Yadda zamani ya sa ɗan'adam ya rage yawan aure

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, CrowdScience programme
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da ake ci gaba da samun manhajojin da ke haɗa ma'aurata marasa adadi, ake kuma samun bunƙasar soyayya tsakanin masoya, tambayar ko me ya sa ɗan'adam a ɗabi'arsa ba ya son haɗa aure da wani na ci gaba da kasancewa mai muhimmanci.

Alina, ƴar asalin Romania mazauniyar London, ta riƙa mamakin kanta bayan da ta samu kanta da kishi a auren mutumin da ke da aure, 'polyamory' - yanayin da ake samun mutum fiye da ɗaya suna soyayya da mutum guda, kuma kowa na sane da hakan.

"Ban jima da haɗuwa da mutumin da ke da aure da yawa ba, kuma shi kullum a haka yake,'' kamar yadda ta yi bayani.

''Ina son sanin: Me ya sa muka taƙaita da aure da mutum guda a al'ummarmu''?

Hanya ɗaya ta fahimtar hanyar juyin halittar mu ita ce ta nazarin makusantan danginmu na farko da kuma dabarun haihuwarsu.

"Goggon birrai kan yi mata da yawa - inda za ka samu biri guda da mata masu yawa,'' in ji Dakta Kit Opie, masanin ilimin yadda halittu suka faro a Jami'ar Bristol a Birtaniya

"Don haka ƴaƴan da ke cikin garken duk goggon biri guda ne mahaifinsu, amma mata daban-daban da ke cikin garken ne suka haifo su.

Amma wannan ba dabarar haihuwa ba ce mai inganci, in ji Dokta Opie, saboda yana haifar da yawan mutuwar jarirai.

"Kisan jarirai, wani mummuman yanayi ne mai ban tsoro a rayuwar goggon birrai ," in ji shi. "Yanayi ne da mijin biri ke kashe jariran garkensa da ba shi ne ubansu ba, ta yadda iyayensu mata za su samu juna biyu cikin hanzari. Wannan ba dabarar juyin halitta ba ce da za mu so yin koyi da ita."

Wasu goggan birrai ke rungumar juna a lokacin barbara a wani gandun daji da ke DR Congo a 2010.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Macen goggon biri kan yi barbara da maza da yawa a lokacin ɗaukar ciki ta yadda idan ta haihu mazan ba za su gane ba nasu ba ne, don kar su kashe mata jariri.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To amma ga wasu nau'ikan dabbobin masu kamanceceniya da ɗan'adam - kamar birrai nau'in 'chimpanzee' da 'bonobos' - matansu kan yi dabarun barbara masu yawa, don kawar da hankalin mazajensu.

Matan kan yi barbara da maza da yawa, a lokacin da suke barbara domin rage kisa ko cutar da ƴaƴansu.

Akwai yiwuwar daga haka ɗan'adam ya fara: maza da yawa kan sadu da mata da yawa. To amma hakan ya sauya kimanin shekara miliyan biyu da suka gabata.

"Dalilin hakan kuwa shi ne sauyin yanayi," in ji Dakta Opie.

"A ƙasashen Afirka kudu da hamadar sahara, inda kakanninmu suka rayu an samu bushewar ciyayi, inda wasu yankunan suka zama wurare masu bishiyoyi. Mutanen farko na buƙatar rayuwa cikin gungu domin kare kansu daga cutarwar namun daji. Kwakwale kan faɗaɗa tunani don yin hulɗa da waɗannan manyan ƙungiyoyi ko gungun-gungu masu rikitarwa don haka lokacin shayarwa ya tsawaita''.

To amma yayin da ake samun maza masu yawa a kowane gungu, ya zama da wahala a iya yin ɓad-da-bami game da juna-biyu.

"Haka kuma, matan na buƙatar saduwa da miji domin haihuwa. Daga nan ne suka koma mu'amala da mutum guda'', a cewar Masanin.

Dancing wedding cake figurines

Asalin hoton, Getty Images

Mu'amala da mutum guda ne hanya mafi kyau?

Dakta Opie ya ce an yi sauyin ne ba don hakan ya fi ba, sai don hakan ya fi zama masalaha.

Wani gida da ƴaƴansu biyu rugume da mahaifiyarsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Renon ƴaƴa da sarrafa tunaninsu, da kuma rashin girman ɗan'adam da wuri ya sa auren mutum guda ya zama mafi amfani ga ɗan'adam

Renon ƴaƴa da kaifafa tunaninsu cikin sauri na buƙatar cikakken lokacin duka iyaye, fiye da mahaifiya kaɗai.

Kodayake bincike ya nuna cewa mutanen farko sun fara ne da auren mace ɗaya, mutanen da suka zaɓi auren mace ɗaya sukan yi ƙoƙari su kasance da aminci ga abokin tarayyar juna.

"Akwai halittun da suka taƙaita kan mu'amala da abokin mu'amala guda a tsawon rayuwarsu, kuma ba sa cin amanar juna, amma kuma ba su da yawa,'' a cewar Dakta Opie.

"Wasu ƙarin halittun da ke kusanci da mu waɗanda ke mu'amala da mace ko miji guda su ne jajayen birrai da ake kira ''gibbons''. Amma su suna da bambanci da sauran nau'ikan saboda mazansu da matansu kan iya sanya idanu kan juna, ta yadda ba za su ci amanar juna ba''.

