Burinmu shirin Gidan Badamasi ya rage wa ƴan Najeriya damuwa - Ɗorayi

Gidan Badamasi

Asalin hoton, FB/Falalu Dorayi

Lokacin karatu: Minti 2

Shirin fin din Hausa na Gidan Badamasi na daga cikin finafinan barkwanci da suka fi fice a shekarun baya-bayan nan a kasar Hausa.

A tsawon shekaru an dade ana zargin masu shirya finafinan Hausa da mayar da hankali kan labaran soyayya tsantsa, tare da watsi da sauran fannoni.

Daraktan shirin, mai dogon zango, Falalu Ɗorayi ya ce sun yanke shawarar ci gaba da shirin ne domin suna fata ya ci gaba da ɗebe wa masu kallo kewa da damuwa a wani lokaci da ake fama da matsi na tattalin arziki a kasashe da dama.

Tuni aka fara haska sabon zango na fim ɗin, lamarin da ya ja hankali har a kafofin sadarwa, ganin yadda fim ɗin ya ɗauki hankalin masu kallo a lokacin da yake tashensa.

Bayan kammala zango na shida ne aka sanar da kammala shirin, amma Falalu ya ce sun koma bakin aiki ne saboda kiraye-kirayen masu kallo.

'Shirin na ɗebe kewa'

Daraktan fim din Gidan Badamasi Falalu Dorayi

Asalin hoton, Falalu Dorayi

Bayanan hoto, Daraktan fim din Gidan Badamasi Falalu Dorayi

A wata tattaunawa da BBC, Falalu Ɗorayi ya ce “mun ga yadda masu kallo ke kewarsa, kuma suke nuna cewa an samu wani giɓi a masana'antar Kannywood," in ji shi.

Daraktan ya ƙara da cewa shirin Gidan Badamasi shiri ne da za a iya tara dangi - kakanni da iyaye da yara da jikoki- a kalla a tare ba tare da wata fargaba ko damuwar ganin abin da bai dace ba.

A game da irin saƙonnin da shirin ke ɗauke da shi, Falalu ya ce, "sun haɗa da fito da haƙƙin iyaye a kan mahaifi, da haƙƙin mahaifi a kan ƴaƴansa da cin amana da son abin duniya, sannan uwa uba muna isar da saƙon ne a cikin barkwanci da nishaɗi."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Falalu ya ƙara da cewa ganin yadda Najeriya take a ciki a yanzu, "akwai buƙatar fina-finai masu nishaɗantarwa cikin barkwaci.

"Kuma shirin Gidan Badamasi na taka rawa a wannan fagen wajen ɗebe kewa da saka farin ciki a zukatan mutane.“

“Shiri ne da ya taɓa kowane ɓangare na rayuwa," in ji Dorayi.

Sai dai daraktan ya ce baya ga barkwanci, a wannan karo shirin zai tabo matsalolin da al’umma ke fama da su a arewacin Najeriya kamar garkuwa da mutane.

"Yanzu kusan matsalar tsaro ce ta fi damun ƴan Najeriya, don haka ne muka shigo da batun garkuwa da mutane, inda ake garkuwa da Alhaji Badamasi duk tsananin son kuɗinsa."

Falalu ya ce sai da suka gudanar da bincike sosai kan yadda ake yi idan an yi garkuwa da mutane, "domin mu isar da saƙon cikin hikima da basira," in ji shi.

"Mun yi fashin baƙi sosai kan garkuwa da mutane bayan bincike da nazarin da muka yi. Sannan mun fito da wani abu kan batun ƙabilanci a harkar, da ma fito da abin da ya kamata a yi idan an kama mutum da ma hanyoyin magance matsalolin tsaro."