Faɗi-tasahin da Dembele ya sha kafin lashe Ballon d'Or

Ousmane Dembele ya sharɓi kuka bayan lashe Ballon d'or ranar Litinin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ousmane Dembele ya sharɓi kuka bayan lashe Ballon d'or ranar Litinin
Lokacin karatu: Minti 6

Danwasan ƙasar Faransa da PSG, Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d'Or ta shekara ta 2025.

An bayyana ɗan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a ɗakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a ƙasar Faransa.

Ballon d'Or kyauta ce da akan bai wa ɗan wasan da ya burge a kowace shekara, inda akan yi la'akari da gudunmawar da ɗanwasan ya bayar ga ƙungiya da kuma ƙasarsa.

Tun farko an fitar da jerin ƴanwasa 30 cikin waɗanda ake sa ran za su lashe kyautar.

Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Bayan shafe wani lokaci na rayuwarsa ta kwallon ƙafa yana faɗi-tashi da raunuka, da zaman benci da kuma zargin rashin tarbiyya, Ousman Dembele mai shekara 28 ya samu nasarar lashe kyautar Ballon d'Or, abin da ya daɗe yana fata.

A lokacin da yake gode wa iyalinsa saboda taimakon da suka bayar wajen samun nasarasa, Dembele ya fashe da kuka, wata alama da ta nuna ya tuno irin gwagwarmayar da ya sha.

Rawar da Dembele ya taka a kakar wasa ta 2024-25 ta taimaka wa ƙungiyarsa wajen lashe kofuna uku: Ligue 1, da Coupe de France a Faransa sai kuma kuma gasar zakarun Turai ta Champions League, sannan kuma ƙungiyar ta kai har wasan ƙarshe na gasar kofin duniya na ƙungiyoyi.

Ya ci ƙwallo 35 sannan ya taimaka aka zura 14 a dukkanin gasanni duk kuwa da cewa a farkon kakar da ta gabata bai fara da ƙarfinsa ba, amma sai ga shi a ƙarshen kakar ya zama ɗan wasan gaba da ya fi taka rawar gani daga farkon shekarar nan idan aka duba alƙaluma.

Ya doke ƴan wasa kamar Mohamed Sallah, wanda ya fi kowa taka rawa wajen zura ƙwallo a manyan gasanni biyar na nahiyar Turai, Kylian Mbappe na Real Madrid wanda ya fi zura ƙwallo da kuma matashi mai tashe Lamine Yamal na Barcelo da takwaransa Rahinha.

Sauyin lamarin Dembele ya fara ne daga kungiyar Barcelona, shekaru kadan kafin ya koma PSG, lokacin da ya fara sauya yadda yake tafiyar da rayuwarsa. Daga nan kuma sai PSG ta ba shi dama.

Tafiyar Mbappe daga PSG zuwa Madrid – wani abu da aka yi tunanin zai sanya Mbappe ya kai ganiyarsa ta ƙwallo a matsayin ɗan wasa mafi tashe a duniya – abin mamaki sai lamarin ya zama akasin haka, lokacin da mai horas da PSG Luis Enrique ya shaida wa Dembele cewa, 'yanzu muna sa ran ƙwallaye daga gare ka, saboda haka dole ka dage'.

Yadda tafiyar Mbappe ta ɗaukaka Dembele

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Agustan 2023 ne PSG ta sayi Mbappe kan kudi fam miliyan 43.5 kacal, inda ya zura ƙwallo 6 ya taimnaka aka zura 14 a kakar da PSG ta lashe kofin lig ɗin Faransa.

A wannan lokaci tauraruwar Dembele ba ta haskawa, yayin da shi kuwa Mbappe ya zura ƙwallo 44 a dukkan gasanni, kuma kakar ce mafi kyawu gare shi a tsawon kaka bakwai da ya yi a PSG, sai dai kuma ita ce kakarsa ta ƙarshe, domin daga lokacin ne ya tafi Madrid.

Sai aka sauya salo, PSG na neman mutumin da zai karbi tuta. Sai aka tura Dembele gaba.

Ya karɓi aikin hannu bibbiyu. Taka rawar da ya yi wajen saka ƙwallaye 51 ya sa ƙoƙarin da ya yi a kakar ya nunca fiye da sal biyu, sannan ƙwallo 35 da ya jefa a raga a kakar sun ɗara waɗanda ya jefa gabanin kakar da guda 21.

Wasu daga cikin tawagar masu horar da PSG sun faɗa masa cewa idan ya yi ƙoƙarin amfani da damarmakinsa to kuwa lallai zai kai ga nasarar ƙungiyar sannan shi ma zai samu yabo. A taƙaice dai ya kamata ya fifita zura ƙwallo da kansa a maimakon taimakawa a ci.