"Amma idan kana cikin gungu mai yawa kamar ɗan'adam inda ake samun maza da mata da yawa, yana da wahala kowa iya iya sanya idanu kan abokin auratayyarsa ta yadda wani zai gane idan ana cin amanarsa.''

Don haka auren mace ɗaya, a wannan ƙadami abu na ɗabi'a a dabarun rayuwa, wanda ya zo tare da ɗabi'a.

Abin da ke haifar da shaƙuwa

To me ke faruwa a ƙwaƙwalenmu idan mun fara soyayya ko a lokacin da muke ƙoƙarin riƙon amanar juna?

Sarah Blumenthal, ƙwararriya kan tunanin ƙwaƙwalwa, wadda ke karatun digirinta na uku a jamni'ar Emory da ke Amurka, ta nazarzi dabbobin prairie voles - ƙananan halittu da suka yi fice wajen jimawa da alaƙar juna, kamar na ɗan'adam.

halittun prairie voles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Halittun Prairie voles masu jimawa da alaƙar namiji da mace

Ba kamar ƴan'uwansu na jinsin vole ba, prairie voles suna da manyan sinadaran oxytocin da ke taimaka wa ƙwaƙwalwa rashin amincewa da tarayyar abokin zama.

Oxytocin - sinadari ne - ƙwaƙwalwa fitarwa a lokacin da gaggar jikin juna ya gogu.

"Idan muka yi gwajin sidabarin a ƙwaƙwalen prairie voles, ba za su iya ƙulla alaƙa mai ƙarfi ba, domin kuwa ba su ɓata lokaci mai tsawo tare da abokan hulɗarsu," in ji Blumenthal.

Wani mutum tare da ƙawayensu biyu mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amma wani sinadarin - dopamine - na iya kawo canje-canje a cikin sha'awar mu kann sabon abu tare da sadaukarwa.

Haka shi ma ɗan'adam na da irin wannan sinadari na oxytocin, wanda ke sanya ƙwaƙwalenmu gamsuwa da alaƙa mai ƙarfi.

Amma wani sinadarin - dopamine - na iya kawo canje-canje a cikin sha'awar mu kann sabon abu tare da sadaukarwa.

Mata masu maza da yawa

Duk da hujjar juyin halitta na auren mace ɗaya, al'adun ɗan adam koyaushe suna nuna tsarin dangantaka mai yawa.

Ƙwararriya kan ilimin halayyar dan'adam, Dr Katie Starkweather ta Jami'ar Illinois Chicago da ke Amurka ta tattara fiye da mata 50 masu auren fiye da miji guda a fadin duniya, kama daga Nepal da Tibet na Asiya zuwa sassan Afirka da Amurka.

Wasu maza biyu na sunbatar mace guda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Batun mace da auren miji fye da ɗaya ba shi da yawa kamar miji ya auri mace fiye da ɗaya.

Yayin da batun mace ta auri miji fiye da ɗaya ba shi da yawa sosai, kamar yadda miji ke auren mace fiye da ɗaya, Starkweather na ganin kuskure ne a ɗauke shi a matsayin abin da ba zai yiwuwa ba.

"Mata za su iya cin gajiyar tattalin arziki ta hanyar samun maza da yawa. Idan mijinki na farko ya mutu ko kuma ya kasance ba ya nan na dogon lokaci - kamar yadda ya faru ga wasu ƴan Arewacin Amurka - ya dace ku sami tsarin ajiyar kuɗi," in ji ta.

A wasu lokuta, auren mace fiye da guda na da amfani a tsarin zamantakewa.

"A halin rashin lafiya da mutuwa, wataƙila auren mace fiye da ɗaya zai taimaka wajen kula da yaran da mace ta mutu ta bari, saboda yaran sun riga sun saba da matar tun kafin rasuwar mahaifiyarsu, kuma hakan zai taimaki yaran'', in Starkweather.

Auren miji fiye da ɗaya

Ga Alina, zama da miji guda bai yi mata daɗi ba, a cikin dangantakar da ta gabata. Yanzu, a cikin zamantakewar maza da yawa, tana samun nishaɗi fiye da baya.

''Kishi tsakaninsu na iya zama da babban ƙalubale mai ƙarfi," in ji ta. "Amma a ɓangare na yawancin abin zai iya zuwa idan na ji kamar suna ɓoye maka wani abu, amma da zarar na fahimci cewa suna da gaskiya, hakan yana taimakawa wajen rage jin kishin."

Wasu maza tsaye sun juya baya tare da mace a tsakiyarsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ga wasu mutanen mace ta auri mij fiye da ɗaya na sa mace ta ci gajiyar tattalin arziki da ƴanci.

Ɗaya daga cikin abokin zamanta ya aminece da iƙirarin nata: "Zan iya cewa, kishi a zahiri ba shi ne babban batun ba, a yawan lokaci ƙoƙarin da ake ɗauka don kula da alaƙar lafiya da yawa na iya zama da ƙalubale."

Dukansu sun ce auren na da kima, "Babu wasu ƙayyadaddun ƙa'idodi," in ji Alina. "Hakan ya tilasta muku yin tattaunawa mai ƙarfi - kuma hakan ya sa dangantakarmu ta yi ƙarfi."

Don haka, a ɗabi'ance mu masu auren mace ɗaya ne? Amsar da alama ita ce e da kuma a'a.