Sakamakon wasannin Champions League na ranar Talata

Ƙwallaye biyu da Jules Koundé ya zura ne suka bai wa Barca nasara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwallaye biyu da Jules Koundé ya zura ne suka bai wa Barca nasara
Lokacin karatu: Minti 5

An ɓarje gumi a gasar Champions League a karawar cikin rukuni, fafatawa ta shida-shida a ranar Talata.

Daf ake da shiga zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai da ƙungiya 16 za su kai zagayen gaba.

Har yanzu Arsenal ce ta farko a kan teburi da maki 15 daga karawa biyar, duk da nasarar da Bayern Munich ta yi kan Sporting da ci 3-1, inda ƙwallaye suka raba ƙungiyoyin biyu na saman teburi.

Sakamakon wasannin ranar Talata:

  • Atalanta 2 - 1 Chelsea
  • Bayern Munich 3 - 1 Sporting
  • Barcelona 2 - 1 Frankfurt
  • Inter Milan 0 - 1 Liverpool
  • Kairat Almaty 0 - 1 Olympiakos
  • Monaco 1 - 0 Galatasaray
  • PSV Eindhoven 2 - 3 Atletico Madrid
  • Tottenham 3 - 0 Slavia Prague
  • Union St Gilloise 3 - 3 Marseille

Bayern Munchen 3-1 Sporting

Lennart Karl ne ya zura ƙwallo ta biyu a wasan ranar Talata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lennart Karl ne ya zura ƙwallo ta biyu a wasan ranar Talata

Bayern Munich ta sake nuna ƙarfinta a gasar ta Champions league ranar Talata bayan inda ta doke Sporting da ci 3-1.

Wannan na nufin cewa Bayern ba ta yi rashin nasara ba a wasa biyar da Sporting a baya-bayan nana, wadda ta ci huɗu da canjaras ɗaya da cin ƙwallo 13 aka zura mata biyu.

Wasa biyu aka ci Bayern daga 31 a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Portugal da lashe 20 daga ciki. Har yanzu ba a doke ta a gida a wasa 15 da lashe 13 daga ciki.

Harry Kane ya zura ƙwallo 16 a raga a wasa 15 a gida a Bayern Munich a Champions League.

Wasa ɗaya Sporting ta ci daga 17 a gasar zakarun Turai a karawar waje da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus aka doke ta 14 daga ciki.

Karawar da ta yi nasara ita ce da ta doke Eintracht Frankfurt 3-0 a Champions League zagayen cikin rukuni a Satumbar 2022.

Kairat Almaty 0 - 1 Olympiacos

Kairat Almaty ba ta ci wasa ko daya ba daga karawa takwas a gasar zakarun Turai, aka doke ta shida daga ciki bayan kashin da ta sha a hannun Olympiacos da ci 0-1..

Monaco 1-0 Galatasaray

Ƙungiyoyin sun fuskanci juna a gasar zakarun Turai sau bakwai, inda a yanzu Monaco ta yi nasarahudu, Galatasaray ta ci biyu.

Wasan baya-bayan nan da suka fafata shi ne a 2000/01 a karawar cikin rukuni a Champions League, Galatasaray ta yi nasara 3-2 a Turkiya da kuma Monaco ta ci 4-2 a Faransa.

Atalanta 2-1 Chelsea

Cole Palmer

Asalin hoton, Getty Images

Atalanta ta doke Chelsea 2-1 a wasan na ranar Talata.

Dama dai Atalanta ta yi rashin nasara ɗaya ne kawai daga wasa tara a gasar zakarun Turai a cikin rukuni a gida da cin huɗu da canjaras huɗu.

Chelsea ta yi nasara a wasa uku baya a gasar zakarun Turai da ƙungiyoyin Italiya ba tare da an zura mata ƙwallo ba a raga - yayin da ta yi nasara 13 daga fafatawa 15 da cin ɗaya da canjaras ɗaya a zagayen cikin rukuni ko lik.

A wasa na biyar-biyar a cikin rukuni da ta doke Barcelona, Estavo mai shekara 18 da kwana 215 ya zama matashi na uku da ya zura ƙwallo a raga a wasa uku a jere a Champions League, bayan Kylian Mbappe (Mai shekara 18 da kwana 113 a lokacin).

Barcelona 2-1 Frankfurt

...

Asalin hoton, Getty Images

Frankfurt ce ta fara zura ƙwallo a wasan kafin zuwa hutun rabin lokaci, sai dai lamarin ya sauya cikin ƙanƙanin lokacin bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Dan wasa Kounde ne ya zura ƙwallo biyu cikin minti hudu bayan minti biyar da take wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Hakan na nufin Barcelona ta ci wasa 16 daga karawa 20 a gasar zakarun Turai a gida da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus da rashin nasara huɗu.

Inter Milan 0-1 Liverpool

Dominik Szoboszlai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dominik Szoboszlai

Liverpool wadda ta je Milan ba tare da ɗan wasanta Mohamed Salah ba, ta samu nasara duk da faɗi-tashin da take fama da shi a wannan kaka.

Ƙungiyoyin nan sun fuskanci juna karo shida a gasar zakarun Turai, inda a yanzu Liverpool ta yi nasara biyar, Inter Milan ta ci biyu.

PSV Eindhoven 2-3 Atletico de Madrid

Julián Alvarez

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa PSV ba ta yi rashin nasara ba a karawa huɗu na baya a gasar zakarun Turai da ta kara da ƙungiyoyin Sifaniya ba, Atlitico ta samu galaba a kanta ranar Talata da ci 2-3.

Ƙungiyar ta Netherlands ta ci ƙwallo a kowanne wasa 17 daga 18 a Champions League karawar cikin rukuni - haka kuma ta ci ƙwallo 17 a karawa biyar baya a gida a gasar ta zakarun Turai.

Tottenham 3-0 Slavia Praha

Mohammed Kudus na ƙungiyar Tottenham na muranar ƙwallon da ya zura tare da abokin wasan Richarlison

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Kudus na ƙungiyar Tottenham na muranar ƙwallon da ya zura tare da abokin wasan Richarlison

Fenariti biyu da cin gida daya ne suka bai wa Tottanham galaba a karawar ta Talata a birnin Landan.

Tottenham ta yi wasa biyar ke nan yanzu da Slavia Praha ba tare da rashin nasara ba da cin hudu daga ciki, kuma a karawa bakwai da ta fafata da ƙungiyoyin Jamhuriyar Czech ta ci wasa shida da canjaras biyu.

Ƙungiya Dukla Praha ce kaɗai daga Jamhuriyar Czech ta yi nasara a kan Tottenham 1-0 European Cup zagayen kwata fainals a Fabrairun 1962.

Wasa biyu Slavia Praha ta ci daga 16 da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila aka doke ta 11 daga ciki - kuma ba ta yi nasara ba daga fafatawa 17 a Champions League aka doke ta 10 daga ciki, tun bayan da ta yi nasara 2-1 a gida a kan Steaua a Satumbar 2007.