Sababbin fina-finan Hausa da suka yi tashe a 2025

Maishadda Global Resources

Asalin hoton, Maishadda Global Resources/Youtube

Lokacin karatu: Minti 4

A shekarar 2025, wasu forodusoshi sun shirya tare da fitar da fina-finai da dama da suka ciri tuta, har suka zama abin magana da tafka muhawara a kafofin sadarwa na zamani.

An samu fina-finai da dama da suka fito a bana, kuma suka samu karɓuwa matuƙa gaya, har suke gogayya da fina-finan da aka daɗe ana nunawa a kafofin YouTube da talabijin.

Kamar yadda muka saba, a wannan shekarar ma mun zaƙulo muku wasu fina-finan Hausa da suka ɗau hankalin masu kallo.

Sai dai a bana, mun taƙaita nazarin ne kan fina-finan da aka fitar a wannan shekarar ta 2025, kuma suka fara ɗaukar hankali cikin ƙanƙanin lokaci.

Jamilun Jiddan

A ranar Asabar, 11 ga watan Janairun shekarar 2025 ne aka fara fitar da fim ɗin 'Jamilun Jiddan' mai dogon zango.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ne ya jagoranci shirya fim ɗin, fasihin marubuci Yakubu M. Kubo ya tsara labarin, sannan darakta Ali Gumzak ya bayar da umarni.

Fitowa ta farko na zango na ɗaya zuwa yanzu masu kallo sama da miliyan 1.3 ne suka kalla, sannan yanzu an kammala zango na biyu na shirin, inda fitowa ta ƙarshe a zango na biyu a watan Oktoba fim ɗin ya samu masu kallo sama da dubu 800.

Fim ne a kan soyayyar Jamilu (Sadiq Sani Sadiq) da Jidda (Firdausi Yahaya) wadda take da tsananin kishi.

A gefe guda kuma Jidda tana samun goyon bayan mahaifinta Farfersa Nuri (Ali Nuhu) wanda asali abokin mahaifin Jamilu ne wato Nura Hussaini wanda ya fito a babban malami mai aikin da'awa.

Farfesa na tsananin ƙaunar ƴarsa Jiddan, wanda hakan ya sa yake goyon bayanta duk abin da take so, lamarin da ya sa suke taka Jamilu yadda suke so saboda ba ɗan boko ba ne.

Daga baya dai al'amura sun rincaɓe bayan Jamilu ya hango Kirista mai suna Ruth (Fatima Hussaini), inda ya nace sai ya aure ta.

Zaɓi Biyu

'yan fim ɗin Zaɓi Biyu

Asalin hoton, Arewa24

'Zaɓi biyu' fim ne mai dogon zango na Arewa24 wanda aka fara nunawa a wannan shekarar ta 2025.

Labari ne a kan wasu ɗalibai a jami'a, Don Nas da Mansur, waɗanda suka saka caca a kan budurwa Safiyya, rawar ta sabuwar jaruma Hassana Ibrahm Rano ta taka.

Cacar ita ce idan har Mansur ya ja hankalinta suka fara soyayya, za a ba shi kyautar mota.

A can gefe kuma akwai Bello, wanda shi ne saurayin da aka saka wa rana da Safiyya, inda abin da aka fara a matsayin wasa ya rikice a tsakanin samarin uku da budurwar.

Arewa24 ce ta shirya kuma ta ɗauki, sannan fitaccen darakta Salisu T Balarabe ya bayar da umarni.

Fim ɗin ya ɗau hankali matuƙa, inda a wani rubutu da mai sharhi kan harkokin fina-finai Muhsin Ibrahim na Jami'ar Cologne ya yi a Facebook ya ce shirin na cikin ƙayatattun dirama mafi kyau da aka shirya na Hausa.

Wata Shida

'Yan fim ɗin Wata Shida - mace da maza biyu tsaye a kusa da mota

Asalin hoton, danhausa1/Instagram

Labari ne a kan wata budurwa Zarah (Fatima Hussaini), wadda ta gaji ɗimbin dukiya daga mahaifinta.

Kawunta Nakowa (Magaji Mijiwana) sai ya dage dole sai ta yi aure da ɗansa, wanda hakan ya sa ta gudu zuwa Kaduna inda ta shirya auren wata shida da wani saurayi mai suna Ɗahiru ko Samir (Adam Garba) wanda ya ɓoye asalinsa da arzikinsa da iliminsa ya fito a talaka domin neman soyayyar gaskiya.

Amma abin da aka fara a matsayin auren kwantiragi, sai ya rikiɗe zuwa soyayya da ƙauna ta gaskiya, sannan abubuwa suka caɓe a kan rikicin soyayya da gado da sauransu.

Kamilu Ibrahim Ɗan Hausa ne ya jagoranci Abba Harara da Sade Yarima wajen rubutawa da tsara labarin, Hayatuddeen Yakubu ya shirya fim ɗin, sannan Kamilu Ibrahim Ɗan Hausa ya bayar da umarni.

An fara nuna fim ɗin ne a ranar 2 ga watan Yulin 2025, kuma fitowa ta farko ta samu kallo sama da miliyan 1.5 zuwa yanzu, sannan fim ɗin ya samu karɓuwa sosai.

Da na sani

Abdul Amart

Asalin hoton, Abdul Amart/Facebook

Fim ɗin 'Da na sani' yana cikin fina-finan da kamfanin shirya fina-finai na Abnur Entertainment ya shirya a cikin kundin shirye-shiryensa na Taskar Kannywood.

Fim ɗin ya yi tashe, musamman irin rawar da jaruma Amina Lulu ta take a matsayin matar Aminu Shariff Momoh.

Fim ɗin ne ya ƙara fito da jaruma Lulu, inda aka riƙa kiranta da suna 'Ƙwaila' saboda rawar da taka a matsayin amarya mai yawan son wasa da shagwaɓa, inda ta aura miji Momoh wanda shi kuma irin mazan nan da ba sa son wasa ko kaɗan.

A ƙarshe dai jarumar tana mutuwa a fim ɗin, lamarin da ke jefa Momoh cikin damuwa da da-na-sani.

Bayan jaruman da suka taka rawa, fim ɗin ya fito da sabuwar forodusa, Amina Adam Yusuf wadda ta jagoranci shirya shirin, inda aka riƙa yaba mata a kafofin sadarwa.

Yakubu M. Kumo ne ya tsara labarin, sannan Ahmad Bifa ya bayar da umarni.

Yanayi

Yanayi

Asalin hoton, Mu'azzamu Idi Yari

Yanayi wani sabon fim ne a kan matasa ƴan tsakankanin shekara 18 da suke shirin kammala makaranta.

Kwatsam sai ƙungiyoyin ɗaliban guda biyu White House da Golden House suka shiga rigima da juna domin nuna ƙwanji da isa.

Amma a ƙarshe sai ɗaya daga cikin ɗaliban ya rasu, lamarin da ya haifar da da-na-sani da wata sabuwar rigima.

Amina Lulu ce ta ja fim ɗin a matsayin Nihal da Faisa Musa da ya taka rawar Bilal da Amina Ahmad da ta fito a matsayin Nafisa, sai manyan jarumai irin su Sani Danja da Amina Uba da sauransu.

Fim ne da Mu'azzam Idi Yari ya shirya kuma ya bayar da umarni. Sabon fim ne, amma daga fitowa ya fara ɗaukar hankali.