensu.

    A Oman kuwa, jami’an kashe gobara na ci gaba da ƙoƙarin shawo kan wata gobara da ta tashi a tankunan ajiyar mai bayan harin da aka kai jiya a tashar jiragen ruwa ta Salalah.

    Bugu da ƙari, gwamnatin ƙasar ta ba da umarnin fitar da jiragen ruwa daga tashar fitar da man fetur a matsayin matakin kariya.

    Rahotanni na nuna cewa Tehran na ƙoƙarin jefa yankin cikin matsin tattalin arziki na dogon lokaci.

    Rundunar juyin juya halin Iran ta kuma yi gargaɗin cewa za ta fara kai hari kan bankunan Amurka da na Isra'ila da ke yankin Gabas ta Tsakiya bayan wani hari da aka kai kan wani banki a Iran.

    A halin da ake ciki, wasu manyan bankunan ƙasa da ƙasa sun rufe ofisoshinsu a yankin Gulf.

    Daga cikinsu akwai HSBC a Qatar, da kuma Citigroup da Standard Chartered a Dubai, inda suka umarci ma’aikatansu su zauna a gidajensu.

  12. Bankuna sun fara rufe ofisoshinsu a UAE saboda barazanar Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Bankin Citi ya bayyana cewa za ta rufe dukkan ofisoshinta a Hadaddiyar Daular Larabawa sai ɗaya kawai ne zai zama a buɗe bayan Iran ta yi barazanar kai hari kan bankuna a yankin.

    Bankin ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo ne “sakamakon yanayin da ke canzawa a ƙasar,” ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ta ruwaito cewa Bankin ya umurci ma’aikatanta su bar ofisoshinsu su sanna su yi aiki daga gida har sai an ba da ƙarin umarni.

    Reuters ya ƙara da cewa bankin Standard Chartered ma ya fara fitar da ma’aikatansa daga ofisoshin su na Dubai.

    Wadannan matakai sun biyo bayan wani jawabi daga kakakin rundunar Khatam al-Anbiya na Tehran, inda aka ce Iran za ta kai hari kan harkokin tattalin arziki da bankuna da suka shafi Amurka da Isra’ila a yankin, bayan harin da aka kai wani bankin Iran.

    Hakazalika, bankin HSBC ya sanar a wata sanarwa ta daban cewa ya rufe dukkan ofisoshinsa a Qatar har sai an ba da ƙarin umarni.

  13. Isra’ila ta ce ta kai 'gagarumin jerin hare‑hare' kan Iran

    Sojojin Isra’ila sun sanar cewa sun kaddamar da “gagarumar jerin hare‑hare” a faɗin Iran inda suka nufi ginin gwamnati da wasu muhimman cibiyoyi.

    A cewar rundunar, sojojin sun kai harin ne da jiragen yaƙi da makamai kan gine-ginen da ya danganci Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran da sauran gine‑ginen soja a cikin Tehran da wasu sassa na ƙasar.

    Wannan ya biyo bayan kwanaki na tashin hankali tsakanin Isra’ila da Iran, inda suka kai wa junansu hare-hare.

  14. An kai hari da jirage marasa matuƙa kan filin jirgin saman Kuwait

    Hukumar kula da ayyukan jiragen sama ta Kuwait ta ce an kai hari da jirage marasa matuƙa a filin jirgin saman ƙasar kamar yadda gidan jaridar ƙasa ta ruwaito.

    A wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta ta X, an bayyana cewa harin ya haifar da lalacewar kayan aiki amma babu wanda ya jikkata.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta a Yankin Gabas ta Tsakiya ayin da Iran da Isra'la da Amurka ke ci gaba da kai wa junansu hari.

  15. Thailand ta gayyaci jakadan Iran kan harin jirgin ruwa a mashigin Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Thailand ta gayyaci jakadan Iran da ke Bangkok domin ya yi bayani kan abin da ta kira “gaskiyar” harin da aka kai wa wani jirgin ruwan dakon kaya mai ɗauke da tutar Thailand kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Rahotannin sun ce gwamnatin Thailand ta buƙaci jakadan ya yi bayani kan harin da aka kai jiya kan jirgin Mayuri Nari, wanda ke wucewa ta mashigin Hormuz.

    Kamfanin da ke tafiyar da jirgin ya bayyana cewa har yanzu ma’aikata uku na jirgin ba a gansu ba, kuma ana zargin sun maƙale a cikin ɗakin inji na jirgin.

    A jiya ne wani jirgin dakon kaya mai ɗauke da tutar Thailand ya fuskanci hari yayin da yake wucewa ta mashigin Hormuz

    Rundunar sojin ruwan Thailand ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ma’aikatan jirgin ‘yan Thailand guda 23 ne ke cikinsa a lokacin da lamarin ya faru.

  16. Adadin mutanen da suka jikkata a hare-haren Iran kan Isra'ila sun kusa 3,000

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar lafiyar Isra'ila ta ce adadin mutanen da suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa ƙasar ya kai 2,745.

