Ku San Malamanku tare da Sheikh Ɗahiru Bauchi

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Dahiru Usaman Bauchi
Lokacin karatu: Minti 1

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba 28 ga watan Yunin shekarar 1927 wanda ya yi daidai da 2 ga watan Al Muharram shekarar 1346 a garin Nafada jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.

Mahifinsa mutumin jihar Bauchi ne, yayin da mahaifiyarsa kuma 'yar jihar Gombe ce, kuma dukkanninsu Fulani ne.

Yana kuma da 'ya'ya sama da 80, wadanda a cikinsu wadanda suka haddace Alkur'ani sun kai 73 ko 74.

Malamin ya rayu a gaban mahaifinsa kuma ya haddace Alkur'ani a wurin mahaifinsa, kana ya tura shi ya shiga duniya don ya gyara tare da karo karatunsa.

A hirarsa da BBC a shirin Ku San Malamanku, malamin ya ce ya kuma samu nasarar kara fahimtar haddar Alkura'ani mai girma a wuraren da ya tafi neman karatun.

''Lokacin har na rika ji wasu mahaddata na kirana da Goni ko kuma Gangara, saboda haddace Alkur'ani mai girma,'' in ji shi.

..

Asalin hoton, Ɗahiru Bauchi/Family

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma ce mahaifinsa ya sake tura shi karo ilimi a garin Bauchi amma kuma neman ilimin bai yi tsawo ba saboda yana cikin karatun sai Allah ya bayyana sha'anin darikar Sheik Ibrahim Khaulak, inda daga nan ne ya shiga ciki ya kuma zama daya daga cikin almajiran Sheik Ibrahim Khaulak din.

Malamin ya kuma kara da cewa; ''Saura kadan in haddace Alkur'ani ina da shekara 13 amma sai muka shagala wajen noma da kiwo, don haka ban karasa haddacewa ba sai da na kai shekara 19 zuwa 20.''

Ya kuma ce babban malaminsa shi ne mahaifinsa, amma kuma ya ce ya soma karatu a hannun Malam Baba Sidi, da Malam Saleh, da Malam Baba Dan Inna.

Kana ya ce ya kuma je garin Zaria wajen su malam Abdulkadir nan ma ya taba karatu, kana ya je garin Kano inda ya sadu da manyan malaman Kano ya kuma yi karatu a wajen Malam Shehu Mai Hula, da Shehu Malam Tijjani, da kuma Shehu Atiku.