Bikin sabuwar shekarar 2018 a Habasha cikin hotunan Afirka

Dandazon mutane ana kaɗe-kaɗe da raye-raye, yayin da ake rera waƙar sabuwar shekara a cocin Entoto St Raguel da ke a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha a ranar Alhamis 11 fga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Images

    • Marubuci, Amensisa Ifa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Addis Ababa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙasar Habasha na bikin shiga sabuwar shekarar 2018. Tana bin wani tsarin ƙirgar shekara na daban inda sauran ƙasashen duniya ke gaba da ita da shekaru bakwai.

Wat mata riƙe da ɗaurin itace tana sayen furanni a hannun wani matashi a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha a ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Furanni masu launin rawaya da aka fi sani da "adey ababa" a Habasha suna yabanya a ƙasar, musamman a lokacin shagulgulan. Ana sayar da ɗauri ɗaya a kan kuɗin Habasha birr 50, kwatankwacin $0.35.

Masu sayar da furanni da doguwar ciyawa a kasuwar Addis Ababa ta Habasha a ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Bikin wanda aka fi sani da Enkutatash ba ya da alaƙa da coci domin biki ne da ya shafi kowa da kowa a ƙasar. Masu saye da sayarwa suna cika titunan Addis Ababa, inda suke sayar da adey ababa da kuma ciyawa, kuma ana amfani da su ne wajen bikin na sabuwar shekara.

Dandazon mutane a kasuwar babban birnin Habasha, Addis Ababa. Wasu mutanen riƙe da kaji wasu kuma da ciyawa duk a cikin bikin sabuwar shekarar Habasha. An ɗauki hoton a ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Wuraren cinikayya irin Addisu Gebeya sun cika maƙil da mutane masu shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar, duk da ruwan da aka tafka ana gobe bikin.

Wani matashi sanye da safar hannu a kasuwar Addis Ababa, yana riƙe da zakaran da ya ke talla a ranar 10 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Wannan matashi mai shekara 19 sunan shi Tamirat Dejene, kuma ya je birnin Addis Ababa daga wani ɗan ƙaramin gari mai nisan kilomita 40 daga birnin wanda ake kira Chancho.

Ya shaida wa BBC cewa yana sayar da kaza ko zakara ɗaya a kan kuɗin Habasha birr 2,000.

Ana yanka kaji a lokacin bikin sabuwar shekarar Habasha kuma an fi zuba kajin a cikin wata miyar gargajiya da ake kira "doro wat", wadda kuma ake ci da burodi ko fanke.

Raguna uku da aka yi wa kwalliya da ƙyallaye masu launin shuɗi da ja, a birnin Addis Ababa. An ɗauki hoton ne a ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025, ana gobe sabuwar shekarar ƙasar Habasha.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Mutane su na cinikin kaji da aka ajiye a cikin keji a babbar kasuwar birnin Addis Ababa na Habasha a ranar Laraba 10 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Iyalai suna taruwa har su gayyaci abokan arziki domin cin abincin rana ko kuma na dare. Ana kiran abincin Enkutatash.

Cunkoson mutane a kan tagwayen titin birnin Addis Ababa a cikin dare. An yi wa wurare kwalliya da hotuna da kuma saƙwannin murnar shiga sabuwar shekara.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Kowacce ranar jajibirin sabuwar shekara a Habasha mutane suna gaggawar kammala sayen abubuwan da suke buƙata domin bikin. Da yammaci kuma ana taruwa domin kallon kaɗe-kaɗe da raye-raye da ake yi a sannan ƙasar.

A ɗaya daga cikin wuraren shaƙatawa da aka yi shagalin murnar sabuwar shekara a ranar Alhamis 11 ga watan Satumban 2025 a birnin Addis Ababa.

Asalin hoton, Amensisa Ifa/BBC

Wata tawagar ƙananan yara masu rawa da waƙa a yayin bikin sabuwar shekarar ƙasar Habasha a ranar Alhamis 11 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Images

A ranar sabuwar shekarar da safe ƴanmata na karaɗe gari da rera waƙar "Abebayehosh". A wasu sassan Habasha ƴanmatan na shiga gida-gida ne suna rera waƙar.

Wasu maza biyu masu sayar da lema da aka yi wa ado da kwalliya a gefen titin birnin Addis Ababa.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Images

Masu bautar addinin kirista suna gaisuwa ga limamin su a cocin St Raguel ta birnin Addis Ababa, a ranar Alhamis 11 ga watan Satumbar 2025.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Images

Mata masu yaɗa busharar addinin kirista guda biyar sun ja layi sanye da kayan ƙawa a cocin St Raguel da ke birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 11 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Images

Al'umar Habasha na amfani da kwanan wata biyu, inda idan suna maganar al'ada da tarihi ko harshen ƙasar suke amfani da kwanan watansu na gargajiya wanda a ƙirgar su yanzu suna a shekarar 2018 ne yayin da idan suka koma fannin amfani da harshen ingilishi suna tare da sauran mutanen duniya a shekarar 2025.