    Ma’aikatar ta ce mutane 179 ne suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya ƙara yawan waɗanda suka jikkata tun bayan fara yaƙin da Sra;ila da Amurka ke yi da Iran.

    Daga cikin waɗanda suka jikkata, wasu na ci gaba da karɓar magani a asibitoci.

    Rahotanni sun ce har yanzu mutane da dama na kwance a asibiti domin kula da lafiyarsu.

    Rikicin tsakanin Iran da Isra’ila ya ƙara tsananta a cikin kwanakin nan, inda ɓangarorin biyu ke ci gaba da kai hare-hare a tsakanin junan lamarin da ke ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali.

  17. Tambuwal ya koma jam’iyyar ADC bayan ficewa daga PDP

    ....

    Asalin hoton, Tambuwal/X

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanatan da ke wakiltar mazaɓar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa ta Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC bayan ficewar daga Jam'iyyar PDP.

    Tsohon gwamnan ya sanar da sauya sheƙr nasa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce matakin da ya ɗauka na komawa ADC ya samo asali ne daga ra’ayinsa cewa Najeriya na buƙatar wani ƙarfi na siyasa da ya ginu kan gaskiya da haɗin kai da riƙon amana da kuma jajircewa wajen bunƙasa ƙasar.

    Ya kuma sake jaddada ƙudurinsa na ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da tsayawa kan manufofin dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa.

    Tun da farko dai Tambuwal ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da saɓanin shugabanci da kuma rabuwar kai da ke ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar.

    A cewarsa,"rikice-rikicen da ke addabar jam'iyyar PDP sun raunana haɗin kai da alƙiblar da a baya suka kasance ginshiƙan jam’iyyar.

  18. MDD ta yi allawadai da hare-haren Iran kan ƙasashen Larabawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani ƙuduri da ke yin Allawadai da hare-haren da Iran ke kai wa ƙasashen Larabawa na yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Jordan.

    Ƙudurin wanda ƙasashen yankin suka gabatar, bai ambaci hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran din ba.

    Har ila yau, ƙudurin ya yi allwadai da matakin Tehran na rufe mashigin Hormuz.

    Ƙasashen China da Russia sun ɗare kujerar naki.

    Sai dai amincewa da ƙudurin ya sha ban-ban da aiwatar da shi, don haka duk wanda ya ce zai sa ran Iran za ta aiwatar da shi, wato ta daina kai hare haren da take kaiwa, to kuwa zai tsaya jiran gawon shanu ne kawai.

    A gefe guda wani kuduri da Rasha ta gabatar na neman yin Allah wadai da dukkan hare hare, ciki har da na Amurka da Isra'ila kan Iran, bai samu isashshen goyon baya ba, don haka ba a amince da shi ba.

  19. 'Ko an kashe wani akwai wani': Yadda Iran ta gina tsarin shugabacinta

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sama da shekaru 40 kenan da aka kafa gwamnatin jamhuriyar musulunci a Iran bayan juyin juya halin shekarar 1979.

    Iran na cikin wani yanayi da ta jima ba ta ga irinshi ba.

    Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai ya kashe jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan kwamandojin soji tare da lalata wasu muhimman wurare.

    Amurka da Isra'ila sun bayyana cewa suna fatan ganin an samu sauyin gwamnati a Iran, inda suke kira ga 'yan ƙasar su kifar da ita.

    Sai dai masana sun ce Iran ta kasa wani tsarin gwamnati wanda zai yi wuya a iya kifar da shi.

    Shin me ya bambanta tsarin da Iran ta kafa da sauran ƙasashen Gabas ta Tsakiya?

  20. Iran na ci gaba da kai hari kan jiragen dakon man fetur a mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran na ci gaba da kai hari kan jiragen ruwan dakon man fetur a Mashigin Hormuz, lamarin da ya ƙara tayar da fargabar tangarɗa ga zirga-zirgar man fetur a duniya.

    Wannan mataki na Tehran ya sa farashin ɗanyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga, sakamakon damuwar da ake da ita kan yiwuwar samun matsala wajen samar da mai, a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran.

    Farashin hannayen jari a wasu kasuwannin Asiya ma ya faɗi ƙasa warwas.

    Hauhawar farashin man na zuwa ne duk da sanarwar da hukumar makamashi ta duniya International Energy Agency ta bayar jiya Laraba cewa mambobinta, ciki har da Amurka za su saki ganga miliyan 400 na mai da kayayyakin man fetur da aka tace daga rumbunsu domin rage matsin farashi a kasuwa.

    A baya-bayan nan ma Iran ta kai hari kan wasu jiragen ruwa biyu na dakon man fetur da ke ɗauke da man Iraqi a Mashigar f Hormuz, kuma rahotanni sun ce har yanzu suna ci da wuta.