Yadda za ku iya ganin daren Laylatul Ƙadari

Asalin hoton, getty images
Daren laylatul ƙadari dare ne mai albarka kuma wanda a tsahon kwanakin duniya baki ɗaya babu daren da ya kai shi alkhairi da albarka kamar yadda Sheikh Ahmad Atiku Auwwal, malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna da ke Najeriya ya bayyana.
Sheikh Awwal ya ce Allah (SWA) ya taƙaita bayanin wannna dare a cikin Suratul Ƙadri
Ya ce Surar ta suffanta daren Laylatul Ƙadiri da cewa ya fi dare dubu alkhairi inda ya ƙara da cewa, ma'anar wannan shi ne ibadah a cikin dare ta fi ibadah a darare dubu lada da alkhairi.
Malamin ya ce daren laylatul ƙadiri dare ne kuma wanda a cikinsa ne Allah (SWA) ya saukar da al-ƙur'ani mai girma.
Kuma a cikinsa ne Allah ke ƙaddara abubuwan da za su faru a tsawon shekara baki ɗaya ta fuskan ajalin mutane da alkhairai da sharri da zai gudana a shekara.
Malam ya ƙara da cewa dare yana da tsada da daraja, wanda bai kamaci duk musulmi ya yi wasa da shi ba, ya kamata ya yi ƙoƙarin laluban wannan dare domin ya dace da alkhairin da yake cikin shi.
Kwanakin da ake sa ran ganin Laylatul Ƙadari
Malamin ya ce abin da ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) shi ne wannan daren tabbas yana cikin kwanaki goma na ƙarashen watan Ramadan.
Kuma a kan kwanakin goman kuma Manzon Allah (SAW) ya yi bayanin cewa daren, ana sa ran ya kasance a cikimn dararen da suke ma.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Manzon Allah (SAW) ya ce al'ummar musulmi su lalubi wannan dare tun daga dare 21 ko daren 23, ko daren 25 ko na 27 ko kuma na 29, ya ce wannan dare na Laylatun Ƙadiri zai iya kasancewa a cikin waɗannan darare." in ji malamin.
"Don haka abun da ake so shi ne mutum ya yi ƙoƙarin raya waɗannan dareye baki ɗayansu saboda ya dace da wannan dare, domin baka san a wanne daren zai kasance ba."
"Malamai sun ce daren laylatul Ƙadiri na iya cacanjawa a kowacce shekara, wata shekara zai iya faɗawa a ranar 21, amma kuma wata shekarar ya faɗa a daren 23 ko 25."
"Amma kuma an samu ruwayoyi da suke nuna rinjayar da daren ya fi kasancewa a 27 shi ne daren da aka fi sa rai ya kasance na Laylatun Ƙadiri.
Ya kasance har ma wasu daga cikin sahabai suna rantsuwa cewa daren 27 shi ne daren Laylatul Ƙadiri." in ji Shiekh Awwal
"Amma kuma mutum mai wayo da dabara shi ne wanda zai raya dararen baki ɗaya, tunda ba a ayyana taƙaimaimai ga ranar da za ta kasance ba, kuma haka a ka ga Shugaban Halitta yana yi. Ya kasance yana raya kwanaki goman gaba ɗayansu kamar yadda muka ji daga matarsa Nana Aisha, saboda fatan dacewa da wannan dare." in ji malamin.
Malamin ya ƙara da cewa Manzo Allah (SAW) ya ce duk mutumin da tsaya ya yi ibada, yana mai imani da Allah, yana kuma mai imanin falala da alkhairin da ke cikin wannan dare, kuma yana mai neman lada a wurin Allah, to Allah ta'allah zai gafarta masa zunubansa da suka gabata.
Abubuwan da ya kamata mutum ya yi a waɗanan darare
Sheikh Awwal ya ce mutum zai iya raya waɗanan dararen da duk wani dangi na aikin ibada kama daga karatun alƙur'ani mai girma da amboton Allah (SWA) da istigfari da tasbihi, da hailala da hamdala da kuma salloli.
"Amma kuma salloli su ne abin da Manza Allah (SAW) ya fi yi a waɗannan darare, baya ga salloli kuma mutum zai iya haɗawa da karatun alƙur'ani da sauran nau'ukan zikiri da suka tabbata daga Shugaban Halitta."
