Abokan hulɗar BBC Hausa

Ana samun shirye-shiryen Sashen Watsa Labarai ga Kasashen Duniya na BBC (wato BBC World Service) ta hanyar radiyo, da talabijin, da kuma intanet.
Wannan alaƙa tana bai wa BBC damar gabatar da zaɓaɓɓun shirye-shiryenta ga jama'a masu tarin yawa.
A yanzu haka za a iya samun shirye-shiryen sashen na World Service ta hanyar wasu tashoshin fm a wasu ƙasashen Afirka.
Wasu daga cikin daɗaɗɗun abokan hulɗar BBC Hausa su ne:
Radio Gotel - 917kHz AM (Yola, Jihar Adamawa)
BRTV - 94.5FM (Maiduguri, Jihar Borno)
Freedom Radio - 99.5FM (Jihar Kano)
Freedom Radio - 99.5FM (Dutse, Jihar Jigawa)
Freedom Radio - 99.5FM (Jihar Kaduna)
PRTV - 88.65 FM, 92.1 FM, 90.5 FM, 1313 kHz AM (Jos, Jihar Plateau)
Rima Radio - 97.1FM, 540kHz AM (Jihar Sokoto)
Alfijir Radio Katsina FM 91.5