Daga nan sai Dembele ya ɗauki wadannan shawarwari kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Yanzu a mafi yawan lokuta yana taka rawa ne kamar lamba 9.

Raunuka, rashin tarbiyya da rashin tabbas – mene ne ya canza?

Idan aka ce tafiyar Mbappe ce kawai ta share masa fagen wannan nasara, wannan zai zama kuskure, duk da dai hakan ya taimaka.

Duk da cewa bai samu rauni ba lokacin da yake wasa a ƙungiyoyin Rennes da Dortmund, ya samu rauni sau 14 a Barcelona tare da kwashe kwanaki 784 yana kann benci.

Damuwar da ake da ita game da ɗabi'unsa da kuma ƙwarewa ta sanya aka nemar masa masu dafa abinci daban na musamman.

Yawan shafe dare yana buga bidiyo game ya Sanya shi yana yawan yin latti zuwa wurin atisaye, inda ya zama ɗanwasan da ƙungiyar ta fi lafta wa tara kan zuwa latti a shekarun nan.

Sai dai duk da haka a duk lokacin da yake da lafiya ƙwazon da yake nunawa a fili ta nuna cewa yana da basira irin wadda Barcelona ke so.

Wane sauyi aka samu?

Mutanen da suka san shi – waɗanda ƙalilan ne – sun ce ya sauya tun bayan auren matarsa Rima, ƴar Moroko, a watan Disamban 2021, inda jim kadan bayan haka ya samu ɗa.

Auren nasa ya bai wa mutane da dama mamaki, musamman abokan wasansa, waɗanda ba su taba tunanin yana budurwa ba.

Saboda haka sauyawar rayuwarsa ta fara ne shekara biyu kafin barin sa Barcelona, lokacin da hankali y azo masa.

Ya riƙa samun sahwarwari da kulawar ƙwararru, sannan kuma tare da hankalin da ya shige shi bayan samun ɗa, sai Dembele ya sauya yadda yake kallon rayuwa.

Ya fara ganin amfanin cin abinci yadda ya kamata, inda ya dauki mai taimaka masa wajen zaɓen abin da zai ci.

A tsawon lokaci masoya ƙwallon ƙafa sun yi amannar cewa PSG za ta iya lashe gasar zakaru ta Champions League ne tare da taimakon ɗaya daga cikin jajirtattun ƴan wasan Faransa. Kuma sun yi tunanin cewa jajritaccen ɗan wasan na Faransa zai zama gwarzon duniya.

Haka ne, to amma akasin tunaninsu, ba Mbappe ba ne, Dembele ne wanda a yanzu ya sauya rayuwarsa.

Ƙwazon da Dembele ya nuna

Dembele

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Dembele ya buga wasa 53 a kakar bara, inda a ciki ya taka leda na minti 3,483.

Ɗan'wasan na Faransa na zura ƙwallo 35, sannan ya taimaka aka ci ƙwallo 14 a kakar baki ɗaya.

Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon ƙungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi.

Ya zura ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya ƙarƙare gasar a matayin wanda ya fi zura ƙwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon ɗan'wasan gasar.

Haka kuma shi ne gwarzon ɗan'wasan gasar Champions League, inda ya zura ƙwallo takwas, sannan ya taimaka aka ci shida.

Ɗan asalin ƙasar Faransa, Dembele ya nuna bajinta a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi, inda ya zura ƙwallo a ragar Bayern Munich da Real Madrid a wasannin zagaye na biyu.

Lamine Yamal (Barcelona)

Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Lamine Yamal ya zo na biyu a kyautar, bayan da ya lashe ta gwarzon matashin ɗanwasan kyautar a 2025.

Yamal ya buga wasa 55, inda a ciki ya yi wasa na minti 4,548, sannan ya zura ƙwallo 18, ya kuma taimaka aka ci ƙwallo 21.

Ɗan'wasan mai shekara 18 yana cikin zaratan waɗanda suka taimaka wa ƙungiyar Barcelona ta lashe kofuna guda uku - La Liga da Copa del Rey da Supercopa de Espana.

Ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasan La liga a watan Satumba, sannan yana cikin gwarazan ƴan'wasan gasar La liga da Champions League.

Ya nuna bajinta a wasan kusa da ƙarshe tsakanin Faransa da Spain, inda ya zura ƙwallo biyu a ragar Faransa, duk da ƙasarsa ce ta yi rashin nasara.

Jadawalin ƴanwasan daga na 1 zuwa na 10

Waɗanda suka yi nasara daga na 1 zuwa na 10