An yi ƴan wasan Senegal alkawarin kuɗi da gidaje a bakin teku, Afcon Morocco 2025/26

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi alkawarin ba da kuɗi sama da dalar Amurka 130,000, tare da filaye a bakin teku, ga kowane ɗan wasan tawagar kasar a matakin ladan lashe Afcon ranar Lahadi a Morocco.
Ya bayyana hakan ne a wani biki da aka gudanar a babban birnin ƙasar, Dakar, inda dubban magoya baya suka yi ta murna suka cika tituna domin tarbar zakarun kofin Afirka, Lions of Teranga, bayan dawowarsu gida.
Senegal ta doke mai masaukin baki, Morocco, da ci 1–0 bayan ƙarin lokaci a karawar da aka samu cece-kuce a ƙarshen mintuna 90, inda aka yanke hukuncin ba da bugun fanareti, lamarin da ya sa suka fice daga filin wasa kafin daga bisani a ci gaba da karawar.


















