BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Mece ce gaskiyar dalilan Abba Kabir na komawa APC?
Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya kwaɓe jar hula ya tsallaka jam'iyya mai mulki a Nijeriya, amma da yawan mutane na da tambayar, shin mene ne haƙiƙanin dalilinsa na barin tafiyar Kwankwasiyya?
Juve na son Beto, Ina Bruno Fernandes zai tafi?
Nottingham Forest ta taya ɗanwasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta kan fam miliyan 35, Juventus na nazarin ɗauko ɗanwasan Everton Beto, Sannan ɗanwasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes zai tantance makomarsa a ƙarshen kaka.
'Abubuwan da ya kamata majalisa ta mayar da hankali bayan komawa hutu'
Kungiyar CISLAC ta nemi Majalisun dokokin Najeriya su mayar da hankali kan gyara dokar zabe da matsalar tsaro bayan sun koma hutu
Larabawan da suka ɗauki kasadar ceton Yahudawa lokacin kisan kiyashi
An karrama mutum 28,000 waɗanda ba Yahudawa ba saboda ɗaukar kasada na ceto rayukan Yahudawa lokacin kisan kiyashi na Holocaust.
Sojoji sun tabbatar da yunƙurin yi wa Tinubu juyin mulki
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.
Abin da ya sa na koma jam'iyyar APC - Abba Kabir Yusuf
Yayin da yake jawabi a wajen taron gwamnan ya ce ya ɗauki matakin komawa jam'iyyar APC bayan tuntuɓar abokansa na siyasa, da kuma ci gaban al'ummar jihar Kano.
Dalilin da ya sa wasu mutane ke jarabtuwa da caca
Caca tare da shan da miyagun ƙwayoyi da barasa za su iya zama jaraba idan ba a yi ta-ka-tsan-tsan ba.
'Sun girke bindiga a kan titi suna ɓarin wuta': Abin da muka sani kan sace mutane a Mafara
Ƴan bindigar sun sace mutum 26 a cikin kwana biyu da suke kai hari kan ƙauyuka a ƙaramar hukumar ta Talatar Mafara, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC.
Lokuta bakwai da aka ɓaɓe tsakanin 'ubangida da yaronsa' a siyasar Najeriya
Saɓani tsakanin ubangida da mabiya ko amini a siyasar Najeriya abu ne da ya daɗe yana faruwa, inda akasari hakan ke faruwa bayan mabiyin a siyasance ya hau mulki kuma ya fara ganin cewa karansa ya kai tsaiko.
'Yadda aka kashe rabin ƙawayena a harin bam kan makarantarmu'
Mutuwar ƙawayensu da malamarsu ta ƙara wa tagwayen mata ƙwazo wajen ganin sun kammala karatunsu.
Yadda haraji ya tilasta rufe makarantar da ta yi shekara 106
An sanar da matakin rufe wata makarantar kudi da ta shekara fiye da 100 ana karatu a cikinta. Za a rufe makarantar ne a karshen zangon karatu na wannan shekarar saboda matsalar kudaden gudanar da ita.
An gano gidajen yarin sirri na Daular Larabawa a Syria
BBC ta ziyarci waɗannan wurare da ake tsare mutane da suka kasance tsoffin sansanonin sojin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Yemen, inda mutane suka ce an ci zarafinsu.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 27 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 26 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 26 Janairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 26 Janairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Wace dabara Carrick ke amfani da ita wajen samun nasara a United?
Michael Carrick na da ƙwarewar da ba za ta sa ya shagaltu ba kan cewa ko yana son zama kocin Manchester United na dindin.
Man City na son Alexander-Arnold, Liverpool ta tuntuɓi Alonso
Manchester City na zawarcin Trent Alexander-Arnold, Liverpool ta samu amsa mai kyau bayan da ta tuntuɓi Xabi Alonso sannan Chelsea ta sake kiran Aaron Anselmino daga Borussia Dortmund.
KAI TSAYE, Ƙwallo ɗaya Haaland ya ci a wasa takwas baya, ko yana bukatar hutu?
