Yaushe ne aka fara zazzafar hamayya tsakanin Madrid da Barcelona?

Asalin hoton, FC Barcelona
- Marubuci, Mary Josieh Al-Qazi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Lokacin karatu: Minti 8
Real Madrid ta yi nasara a karawar El Classico ta farko a wannan kakar bayan ta doke Barcelona da ci 2-1. Kwallayen da Kylian Mbappe da Jude Bellingham suka zura ne suka bai wa Real nasara, a yanzu kungiyar ta bai wa Barcelona tazarar maki biyar a kan tebur.
Real Madrid ta yi rashin nasara a wasanni hudu da ta kara da Barcelona a kakar wasa da ta gabata, sai ga shi a karon farko karkashin jagoranci mai horaswa Xabi Alonso Real ta lallasa Barcelona a wani wasa da ya yi zafi cike da takaddama har da bayar da jan kati guda biyu, kamar sauran wasannin El Classico na baya.
Bayan kammala wasan, Dani Carvajal ya je domin ja wa Lamine Yamal kunne game da kalaman da Yamal din ya yi a shafin sada zumunta, lamarin da ya haifar da yamutsi tsakanin ‘yanwasan bangarorin biyu.
To amma tun yaushe ne wannan karawar da ke jan hankali fiye da kowanne wasa, baya ga wasan karshe na gasar Champions League ya zama mai muhimmanci ga masoya kwallon kafa? Ko kuma a ce daga ina ne adawar da ke tsakanin wadannan kungiyoyi biyu ta samo asali?
A ranar 13 ga watan Mayun 1902, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, wadda aka kafa shekara biyu da rabi baya, ta isa birnin Madrid domin karawa da kungiyar birnin mai suna Madrid, wadda ita kuma aka kafa ta wata biyu kafin lokacin.
A wannan lokaci babu wanda ya san cewa wannan wasa ne zai zamo farkon wata ”hamayya mafi zafi” a tarihin kwallon kafa a duniya.
Ga kungiyar ta Catalonia, karawar ba wata aba ba ce face “wasa irin wanda ta saba yi”, wanda idan ta yi nasara zai ba ta damar karawa da kungiyar Athletic Bilbao, wadda ita ce kungiya mafi kwarewa a kasar Spain a wancan lokaci.
Barcelona ta ziyarci Madrid ne a matakin wasan kusa da karshe na cin kofin “Copa Coronacion”, wanda aka tsara domin murnar nadin sarautar Alfonso XIII bayan ya cika shekara 16 da haihuwa (shekarun balaga a hukumance) kuma a lokacin ne ya karbi aikin Sarkin Spain a hukumance.
Wannan ne karo na farko da aka kara tsakanin kungiyoyin kwallon kafa daga shiyyoyi daban-daban na kasar Spain.
"Gasa mafi suna"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu matasa baki da ke zaune a birnin ne suka kafa kungiyar Barcelona a shekarar 1899, bayan karuwar samun karbuwar kwallon kafa da sauran wasannin motsa jiki na Birtaniya a kasashen Turai.
Gabanin karawarta da Real Madrid, Barcelona ta buga wasanni a gasar Macana, wata gasa ta kungiyoyin kwallon kafa na yankin Catalan tsakanin shekarar 1900 zuwa 1903.
Ita kuwa Real Madrid wani injiniya dan Spain mai suna Julian Palacios ne ya kafa ta. Shi ne shugaban kungiyar na farko tsakanin 1900 zuwa 1902.
A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1902 Palacios ya mika ragamar kungiyar ga Juan Padros, wanda shi ne ya samar da kungiyar a hukumance.
A lokacin da aka buga wasan El Classico na farko, Barcelona na kunshe ne da yan wasa yan asalin kasar Switzerland da dan kasar Jamus daya da kuma ‘yan kasar Ingila uku yayin da ita kuma Madrid (wadda ta zama Real Madrid a shekarar 1920) tana kunshe ne da danwasa daya tal daga wata kasa ta ketare a cikin tawagarta..
A wannan lokaci Madrid ba ta goge wajen buga wasanni ba, domin kuwa ‘yan wasannin da ta buga ba su wuce na sada zumunta ba da wasu kungiyoyin da ke babban birnin.
Wasan kwallon kafa a filin sukuwa

