'Daren ƙarshe na rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi'

Bayanan bidiyo, latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
'Daren ƙarshe na rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi'

Matar Sheikh Dahiru Bauchi, Hajiya Aisha, ta bayyana wa BBC yadda malamin ya yi numfashinsa na ƙarshe a lokacin da yake jinyarsa ta ajali.

Sayyida Alayka kamar yadda mijinta ke kiranta, ta kuma bayyana rayuwar soyayya tsakaninsu irin wadda ba ku saba ji ba.

A ranar Juma'a, 29 ga watan Nuwamba aka yi jana'izar shehin malamin, wanda ya rasu ranar Alhamis bayan gajeriyar jinya.

Ya rasu yana da shekara 100 da haihuwa, kuma an binne shi a masallacinsa da ke garin Bauchi.

Abba Auwalu ne ya ɗauka da kuma shirya bidiyon.

Hajiya Aisha Matar Sheikh Dahiru Bauchi