Matasa 10 da za su haska a Champions League a bana

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Desire Doue yana daga cikin taurarin matasa da suka haska a kakar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai da ta gabata, yayin da ya taimaka wa ƙungiyar Paris St-Germain ta lashe gasar zakarun Turai a karon farko.

Haka kuma matashi Lamine Yamal ya taka rawar gani a Barcelona, inda ya kasance cikin matasan da suka haska a kakar da ta wuce.

To sai dai waɗanne matasa ne za su taka rawar gani a gasar ta bana?

Za a fara wasannin farko a Champions League a bana daga ranar Talata da Laraba da Alhamis a makon nan.

BBC ta zaƙulo ƴan wasa 10 da ake sa ran za su yi abin a zo a gani a gasar ta zakarun Turai ta Champions League.

Vasilije Adzic (Juventus)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: Tsakiya

Ƙasa: Montenegro

Vasilije Adzic ya koma Juventus ne kan kwantiragin kaka uku a shekarar 2024 bayan da ya taimaka wa Buducnost Podgorica ta lashe gasar lig a kasar a kakarsa ta farko yana ɗan shekara 16.

Ya buga wa Juventus wasa tara a 2024-25, ciki har da wasa ɗaya da ya yi a gasar zakarun Turai, kuma ya buga yi Club World Cup a karawar da Manchester City ta yi nasara ranar 26 ga watan Yuni a Amurka.

Tuni Adzic ya wakilci kasarsa, inda ya zura kwallo a wasansa na farko ranar 9 ga watan Yuni a wasan da suka tashi 2-2 da Armenia.

Jobe Bellingham (Borussia Dortmund)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: Tsakiya

Kasa: Ingila

Kamar yadda yayansa Jude ya yi, Jobe Bellingham ya bar Ingila ya koma Borussia Dortmund daga Sunderland a bana, bayan da ya ba da gudunmuwar da ta samu gurbin shiga Premier League daga gasar Championship.

Jobe Bellingham, wanda ƙungiyar Jamus ta saye shi kan fam miliyan 27, ya wakilci matasan Ingila ƴan kasa da shekara 21, zai buga wa Dortmund wasan Champions League a bana a Ingila da Manchester City da kuma Tottenham

Claudio Echeverri (Aro a Bayer daga Man City)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: Ɗan gaba mai kai hari/gefe

Kasa: Argentina

Magoya bayan Manchester City za su so ganin rawar da Claudio Echeverri zai taka, bayan da zai yi mata wasannin aro zuwa karshen kakar bana.

Kuma Manchester City ba ta da damar kiran ɗan wasan a watan Janairu domin ya koma Etihad da taka leda har sai an kammala kakar nan.

Echeverri ya koma City kan fam miliyan12.5m a Janairun 2024, amma sai ya ci gaba da zama a matakin aro zuwa karshen kakar nan a River Plate.

Ya fara buga Premier League a wasan karshen kakar 2024-25, ya kuma canji ɗan wasa a FA Cup da Crystal Palace ta doke City.

Ya fara ci wa City ƙwallo a Club World Cup a karawa da Al-Ain.

Jorrel Hato (Chelsea)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: Tsaron baya

Kasa: Netherlands

Jorrel Hato mai shekara 19, ya buga wasa sama da 120 a ƙungiyarsa, ya kuma buga wa Netherlands karawa shida.

Hato, ya fara buga wa Ajax tamaula yana da shekara 16 da yin kyaftin yana da shekara 17 - Shi ne matashin kyaftin mai shekara 17 a Ajax a wasan Turai.

Rawar da ya taka a bara ta sa an bayyana shi a matakin fitatcen matashi mai shekara 21 a gasar Eredivisie daga nan ya koma Chelsea a Agusta kan fam miliyan 37.

George Ilenikhena (Monaco)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: Mai cin ƙwallo

Kasa: Nigerian / Faransa

George Ilenikhena ya taka leda a Amiens mai buga gasar Faransa mai daraja ta biyu ya kuma taka rawar gani a Royal Antwerp a 2023/24, wadda ya taimaka da ta lashe Belgian Super Cup a 2023.