Malamin ya ƙara da cewa "Sallolin dare a waɗannan kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadana suna da matuƙar muhimmanci. Saboda waɗannan kwanaki 10 su ne kwanaki mafi tsada a cikin watan Ramadan."
"Shi yasa Manzon Allah (SAW) ya kasance yana ƙara ƙoƙari a daren sama da yadda yake yi a sauran kwanakin watan Ramadan da suka wuce, kuma yanayin ibadun tare da iyalensa gaba ɗaya."
Malamin ya ce wannan ya nuna cewa idan waɗanna kwanaki 10 suka zo bai kamata mutum ya riƙa sako-sako wajen ibada ba.
Kamata ya yi mutum ya ƙara dagewa saboda waɗannan kwanaki 10 sune mafi daraja kuma mafi tsada kuma a cikinsu domin dacewa.
Adadin raka'o'in da ake son musulmi ya yi a daren Laylatul Ƙadiri
Malam Awwal ya ce Manzon Allah (saw) ya kasance yana yin raka'a 11 a cikin watan Ramadan to amma abin da malamai ke cewa shi ne su sallolin dare adadin su, adadi ne da yake a buɗe, babu wani adadi da aka ƙayyade da aka ce dole sai mutum ya taƙaitu da su.
"Sallolin dare kamar yadda yazo a hadisai ana yin su raka'a bibbiyu ne, gwargwadon abun da Allah ya horewa mutum, saboda haka abin da ake so shi ne mutum ya dage ya yi iya bakin ƙoƙarinsa, babu wani laifi a yin hakan."
"Fatan shi ne Allah ta'allah ya karɓi ibadunmu." in ji malamin
Lokacin da ya kamata a fara sallar dare

Asalin hoton, getty images
"Sallar daren tana farawa ne daga bayan sallar Isha'i, don haka sallar tarawihi da ake yi da kuma wace ake yi ta cikin dare duka suna cikin sallar dare, to sai dai bambancin shi ne, ita sallar tarawihi ana yin ta ne kafin a kwanta bacci, ita kuma sallar tahajjudi ita ce wadda ake yi cikin dare bayan an kwanta an tashi daga bacci" kamar yadda malamin ya ƙara da cewa.
A ina aka fi so a yi sallar
Malam Awwal ya ce ita sallar dare a watan Ramadan musamman ma ga maza, an fi so a je masalaci a yi saboda sunnah ce tabbatacciya ta Manzon Allah (saw) wanda ya yi tare da sahabai a masalaci.
"A farkon lokacin da Manzon Allah (saw) ya fara yin sallar dare, sahabbai suka zo suka fara taruwa suna yi tare da shi, toh sai ya ji tsoron ka da a sanya ta ta zama farilla, toh daga nan sai ya bari."
"Bayan Manzon Allah (saw) ya koma ga Allah ta'allah, sai sayyidina Umar ya sake tattara sahabbai ya saka musu limami guda ɗaya, saboda fargabar farillanta sallar ta ƙare Shugaba ya yi wafati, babu sauran wahayi."
"Daga nan sai sahabbai suka tafi a kan wannan sunnah da suka raya ta Manzon Allah (saw) suke taruwa a masallaci su yi tare da liman kamar yadda hadisi ya zo daga Manzan Allah (saw) cewa duk wanda ya yi sallar tsayuwar dare tare da liman har zuwa lokacin da liman ya sallame, to Allah zai rubuta masa ladan wanda ya yi sallar dare baki ɗaya."
"Amma idan mutum ya yi a gidansa, wannan ma ba laifi, ya yi ba, amma su mata, hadisi ya zo daga Manzan Allah (saw) cewa sallarsu a gidajensu ta fi musu alkhairi a kan su yi a masallaci."
"Amma kuma idan su ma matan suka ce suna son su je masallaci su yi, Mazan Allah ya ce karda a hana su."
Mene ne ingancin riƙe alƙur'ani lokacin sallar dare?
"Abin da malamai suke cewa shi ne idan mutum ya zama ba zai iya yin sallar dare ta hanyar yin karatu da ka ba, ma'ana bai haddace alkur'ani ba, to babu laifi ya riƙe alƙur'ani wajen karatu a lokacin sallar." malamin ya ƙara bayani.











