BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hari kan ofishin shugaban ƙasar Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 3 ga watan Maris 2026.
Yadda ake takun-saƙa tsakanin El-Rufai da ICPC
Sa-in-sar ta ɓarke ne bayan da a ranar Litinin hukumar ta shigar da shi ƙara gaban babbar kotun tarayya da Abuja.
Yadda yaƙin Iran zai shafi farashin man fetur a Najeriya da duniya
Wani mai magana da Iran ya yi gargadin cewa za a cinna wuta a kan duk jirgin ruwan dakon man fetur da ya yi yunƙurin bi ta mashigar.
Mutum shida da za su iya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei
Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin mutum uku da aka kafa ya fara aiki a asirce kan wani jerin sunayen mutanen da ake tunanin za su iya cike gurbin na Ayatollah Khamenei.
Yadda APC da ADC ke sabunta rajistar mambobinsu
A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam'iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026.
Ko ya kamata a riƙa zubar da ruwan da aka tafasa shinkafa?
Shinkafa na ɗaya daga cikin abincin da aka fi amfani da shi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Mun shirya wa dogon yaƙi da Amurka - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 2 ga watan Maris 2026.
Me ƙasashen Afirka suka ce kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila?
Ƙasashen Afirka na ci gaba da yin martani kan yaƙin da ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Iran da kuma Isra'ila.
Nafilolin da ake son mai azumi ya riƙa yi a watan Ramadan
Sallolin dare na daga cikin ibadun cikin dare da musulunci ya kwaɗaitar da ƙarfafa gwiwar yinsu, musammana a lokacin watan azumin Ramadan.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 3 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 3 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 3 Maris 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 3 Maris 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Arsenal ta ci gaba da riƙe wuta a saman teburin Premier
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Maris 2026.
Ko Barcelona za ta iya farke cin da Atletico ta yi mata?
A kakar bana, Barcelona ta lashe dukkan wasanninta na gida tun bayan da ta koma taka leda a filin wasa na Spotify Camp Nou.
Arsenal na zawarcin Goretzka, Real Madrid na bibiyar Schlotterbeck
Mai tsaron ragar Liverpool Alisson yana cikin jerin 'yan wasan da Inter Milan da Juventus ke nema, Manchester United na son Bruno Guimaraes na Newcastle, 'yan wasan Tottenham na fuskantar rage albashin da za a biya su.
Rashford ya amince a rage albashinsa don raba gari da Man U, Chelsea ta shiga zawarcin Nunez
Chelsea ta shiga takarar neman dan wasan gaba na Al-Hilal Darwin Nunez, Manchester City za ta yi babban tayi ga mai tsaron baya na Newcastle United Tino Livramento, sannan Crystal Palace ta kuduri aniyar ci gaba da rike golanta Dean Henderson.
Champions League: Madrid da City, Barca da Newcastle, Arsenal da Bayer
Za a buga fallen farko na wasannin ne ranakun 10 da kuma 11 ga watan Maris, sannan a buga falle biyu na wasannin a ranakun 17 da 18 ga watan na Maris.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ku aiko mana girke-girken Ramadan na 2026
Ku sanya bidiyon abincin buɗe-baki na musamman da kuka haɗa wa iyalanku ta yadda wasu za su iya kallo su kwaikwaya.
Yadda zamanin Ayatollah Khamenei na fiye da shekara 30 ya zo ƙarshe
Gidan telebijin ɗin Iran ya tabbatar an kashe Jagoran Ayatollah Khameinei a harin Isra'ila da Amurka
Wane ne Alireza Aarafi, shugaban kwamitin zaɓen sabon Ayatollah a Iran?
Alireza na cikin mutanen da Ali Khamenei ya amince da su kuma yana cikin na kusa da shi. Wannan karɓuwa da ya samu a wurin jagoran addinin ta sanya darajarsa ta riƙa ɗagawa, har ya kai ga inda ake ambaton sunansa a matsayin wanda zai iya gadon Ali Khamenei.
'Mutane fiye da 300,000 aka raba da muhallansu a jihar Neja'
A baya-bayan nan dai ana samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a Najeriya duk da isowar sojojin Amurka a arewacin kasar don tallafawa dakarun Najeriyar wajen kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.
Yadda aka gano ƙasusuwan dabba mai shekara miliyan 100 a Nijar
A karkashin tsananin zafi da ake yi a yankin na Sahara, masu binciken suka gano sauran ƙasusuwan dabbar ta dinosaur, wadda ake ɗauka a matsayin wata dabba ta daban a tsawon ƙarni.
Yadda Amurka da Isra'ila suka kwashe watanni suna kitsa kashe Ayatollah Khamenei
Ƴan awanni kaɗan kafin kai hari kan Ayatollah Amurka ta samu wani bayanin sirri mai matuƙar muhimmanci.
Mene ne hukuncin ɗanɗana abinci ga mai azumi?
Azumin Ramadana lokaci ne da al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke zage damtse domin yin ayyukan da za su inganta imaninsu tare da kyautata wa ƴan uwa da abokan arziki duk domin neman tsira da samun lada.
Matakan da ake bi wajen zaɓen sabon Jagoran Addinin Iran
Sashe na 111 na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa, daga lokacin rasuwar jagoran addini zuwa lokacin da Majalisar Masana za ta sanar da sabon Jagora, Majalisar wasu mutane guda uku ne za su tafiyar da ayyukan ofishin Jagora.
Iran ta naɗa shugaban kwamitin riƙon-ƙwarya na ƙasar
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/03/2026
Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 28/02/2026
Béhanzin: Sarkin Afirka da tarihin duniya ba zai manta da shi ba
Dubban masu yawon buɗe ido ne suke zuwa ƙasar Benin domin gane wa idonsu tarihi da al'adun mutanen ƙasar wadda a baya ake kira da Jamhuriyar Dahomey.
Matar da ke fama da cutar da ke sanya mutane tsukewa
Rayuwar wata mata da ta ce ya kusa zuwa ƙarshe jim kaɗan bayan gano tana ɗauke da wani nau'in ciwon hanta, ta faɗi labarinta don ƙarfafa wa mutane gwiwar cewa kada su sare.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.
































































