Na ɗauki wasa da mota a matsayin sana'a - JayBash
Na ɗauki wasa da mota a matsayin sana'a - JayBash
Daga toshe tituna da abokansa don yin wasan motoci, zuwa wakiltar Najeriya a gasannin wasan mota a ƙasashen waje.
Bashar Muhammad Jamus wanda aka fi sani da JayBash ya ɗauki wasan mota a matsayin sana'a duk da irin hatsarin da ke tattare da shi, ya kuma bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta da alfanun wasan ga Najeriya idan har gwamnati za ta inganta fannin.



