...Daga Bakin Mai Ita tare da Ahmad Shanawa
...Daga Bakin Mai Ita tare da Ahmad Shanawa
Wannan mako cikin shirin Daga Bakin Mai Ita mun kawo muku tattaunawa da mawaƙin Hausa Ahmad Abubakar Sa'id, wanda aka fi sani da Ahmad Shanawa.
Ɗan asalin garin Jos da ke arewacin Najeriya, Ahmad ya bayyana wa BBC yadda ya fara waƙa duk da cewa ba abin da ya so ba ke nan a farkon shigar sa Kannywood.



