Tsaka mai wuyar da Kannywood ke ciki

Abba Mustapha Inuwa

Asalin hoton, Abba Mustapha Inuwa/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

A ɓangaren nishaɗin Najeriya, za a iya cewa masana'antar fim ta kudancin ƙasar da ake kira da Nollywood ta rufe takwararta ta arewaci da ake kira Kannywood, musamman a ɓangaren samar da kuɗi.

Sai dai Kannywood ɗin ma ta dage wajen samar da hanyoyin da take ganin za su ɓille mata domin samun nasarar riƙe kanta da kuma ci gaba da kasancewa a harkar ba tare da durƙushewa ba.

Masu shirya fina-finai da dama daga kudancin Najeriya da wasu daga sassan duniya suna sha'awar zuwa arewacin Najeriya domin shirya fina-finai ta hanyar amfani da labaran yankin, amma suna fuskantar ƙalubale.

Daga cikin matsalolin da suke ganin suna musu cikas akwai al'adun mutanen yankin, waɗanda yawanci musulmai ne, kuma addini na da matuƙar tasiri a yankin, lamarin da ke buƙatar dubawa kasancewar domin masu kallo ake fim.

Akwai kusan mutane miliyan 80 da suke magana da harshen Hausa a duniya, inda suka bazu a tsakanin yammaci da tsakiyar Afirka, da kuma wasu mazauna wasu ƙasashen duniya, wannan ya sa dole wani mai shirya fim ya yi sha'awar shiga kasuwar fina-finan Hausa.

Sai dai ƙalubalen da ke tsaiko ɗin na da wahalar tsallakewa. Bayan al'adu, akwai shari'ar musulmi da ake da yi a wasu jihohin yankin, musamman jihar Kano, wadda ita ce babbar cibiyar Kannywood, sannan kuma akwai hukumar tace fina-finai da dubawa tare da tace fina-finan da ake fitarwa.

Duk fim ɗin da ya saɓa da dokoki da ƙa'idar hukumar, masu shirya fim ɗin sukan fuskanci hukunci, ciki har da dakatarwa da cin tara da sauransu.

Kamilu Ibrahim na cikin matasan daraktoci a masana'antar da suke ƙoƙarin kawo sauyi, inda bayan saka fassarar Ingilishi a fina-finansa, yanzu ya fara sanya fassarar Larabci domin kai wa ga masu kallo da dama a ƙasashen duniya.

Masu shirya fina-finai dai suna ta ƙoƙari wajen ci gaba da tsara a fina-finan da suka fi yawa na taken Nollywood: wato soyayya da ramuwar gayya da cin amana da sauransu.

Amma duk "wani abu da yake nuna sassan jiki na al'aura da ma duk wasu fina-finan ko shirye-shirye da suka saɓa da al'ada da addini, ba za mu lamunta ba," in ji Abba El-Mustapha, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a zantawarsa da AFP.

Biyan kuɗi a kalla fim

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

AFP ta ziyarci Ibrahim a wajen shirya zangon na biyu na shirinsa na "Wata Shida", wanda ya shirya kan budurwar da aka yi yunƙurin yi wa auren dole bayan rasuwar mahaifinta.

Domin tserewa daga yunƙurin auren, sai ta shirya da wani saurayin, suka yi auren kwantiragi maimakon auren soyayya.

"Ba mu saba ganin mutum ya yi abu ba ba tare da neman albarkar iyayensa ba," in ji Ibrahim, sannan ya ƙara da cewa za a iya amfani da fim wajen "tattaunawa da magance wasu matsalolin rayuwa."

Jaruma "Wata Shida", Adam Garba ya ce yana fata za a haska fim ɗin a manyan manhajojin haska fina-finai nan gaba, duk da cewa yanzu haka ana kallon shirin a kafar YouTube.

Yawancin fina-finan Najeriya da ake iya samu a Netflix da Amazon Prime na kudancin ƙasar ne, domin babu fina-finan Hausa da yawa.

"Kudancin Najeriya sun fi kashe kuɗi a fim, sun fi amfani da manyan kayan aiki, sun fi masu ɗaukar nauyi da masu zuba jari," in ji Adamu Garba.

A wani ɓangaren kuma, Abdurrahman Muhammad Amart, wanda ya ƙirƙiri Arewaflix domin haska fina-finan Hausa kamar yadda ake da Netflix ya ce za a iya samun gagarumin canji.

"Amma Arewaflix ba za ta tsaya a fina-finan Hausa ba kawai, za ta haɗa da fina-finan wasu harsunan na arewacin Najeriya kamar Kanuri da Nufanci da sauransu, " in ji Amart.

Ya ƙara da cewa za a riƙa rubuta fassarar fina-finan da turancin Ingilishi da Farasanci da Larabci.

Sai dai ba Arewaflix ba ce manhaja ta farko da aka ƙirƙiri domin wannan aikin, domin a shekarar 2023 ma an yi ƙoƙarin samar da manhajar Northflix, amma ba a samu nasarar da ake buƙata ba.

Sai dai samun mutane su riƙa biyan kuɗi domin kallon fim a Najeriya yana da wahalar gaske, musamman ganin yadda ƙasar ke fama da talauci da taɓarɓarewar tattalin arziki.

"Da zarar wasu sun samu fim ɗin, sai su sauke su riƙawa ga wasu saboda cikakken tsaron haƙƙin mallaka," in ji Abba.

Koyi da Indiya

Masana'antar dai a yanzu tana fuskantar ƙalubale masu yawa, amma tana ci gaba da ƙoƙarin gurgurawa, amma duk da haka, a cewa Umar Abdulmalik, akwai buƙatar samun manyan kayan aiki na zamani.

Ya ce idan suka samu kayan aiki da masu zuba jari, suna da labarai masu kyau da ƙwararrun da za su isar da fina-finai masu kyau da ƙayatarwa da Hausa ba tare da matsala ba.

Ya kwatanta yadda fina-finan Indiya suka samu karɓuwa a Najeriya duk cewa akwai waɗanda ba sa jin Ingilishi da Indiyanci, "amma suna jin daɗin abin da suke kallo."

Amma dai yanzu babban abin da gaban Kannywood shi ne: shirya fina-finai masu kyau, da ɗan abun hannunsu.