Mene ne asalin muzaharar Qudus da 'yan Shi'a ke yi a duk shekara?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
A duk ranar Juma'a ta ƙarshen watan Ramadan ne ƴan Shi'a da wasu magoya bayan Falasɗinu a ƙasashen duniya suke gudanar da zanga-zangar "Ranar Qudus" ta duniya domin bayyana rashin jin daɗinsu da mamaye Gaza da gaɓar yamma da tekun Jordan.
A ranar ta Al-Quds ko kuma Quds ta duniya, magoya bayan Falasɗinu suna gudanar da zanga-zanga ko kuma muzahara nuna adawa da ƙasashen Amurka da Isra'ila.
Jagoran addinin Iran na farko, Ruhollah Khomeini ne ya assasa ranar a shekarar 1979 bayan juyin-juya-hali a ƙasar domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa. Tun daga shekarar ake gudanar da muzaharar, kuma take ƙara samun karɓuwa a ƙasashen duniya.
A wannan shekarar ta 2026, ranar ta faɗo ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairu, wato Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan na shekarar 1447.
Ina aka samo sunan Quds?
Al-Quds ko Quds kalmar Larabci ce da ake kiran birnin Jerusalem, wannan ya sa ake iya kiran ranar da "Ranar Jerusalem."
A Larabci kuma kalmar na nufin "mai tsarki."
Birnin Jerusalem, birni ne mai tsarki a wajen manyan addinai guda uku wato Kiristanci da Musulunci da Yahudanci.
Haka kuma Masallacin Al-Aqsa shi ne Masallaci na uku mafi daraja a Musulunci, duk da cewa Musulmai na fuskantar ƙalubale wajen amfani da shi daga Yahudawa na tsawon shekaru.
Yadda ake muzaharar Quds a ƙasashen duniya
Ana gudanar da zanga-zangar lumana ne a ƙasashen duniya, musamman a yankunan da magoya bayan Falasɗinawa suke da tarin yawa da kuma taruka da sauransu.
Zanga-zangar ta fi armashi a ƙasashen Pakistan da Iran da Iraqi da Lebanon da Yemen da Jordan da gaɓar yamma da kodin Jordan.
Haka kuma ana gudanar da zanga-zangar a ƙasashen Afirka, musamman Najeriya da Morocco da wasu ƙasashen daban.
A shekarun baya, ɗaruruwan mutane sun yi zanga-zangar a ƙasashen turai irin su Amurka da Canada da Birtaniya da Jamus da sauran ƙasashe a turai da Asia.
Rahotanni na nuna cewa ba Musulmai kaɗai suke zanga-zangar ba, domin ana samun wasu Kiristoci da Yahudawa da suke adawa da mamaye yankunan Falasɗinawa da suka shiga zanga-zangar.
Iran takan yi amfani da ranar domin nuna ƙwanji da ƙarfin sojinta ta hanyar shelanta su a kafofin sadarwa.
Ranar Quds a Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Najeriya, an sha samun lokutan da jami'an tsaro suke tarwatsa masu zanga-zangar, inda a wasu wuraren ma aka samu asarar rayuka idan masu zagayen sun yi arangama da jami'an tsaro.
Kusan shekara 40 ke nan ana zanga-zangar a jihohin Najeriya, yawanci a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ƴan Shi'a ta IMN da aka haramta a ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Zakzaky.
Wannan ya sa muka tattauna da Farfesa Abdullahi Danladi, kodinetan majalisar masana ta kungiyar wato Resource Forum kan ranar.
A cewarsa, rana ce ta jimami da nuna goyon baya ga mutanen yankin Falasɗinu, da kuma duk mutanen da ake tauye wa haƙƙi.
Sai dai ya ce suna mamakin yadda ake gudanar da zanga-zangar cikin lumana a ƙasashe, amma a Najeriya sai take yawan rikiɗewa zuwa tarzoma.
"Mu dai muna zagaye, sannan muna shirya tarukan ilimi. Kuma lafiya ƙalau muke gudanarwa mu tashi."
Daga cikin ranakun Quds da suka fi tashe akwai muzaharar ranar 25 ga watan Yulin 2014, inda aka samu arangama tsakanin jami'an tsaro da ƴan Shi'a a Zaria da ke jihar Kaduna.
A muzaharar shekarar ce aka kashe ƴaƴan jagoran ƙungiyar IMN, Malam Ibrahim Zakzaky guda uku, lamarin da ya ɗauki hankali matuƙa.
A game da irin wannan arangamar, Farfesa Abdullahi ya ce su dai ibada suke yi, "kuma ban san me ya sa a Najeriya kaɗai ake yawan samun haka ba. Shi ya sa nake inkarin a ce muna arangama. Muna zagaye ne kawai ake far mana. Idan ba a far mana ba, muna yi mu tashi lafiya."
Ya ƙara da cewa ko a shekarar 2003, a Kano an kashe musu mutum shida, sannan a shekarar 2009 ya ce an kashe mutum uku.
"Sannan ko a bara an kashe mana mutane, aka tafi gawarwakin wasu. Wasu daga cikin gawarwakin sai kwanan nan aka dawo mana da su, sannan akwai kusan 100 da ke tsare," in ji shi.
Wuraren da aka samu hargitsi a baya

Asalin hoton, Getty Images
An yi sama da shekara 40 ana gudanar da zanga-zangar Ranar Quds a Birtaniya, amma a shekarar 2017, Magajin Garin London Sadiq Khan ya buƙaci sakataren harkokin ciki na lokacin, Amber Rudd ta sanar da haramta zanga-zangar.
Sai dai ta ce ba za ta rubuta ba, domin a cewarta dole a bar mutane su gudanar da zanga-zangar domin suna da ƴanci.
Masu zanga-zangar suna fuskantar barazanar hargitsi da rikici daga ƴansanda da sojoji.
A shekarar 2010, ƙungiyar Tehreek-e-Taliban ta Pakistan ta ɗauki alhakin harin ƙunar bakin-wake kan masu zanga-zangar Ranad Quds a birnin Quetta na ƙasar, wanda ya kashe aƙalla mutum 65, ya raunata sama da mutum 100.
Bayan wannan, an kuma wasu wuraren da zanga-zangar ke riƙewa ta zama tarzoma, inda a wasu wuraren ma ake asarar rayuka.