Asalin hoton, Getty Images
An fara wasan ne da karfe 11 na safe a filin da ake kira Hipodromo de la Castilla da ke birnin Madrid, fili mai dimbin tarihi wanda a nan ne aka gina filin wasa na Santiago Bernabeu da Madrid ke amfani da shi a yanzu.
Filin ya kasance mai girma kuma an yi amfani da kashin shanu ne a matsayin taki, wanda zai iya janyo cutuka.
Arthur Johnson, dan wasa daya tilo daga ketare na kungiyar Madrid shi ne ya ci kwallo ta farko a wasan, kuma shi ne dan wasan da ya ci kwallo ta farko a tarihin karawar El Clasico, duk kuwa da cewa Barcelona ce ta lashe wasan da ci 3-1.
Wannan nasara ce ta kai kungiyar Barcelona zuwa wasan karshe inda kuma ta lashe kofin bayan doke kungiyar Athletic Bilbao. Gasar ita ce ta farko, wadda a yanzu aka sani da Copa del Rey (Spanish Cup).
Farkon rashin jituwa

Asalin hoton, Getty Images
Hamayya tsakanin kungiyoyin biyu na Spain ta ci gaba a shekarun da suka biyo baya, kuma a tsakanin shekarun 1902 da 1916 Madrid da Barcelona sun kara sau bakwai, inda Barcelona ta yi nasara a wasa biyar sannan aka yi canjaras a biyu.
To sai dai an fara zazzafar hamayya da adawa da juna ne tsakanin kungiyoyin biyu bayan zargin alkalin wasa da nuna rashin adalci a karawa ta takwas tsakanin su, inda aka buga wasanni gida da waje.
Barcelona ta lashe karawa ta farko (ranar 26 ga watan Maris, 1916) da ci 2-1, sai dai Madrid ce ta yi nasara a wasa na biyu da ci 4-1 bayan mako daya. A wancan lokacin ba a la’akari da yawan kwallayen da aka zura saboda haka ne aka buga wasa na uku a ranar 13 ga watan Afrilu domin tantance kungiyar da ta yi nasara.
An buga wasan ne a filin Campo de O’Donnel a birnin Madrid, inda tsohon dan wasan Madrid Jose Angel Braundo ya zama alkalin wasa.
Ya bai wa Madrid bugun fenariti uku sannan ya danne wa Barcelona kwallo daya da ta zura.
A karshe dai an tashi wasan canjaras 6-6 a filin wasa na Santiago Bernabeu.
Sai aka sake buga wasan, inda har wa yau Angel Braundo ne ya hura usur, kuma ya sake bai wa Madrid bugun fenariti, lamarin da ya harzuka yan wasan Barcelona wadanda suka fice daga fili domin nuna adawa da matakin.
Real Madrid ta kai wasan karshe na gasar sai dai kungiyar Bilbao ta doke ta da ci 4-0 a wasan da aka buga a birnin Barcelona. Bayanai sun nuna cewa an yi wa ‘yanwasan Madrid ruwan duwatsu a lokacin da suke ficewa daga filin wasan.
Ya aka yi El Clasico ke jan hankali sosai?

Asalin hoton, Getty Images
Gasar kungiyoyin kwallon kafa na Spain, wadda yanzu ake kira La Liga, an kaddamar da ita ne a shekara ta 1929, inda aka rika karawa a kai a akai tsakanin kungiyoyin biyu.
A tsakanin shekarun 1950 da 1960, Real Madrid ta yi karfi sosai, inda take tinkaho da kwararrun yanwasa irin su Alfredo Di Stefano na kasar Argentina da Spain Da Ferenc Puskas na kasar Hungary, inda kungiyar ta lashe kofin gasannin nahiyar Turai sau biyar a jere, daga shekara ta 1956.
Hamayya tsakanin Real Madrid da Barcelona ta kara zafi ne sa’ilin da Barcelona ta samu jagorancin Johan Cruyff a tsakiyar shekarun 1970 da kuma isar dan wasa dan asalin kasar Jamus Paul Breithner kungiyar Madrid, tare da wasu yanwasan Spain kamar Vicente del Bosque da Guy Benito.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin biyu sun ci gaba da jan hankalin shahararrun ‘yanwasa daga sauran kasashen Turai da kuma yankin Kudancin nahiyar Amurka kamar su Argentina da Brazil.
Real Madrid ta janyo ‘yanwasa daga kasashen da ke tsallaken Spain daga shekarun 2000 zuwa 2006, kamar irin su Luis Figo, da Zinedine Zidane da Ronaldo da David Becham
Ita ma Barcelona ta sayi manyan ‘yanwasa irin su Ronaldinho da Samuel Eto, Thierry Henry da Yaya Toure, wadanda suka kara haskaka gasar da kuma janyo mata masoya.