Bayan da ya ci ƙwallo 14 a wasa 49 a bara daga nan ya koma Monaco. Ya kuma ci Barcelona a Champions League a kaka biyu baya - a wasan da Antwerp ta ci 3-2 a Disambar 2023 mai shekara 17 da wanda Monaco ta ci 2-1 a Satumbar 2024.

Franco Mastantuono (Real Madrid)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 18

Gurbin da yake bugawa: Tsakiya

Kasa: Argentina

Ɗan wasan Real Madrid, Franco Mastantuono ana ganin ɗaya ne daga matashin da ake ganin zai haskaka a fannin taka leda a duniya.

Real Madrid ta sanar da sayen Mastantuono ranar 13 ga watan Yuni ranar da ya cika shekara 18 da haihuwa - ranar 14 ga watan Agusta ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida a ƙungiyar kan fam miliyan 39 daga River Plate.

Ya fara buga wa tawagar Argentina tamaula ta ƴan kasa da shekara 17 a watan Yuni, ya kuma yi wa Real Madrid dukkan wasan da ta fara a La Liga a 2025-26.

Senny Mayulu (Paris St-Germain)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 19

Gurbin da yake bugawa: tsakiya

Kasa: Faransa.

Senny Mayulu, mai shekara 19 ya lashe kofi biyu a babbar gasar tamaula ta Faransa, ya zura ƙwallo a raga a Club World Cup a Amurka.

Ya fara buga wa PSG tamaula a 2024 ya kuma wakilci tawagar Faransa ta matasa ƴan kasa da shekara 20.

Mai buga wasan tsakiya, yana canjin ɗan wasa ne a PSG, ya kuma nuna kansa, bayan cin Inter Milan ƙwallo na biyar a wasan da suka yi nasarar cin 5-0 suka lashe Champions League a watan Mayu.

Rio Ngumoha (Liverpool)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 17

Gurbin da yake bugawa: Gefe / Mai cin ƙwallaye

Kasa: Ingila

Rio Ngumoha ya fara daga makarantar koyon tamaula a Chelsea daga nan ya koma Liverpool a 2024, yana da shekara 16 ya fara buga wa ƙungiyar Anfield wasa a karawar da ta doke Accrington 4-0 a FA Cup a Janairun 2025.

Haka kuma Ngumoha ya ci Yokohama da Athletic Club a wasannin atisayen shiga kakar bana.

Haka kuma ya shiga kundin tarihin Liverpool a watan Agusta a matakin matashin da ya ci ƙwallo a Premier League - shi ne ya ci Newcastle ƙwallo na uku da Liverpool ta yi nasara 3-2 a St James Park, kwana huɗu tsakani kafin ya cika shekara 17 da haihuwa.

Ethan Nwaneri (Arsenal)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 18

Gurbin da yake bugawa: Mai kai hari daga tsakiya / Gefe

Kasa: Ingila

Bayan da ya fara wasa daga makarantar koyon tamaula ta Arsenal, Ethan Nwaneri yana da shekara 15 ya zama matashin da ya buga Premier League a tarihi a wasan da Arsenal ta kara da Brentford cikin Satumbar 2022.

An fara wasa 16 da shi a dukkan karawa a Arsenal a 2024/25 da yin canji sau 21 da cin ƙwallo tara har da biyun da ya ci a Champions League a kakar da ta wuce.

Ƙwazonsa ya kai aka zaɓe shi cikin ƴan takarar fitattun matasa a Premier League a kakar da ta wuce, yana cikin tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21 da suka lashe kofin nahiyar Turai.

Geovany Quenda (Sporting)

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Shekara: 18

Gurbin da yake bugawa: Gefe / tsare baya

Kasa: Portugal

Magoya bayan Chelsea za su samu damar kallon rawar da Geovany Quenda zai taka, wanda zai koma Stamford Bridge a karshen kakar bana kan fam miliyan 44.

Ya bayar da gudunmuwar da Sporting ta lashe lig da kofi a 2024/25, wanda cikin watan Maris aka sanar cewar zai koma Chelsea.

Quenda ya yi bajinta a gasar nahiyar Turai ta matasa ƴan kasa da shekara 21 da ci wa Portugal ƙwallo uku, shi ne fitatcen ɗan wasa a gasar.