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 18 zuwa 30 ga Janairun 2026
Chelsea na son Mbaye, Arsenal sai ta biya £80m kafin karɓo Alvarez
Tottenham da Liverpool na tattaunawa kan cinikin Andy Robertson, Bournemouth na dab da ɗauko Christos Mandas a matsayin aro, yayin da Arsenal ke shirin lale fam miliyan 80 kan Julian Alvarez.
Arsenal na son Alvarez, Mece ce makomar Alexander-Arnold?
Ɗanwasan baya na Real Madrid Trent Alexander-Arnold ba a shaida masa ya nemi wata ƙungiya ba a bazara, Arsenal na harin ɗanwasan gaba na Atletico Madrid Julian Alvarez, yayin da Liverpool ke shirin hamayya da Bayern Munich kan ɗanwasan RB Leipzig Yan Diomande.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Abubuwa 7 game da tsohon fitaccen mawaƙi Fela Anikulapo Kuti
Bayan shekaru da dama, taurari a mawaƙan Najeriya da suka yi ƙaura daga ƙasar na amfani da irin salon waƙoƙinsa bayan ya mutu.
Alamu biyar da ke nuna cewa ɗan'adam na samun ci gaba a doron ƙasa
A cikin wannan muƙala, mun zaƙulo wasu abubuwa biyar, da ke tuna mana irin nasarorin da muka samu cikin gomman shekaru a fannoni daban-daban
Ƴan majalisar dokokin jihar Kano 22 sun fice daga NNPP
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Me ya sa ƙasashen Larabawa ke ɗari-ɗari kan yiwuwar rushewar gwamnatin Iran?
Yiwuwar ɗaukar matakin soji na Amurka kan Iran ya kasance wani muhimmin batu da ke matuƙar kawo damuwa a ayyukan diflomasiyyan ƙasashen larabawa, musamman tsakanin ƙasashen da ke ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf.
Abin da APC ta ce kan matsayin Wike a jihar Rivers
Da alama jam'iyyar APC da gwamnatinta a Najeriya, sun fara juyawa ministan Abuja, babban birnin tarayyar kasar, Nyesom Wike, baya
Yadda 'Isra'ila ke ƙara cin wasu yankuna a Gaza' duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Isra'ila ta ƙara matsar da shigenta - da aka amince da ta tsaya a lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin wurin da take iko da shi - zuwa cikin Gaza, wani abu da ya ƙara haifar da fargaba tsakanin Falasɗinawa.
Wani abincin ƴan China da ke sanya mutane gane-gane
Marasa lafiyar kan bayyana wasu alamomin da ba a saba gani ba: ganin wasu mitsi-mitsin mutane da ke taruwa a ƙarƙashin ƙofofi, ko suke hawa bango ko suke mannuwa a jikin kujeru.
Manyan dokokin zaɓen da ake son yi wa gyara a Najeriya kafin 2027
Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la'akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023.
Kun san abin da ya sa ɗan'adam ke yin kuka?
Me ya sa ɗan'adam ke yin kuka, kuma me ya sa wasu ke zubar da hawaye saboda tausayi? Wannan na cikin abubuwan da ba a gama sani ba har yanzu.
Ko yawan aske gashin al'aura na ƙara haɗarin kamuwa da cutar sanyin gaba?
Wannan sakamakon binciken ya saɓa da wasu binciken da aka yi a baya da suka yi gargaɗin cewa cire gashin al'aura gaba ɗaya na iya haifar da yanka a kan fata, wanda hakan zai bai wa cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STIs) damar shiga jiki .
Mece ce makomar NNPP bayan ficewar Gwamna Abba Kabir?
Ana tunanin gwamnan zai tafi da wasu jiga-jigan gwamnatin, waɗanda ƙusoshi ne a tafiyar Kwankwasiyyar.
Mece ce makomar jagoran addinin Iran?
Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei - wanda ke ɓoye a wani wuri na sirri - a ƴan kwanakinnan yana cike da sanin cewa ana sanya idanu a kansa, fiye da lokutan da suka gabata a baya.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.









































