Asalin hoton, Getty Images
To amma ‘yanwasan da suka sa hamayyar El Clasico ta kai kololuwa su ne Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, ‘yanwasa biyu da suka kwashe shekaru suna ba ni in ba ka da kyautar Ballon d’Or a tsawon shekaru.
Baya ga su akwai kuma ‘yanwasa kamar Xavi da Iniesta da Gerrard Pique, Segio Ramos, Luka Modric da Karim Banzema wadanda su ma suka taka rawa.
Karawar El Clasico da ta fi samun masu kallo ita ce wadda aka yi a ranar 23 ga watan Afrilun 2017: wasan da aka nuna shi a gidajen talabijin a sama da kasashe 185.
Ya zuwa yanzu, kungiyoyin biyu sun kara a tsakaninsu sau 262: Real Madrid ta yi nasara sau 106, Barcelona kuma ta yi nasara a wasa 104 yayin da aka tashi canjaras a wasa 52.
Wasan El Clasico da aka fi zura kwallaye a tarihi shi ne lokacin da Madrid ta yi nasara kan Barcelona da ci 11-1 a ranar 13 ga watan Yunin 1943, wasan da ake alakantawa da siyasa kuma ake dora laifi kan shugaban kama karya na Spain Francisco Franco.
An bayyana cewa jami’an tsaron Franco ne suka yi wa ‘yanwasan Barcelona barazana gabanin wasan, lamarin da ake ganin shi ne ya haifar da sakamakon mai ban mamaki.
Wannan sakamako ya taba kimar Madrid, kuma tun daga wancan lokaci ne magoya bayan Barcelona ke yawan sukar Madrid, wadanda ke kiran Madrid din “kungiyar gwamnati”.
A shekarar 2012, dan jaridar Birtaniya Sid Lowe ya tattauna da Fernando Arquilla, wanda shi ne dan wasa na karshe da ke raye a cikin wadanda suka buga wannan karawar. Arquilla, wanda shi ne gola na biyu na Barcelona a wancan lokacin ya bayyana cewa wani jami’in gwamnati ya je dakin da suke canza kaya gabanin wasan.
“Wani babban jami’in dansanda, ina ganin daga cikin dakarun tsaron kasa yake.”
“Abin da ya fi tsaya min a rai shi ne dubban usur da ke a hannun magoya bayan Madrid, da yadda suka sa mana matsi da tsoro.
Magoya bayan Barcelona sun ce dansanda sirri na Franco ne ya tsorata ‘yanwasan, sai dai har yanzu ba a tabbatar da wannan zargi ba.
Sakamakon wannan wasan har yanzu ya zama tabo ga kungiyar Real Madrid.
A shekarar 2023, Barcelona ta fada cikin wata badakala ta zargin bai wa tsohon mataimakin shugaban kwamitin alkalan wasa na Spain kudi Yuro miliyan 8.4.
Shugaban kungiyar Barca, Juan Laporta ya yi ta kokarin wanke kungiyarsa daga batun ta hanyar dora laifi kan Madrid, inda ya ce Real Madrid ce ”kungiyar gwamnati”, tare da cewa alkalan wasa ne suke mara wa kungiyar baya a tsawon shekaru 70 da suka gabata.
A matsayin martani, Real ta fitar da wani bidiyo da ke nuna lokacin mulkin Franco, inda ta nuna cewa Barcelona ce ta fi cin ribar gwamnati a wancan lokacin.










